SILAR GIDAN AIKI

1.2K 69 10
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad #Freshummieyxeey*

*PAGE 7⃣8⃣*

Mansur suna tafe suna hirar soyayyarsu gwanin sha'awa Har kofar gida yazo ya sauketa, Bude kofar tayi bayan sunyi sallama Zata fita kenan ya janyo mata gyale, tsayawa chak tayi, sannan ta waigo, Yace Love wallahi kamar karki tafi, Smiling tayi tace Dear saura kwana nawane? Murmushi yayi yace Kwana 6 Ko yana magana yana lashe baki yana kare Mata kallo daga sama har kasa hade da wani kashe mata ido, tuni ta gane inda ya dosa tace Love, Allah ya shiryaka, Murmushi yayi yace AI Indai akan sonkine I think I'm in the right way, tace uhmm tai tafiyarta gida

Jiyai kamar ya bita amma ba hali, seda ya bari ta shiga gidan da kusan 5 mins sannan ya tada motarshi yai gida

Koda yaje gida Daki ya shiga yai wanka yasa jallabiya na shan iska yai alwala yai sallah yai karatun qur'ani sannan yaita addu'a

Nazeefa kuwa tunda ta shiga Gida itama Room din iyayenta ta shiga ta samesu sunata kiran wayar yan uwa da abokan arziki Wanda aka Zauna tare, suna Sanar da su bikin Nazeefa satin nan mai zuwa.

Nazeefa Sannunku da gida tai musu sukace yauwa har kindawo? Tace eh, Sukace madallah

Dakinta ta shige itama tadan watsa ruwa tasa Riga bame nauyi ba, tahau gado tai kwanciyarta, Lalubo wayarta tayi cikin jaka taga, Tetxs kusan guda 10, fara karantawa tayi tai murmushi aranta tace M.T sarkin soyayya itama fara aikamai tayi, Shima yana gani yaji dadi sosai aranshi

Wunir ranar dai ba wani baccin kirki sukai ba dan sun kusan raba dare suna chats na soyayya

Washe Gari
    Misalin karfe 10:00 na safe baban Nazeefa yace ta kirawo kawarta shin suna gidane? Nan Take Nazeefa ta kira Amerah ta tambayeta tace yes suna gida, Nazeefa tace OK, Sanar da iyayanta tayi sannan suka Tafi gaba dayansu,

Gidansu da akasaima su Ameerah suka Fara zuwa, Nazeefa tace Masha Allah kai gidan ya yi ba laifi, 4 bedrooms ne se falo guda biyu ga kitchen da dakunan maza har biyu kowanne da bayinshi ga Dan madaidaicin tsakar gida harda shukan gwanda da gwaiba lol,
    Nazeefa tace Allah ya Kara daukaka baba Yace Ameen kema Allah yaiwa rayuwarki Albarka, rike hannunshi tayi tace Ameen baba na, Umma hafsatu ma tace Masha Allah

Fitowa sukai suka wuce gidansu Ameerah, Nazeefa ce ta Fara shiga ta sanar dasu da iyayanta suke, Allah yasa baban Ameeran nanan

fitowa yai, yai musu bismillah su shugo, Bayan sun shugu sun gaisa nan Baban Nazeefa ya sanar dashi abunda sukazo dashi

   Baban Ameerah yace banfahimce kaba gida nawaye? Wani gida kuma?

Baban Nazeefa yace Gida muka baku halak malak, Nan gidan gaba daya ya kaure da murna Dan dadi abunda basu taba tsammanniba, lalle mutanan nan sun cika yan halak,

Ameerah kuwa kasa magana tayi Dan dadi, kallon Nazeefa kawai takeyi, tabbas Wasu kawayen yan amanane wasu kam Kullun burinsu suganka cikin wahala, Rungumo Nazeefa tayi tana kuka tana mata godiya tace kidena wallahi, Mu godewa Allah ne kawai tace hakane

Baban Nazeefa yace to Alhamdulillah sai ku tashi gaba daya muje gidan ku gani sannan yaba mahaifin Ameerah takardun gida,

Dukansu suka tashi suka tafi, sukaga gidan Masha Allah, Wayyo Dadi, Yara se tsalle suke sundawo sabon gida, Ga bishiyan gwaiba da gwanda ga tiles se kyalle yake, Tsalle suke tayi suna yeeehhh muma muna zama yan gayu, Nazeefa na tsaye ta tino da rayuwarta nada irin wahalan da tasha Aranta tace nima hardani na zama yan gayu lol,

Maman Ameerah tai musu Godiya sosai, tace inshaa Allah yau sai kwanan sabon gida, Yara suka Kara tsalle,

***
    Mansur ne ya Kira Nazeefa akan cewar yauma yanason ganinta, tacemai please yayi hakuri, Ga abun dake faruwa Su Ameerah sun koma sabon gidansu so da ita ake komai bazasu sama daman haduwa ba, Yace please ya saukar da murya kamar me shirin yin kuka yace inane gidan nazo kinsan yau bazan Iya bacci inbangankiba? Tamai kwatance yace OK kinachan dai ko? Tace eh yace at anytime Zan Iya zuwa tace OK I love you yace, I love you too

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now