SILAR GIDAN AIKI

1.5K 83 1
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

*PAGE 3⃣8⃣*

Tun Asuba Nazeefa sanyi  ke kad'ata, Zak'olo hijab dinta tayi ta Kara rufe jikinta, idonta biyu aka kira sallar asubahi dan haka ta tashi ta dakko ruwan data siyo tai fitsari tai alwala tai sallah ta zauna tai azkar, da yake ta haddace su akanta, Ganin safiya tayine ga mutane sunfara zirga zirga a Ung ta tashi ta nannade kayanta ta zura a jakar ghana most go dinta, Ta ajiye chan karshen lungun dan bama wanda zaiyi tinanin akwai wani Abu

  Shiga cikin gari tai sosai, jitai garin na Mata dadi, Kallon al'adar garin take gwanin sha'awa Ba ruwan wani da wani, kowa abunda yasa gaba shi yakeyi, tana tsaye wasu Mata da miji sukazo wucewa ta gabanta sun burgeta sosai, kana ganinsu kasan suna tsananin son junansu, Dan hannunsu rik'e yake suna lafiya suna hira hade da murmushi a fuskarsu, A zuciyarta tace" inama nine! Inason inga Ana soyayya yana burgeni sosai, Nan take se taji tanajin haushin kanta, tace wama zai sota bare ta sama irin soyayyan nan, hawaye ne suka zobo mata Tace" Ya Allah ka kawomun dauk'I Haka taketa kallon masoyan nan har seda suka bace Mata!

     Gidan Sarki
   Hajiya ne zaune a fad'eden falonta, Kuyangi se tausa suke Mata, Hassan ne ya shugo ya gaisheta ta amsa, apple din dake kan plate ya dakko ya faraci, Saiga Hussani, Shima zama yayi kusa da Hassan, ya dakko Apple yanaci, Ganin yaranta biyu sun hadu ta Kora kuyangin nan tace subar wajen Sukace Angama Hajiya

   Hussaini ya kureta da ido yace" Mum our promise kin tuna? Hassan yace Our promise kuwa? Wani alkawarine wannan da bansaniba? Hussain ya dafa Bro dinshi yace"  Calm down sarkin jin kwakaf,

Hassan yace OK to Shikkenan, Kallon mahaifiyarsu yayi se a time din ya lura da yanayin mood dinta yace" Hajiya Lafiya kuwa KO bakijin dadine

   Kafin tai magana, Hussaini yace" ai maganar zamui yanzu kenan,

A tare suka hada baki sukace to Menene Hajiyarmu?

Kallonsu tayi cik'e da tsantsan Kauna zata Fara magana kenan Sega me martaba Sarki yazo, Cos tunda Hajiya ta tashi da safe bataje sasanshiba saboda duk safe se taje, So Yajita shuru sai yasa ya biyo baya

Ya naganku anan this early morning bakuje aiki bane? Inji me martaba

Hada baki sukai sukace today is Saturday

Ohh Namanta yace" wato shine akaimun wayau wani meeting akeyi anan da ba a gayyaceni ba?

Murmushi sukai basuce komai ba, Me martaba ya kalle matarsa yace me ya sameki KO bakijin dadine? Hussain yace Dad tambayar da muke Mata Kenan, Dukansu suka kureta da ido

"Hajiya Bilkisu ta soma magana kamar haka tace" hmm Da lafiyana ne da da sauki, Kawai Ina tinanin Halin da Yar'nan Nazeefa ne zata shiga, yanzu duniya ba gaskiya, tana magana muryanta na tawa!

Me Martaba dukda yafi Hajiya saukin Kai Tsaki yayi, yace Zancen banza da wofi, Ni kunsan ban daukar raini da Wawanci, Nan a ga yarinya tai sata dumu dumu shine har zaki Tara yaranki? Sui Mata mene? Nasan be wuce kice aje a nemota to banan gidan ba Ina fada miki, Sannan ya kalle yaranshi yace" Ku bace anan KO na bata muku rai, Amma kekam baki da hankali,  Mtswww yai ficewarsa, Wani Tinani Hajiya tayi tace" hakane fa banda hankali da ta tafi da gold din 3M inyi yaya, tsaki itama tayi taji ta tsana Nazeefan gaba daya

Bangaren Su Suhaila kuwa burinsu ya cika dama sun kudara sai sun sa Nazeefa tabar gidan kuma ta Bari, Sai chusa kansu suke wajensu Su Hassan amma Ikon Allah Su Hassan kamar sunsan Sune Silar barin Nazeefa gidan ko kulasu basayi,
 
    Hassan da Hussaini ne zaune suna discussing abunda akaima Nazeefa Sam be daceba, Hussani yace kabari, Nifa ban yarda dasu Suhailan nan ba, Hassan yace" tab gaibu kenan, Bakaga sai shige mana sukeyiba ko zamuce muna sonsu? Hussaini yace" kaga psychologist kaifa akwaika da karanta mutun, Hassan yace" tuni na ankare Su ai sai yasa bana musu Wasa, Hussain yace tab Allah to yasa Mu dace Hassan yace" Ameen

Nazeefa ne Ganin jikinta na Mata ciwo tace" Bari naje chemist Ko Zan sama magani, Wani Dan madaidaicin shagon saida magani ta gani ta Shiga, tace abani maganin ciwon jiki

Me zama a chemist dinne yace na nawa? Dago kan Da zatai suka hada ido dashi, kashe Mata ido yayi Dan nan take yaji yana kaunarta

Ce Mata yayi yan Mata amma ba anan garin kikeba ko Harara takai mai tace Bansaniba nidai kabani magani inzaka bani! Miko Mata yayi tace ga kudin yace yan Mata kodan kyanki kibar kudin, tsakk tayi tace wasu dai kamar bunsuraye suke wlhi

Tafiya takeyi samari sai nunata suke wai Kai yarinyar Chan ta hadu...

****
    Bangaren Mubeen kuwa Abubuwan da Haleema takeyi ya isheshi Dan ta kaishi bango, Dan haka samun mahaifiyarshi yayi yace" shi gaskiya Ya gaji da zama da ita bazai iyaba, ga kazanta gashi batamai abinci, seya tafi aiki ta taro kawayenta suzo kowa ya dafa abinda ranshi keso amma shi idan ya dawo sedai ya dafa da kanshi

MOM dinshi Tace" Alhamdulillah nima dama na gaji, aurenku getting to 4years kenan ace KO Bari bata taba ba, to gaskiya ba nan gidan ba, yanda kuke KO ukun nan munaso ku Tara mana jikoki ta KO Ina,

Kabari mugani dole nema ka saketa Dan bazamu iya zama da juya ba

Hankalin mubeen ya kwanta cos mamanshi ta goyon mai baya yace to shikkenan Mum

Part dinsu ya wuce me murna yakeyi

Yana fita Mum dinshi tace" Aiko Zaman gidanki ya kusan karewa a nan gidan, ba ansama abunda akesoba, Ji yanda Mubeen ya koma abun tausayi hmmmm

Tana ganinshi taga face dinshi dauke da fara'a, Ita kwararriyar Yar Yaudara, kusa dashi taje ta makale a jikinshi wai sanyi takeji, wani daka Mata tsawa yayi yace" wuce ki bani waje

Yau aka Fara sanyi?

Ko jiya ba'ai sanyi bane, ni ki matsamun with this your dirty mouth kazama kawai, Kalleki ko zani biki Iya daurawaba

Gabantane yai mugun fadi ta shige daki, tace kodai Mubeen Aljanu yake dashi? 2days dinnan tsorata take da al'amuranshi


Muje Zuwa

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now