SILAR GIDAN AIKI

1.5K 98 6
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

      _Ina ganin one love💕💕 love you All💜_

*PAGE 3⃣1⃣*

Bayan Kwana Uku
   Rana bata karya sedai uwar diya taji kunya, yau Saturday, za'a daura auren Mubeen da Haleema,

Bangaren Nazeefa kuwa tun garin Allah ya waye hankalinta yai mugun tashin Dan tasan yau ba makawa za'a daura auren Mubeen, zazzabine ya rufeta sosai har dinshi dinshi take gani, tai kokarin ta boye abun dake ranta amma Ina seda aka gane! Dan jikinta yai zafi sosai, Asibiti aka kaita aka kwantar da ita akace Tana bugatan hutu sosai Dan jininta yayi kasa, anan ta sama daman Kuka yanda takeso koda an tambayeta se tace ita jikintane ya matsa Mata basusan Kukan rashin Mubeen bane.....

Haleema burinta ya cika, Mubeen kuwa KO a jikinshi inkun ganshi bazamu kuce ango bane, Dr Bashir ne da abokanshi suka matsamai ya shiga wanka Dan sunsan ana jiransu dan karfe 12:40 kuma 1:00pm ne daurin auren Mubeen ya Kalle Bashir yace" bazanjeba kuje kuce banda lafiya

Dr bashir ne yai kasa kasa da murya yace" nasan ba sonta kkeyiba Nazeefa kakeso but please ka daure ka shiga wankar Dan Kar a gane akwai wani abun please koma menene we talk later, Binshi da ido kawai yayi sannan ya shiga toilet, ya shiga ya kasayin Komai Dan ko kaya be cireba, kallon kanshi yayi a jikin mirror din dake bayin kawai ya fashe da kuka, Dan Zuciyarshi gaba daya ta kwadaito da son Nazeefa, A ranshi yace" Inama da Nazeefa za'a  dauramun aure ai da tuni nayi wankana ya sake fashewa da kuka ya kusan 15mins a bayi yana tsaye yana kuka

Buga kofar toilet din yaji anayi yaji muryan Bashir yace" We're waiting for you gentleman

Tsaki yayi yai sauri ya watsa ruwa ya dauro alwala ya fito fuskar nan a murtuke ba annuri, Abokanshi kuwa se ango Ango suke cewa

Shiryawa yayi cikin shadd gezna blue yasha ado sannan suka fito kayansu iri daya da Bashir direct motocin Eu suka shiga basu bata lokaci ba se wajen daurin auren

A daura auren Mubeen da Haleema, Mubeen na cikin mutane Haleema ta kirashi tace" angona na kaina, haushi ya isheshi yace plz Ina Cikin mutanene zamui magana later

nan take fuskarta ya sauya wai me yasa Mubeen yake Mata hakane, Wata zuciya kuma tace aikin banza an daura dai

Bayan daurin auren ne aka tafi dinner, shima nan seda abokanshi sukaiwa Mubeen fada sosai akan ya daure yaje, yace shi ba inda zaije, ansha gwagwar maya da shi sannan ya Kara kintsawa suka tafi amman fuskar nan ba annuri Sam, Dan shi gaba daya hankalin shi na wajen Nazeefa

Tun a wajen bikin yaga kalar kawayenta jikinshi yadanyi sanyi but bece Komai ba a cewarshi saboda bikin ne yan Mata sukai dressing haka

Nan MC ya umurce amarya da ango su fito sui rawa, Haleema ba jan aji, kan nan na rawa ta fito tsakiyar hall, kayan jikinta ya matseta, Mubeen shuru shuru be fitoba, MC yace ango ka fito Kar Kai mana fuck up ga amaryanka a tsakiyar hall, tsaki yayi, Haleema Kuwa dataga yana shirin bata kunya gaban kawayenta gogaggu, zuwa wajen inda yake tayi ta kamo hannunshi gaba daya hall din Yadau tafi raff raff raff duk rashin kunyarshi ranar seda yaji kunya

He has no option hakanan ya biyowata aka samu musu kida Haleema rawa tayi son ranta tamkar ba kowa a hall din, Mubeen kuwa se basarwa yakeyi yana mamakin rashin kamun kanta, Sundau kusan 15mins a haka masu musu vedio Masu hoto nayi, Sannan MC yace duk su matsa a bar amarya da ango a wajen, kowa komawa wajenshi yayi ya zauna

MC ne ya mik'a wa Haleema Speaker yace ta fadawa al'umman nan irin farin cikin da taji na yau ranar auranta...ta amsa tana murmushi tace" _I can't express how happy I am, domin wani dadi nakeji na musamman, Sannan ta kalla Mubeen tace I love you my darling sannan inama kowa addu'an Allah yakaiku gida lafya mungode da soyayya_ Hall din yadau ihu sosai

MC yace" mungode Amarya, sannan ya mik'a wa Mubeen yace" Wani irin farin ciki kaji ayau?

Mubeen ya amsa yace" ina godewa Allah daya kawomu wannan rana me albarka, Allah ya kara cika mana burinmu na alheri!

Dr bashir yana jin maganar Mubeen ya gane inda ya dosa girgiza Kai yayi yace" Allah ya baka Nazeefa abokina

Anyi dinner Iya dinner Masha ALLAH, abun se Wanda yagani

Ankai amarya dakinta, komai Masha Allah, kawaye kuwa kowa se tsegumi akeyi dan part din da aka kaita yai bala'in haduwa

Haleema hankalinta kwance Dan burinta ya cika

Kawayen amarya ankwana an hantse, dare nayi abokan ango suka kawo angon dakinshi, nan dai suketa musu fada akan zauna lafiya

Da zasu tafine Mubeen ya rakosu, suka Dan kebe da Dr Bashir yai Mai fada sosai akan ya daure duk da ba choice dinshi ya aura ba yayi hakuri, Kar ya dinga nuna Mata kiyayya komai zaizo ya wuce da yardan Allah, Mubeen yace yaji ya gode sukai tafiyansu ango ya shiga dakin amaryanshi

Tunda Mubeen ya shiga dakin amaryarsa Ko kallon inda take beyiba hasalima Wayarshi ya dakko ya na Dan danne danne a wayarshi, mutumiyarku kuma Se iyaye takeyi ita adon dole amarya..haha

Yana zaune Yaga tinanin zemai yawa ya kalleta yace tashi muje muyi alwala mui sallah Mu godewa Allah, da sauri ta mik'e ta nufa toilet, shima toilet din dakinshi ya shige yai alwala sannan yazo dakint sukai sallah daganan be Kara ce mata komai ba ya koma gefen gado yai kwanciyarshi, da tinanin Nazeefa yai bacci

Haleema kuwa yau taga ikon.Allah, a ranta tace ji mutum kamar dutse AI KO hannunta ya taba a matsayin matarshi, Tsaki tayi itama ta kwanta tace munanan dakai Mubeen




Thanks for your time


*Wattpad #Freshummieyxeey*

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now