SILAR GIDAN AIKI

1.4K 82 7
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

*PAGE 5⃣3⃣*

Motocin yan sanda aka kawo akace Su baban mubeen Su shiga, Jikinsu KO Ina na rawa Daka gansu kasan basu da gaskiya bare mubeen da kamar kucemai arr ya ruga

   Mansur ne yace No bari ya saman musu napep ko, ai zaifi Tunda angama maganar

Fita yayi ya sama napep guda biyu yace Su jirashi, court din ya shiga yace Su fito sannan yai ma lauyan godiya sosai yace idan akwai wani abun ya nemeshi yace to angama

   Nan ya umurce masu Napep din duk inda ya shiga Su dinga binshi zai basu kudi masu tsoka sukace angama ranka shi Dade

Saboda sunsan Mansur sosai Dan commissioner ne amma ba ruwanshi ko ina sa kafa yakeyi kamar ba Dan babban gida ba sedai kalar fatarshi kawai zaka gani kasan he is from rich family

Sunyi tafiya kadan suka shugo layin

tun akan layin yan unguwa kamar an Kai musu rahoto suketa leke leke

Daidai gidan motar Su Mansur tai parking da napep din, Suka fito suka shiga gidan dukansu!

    Kowa jikinshi a sanyaye Dan alkalaminsu ya bushe, Dan sun zama abun tausayi, Hajiya Hadiza suna shiga takai gwiwoyinta kasa tana rokan Nazeefa akan ta yafe musu ita tayi nadama Wallahi bazata karaba,

Nazeefa ko kallonta batai ba, Sannan ta juya wajen Mansur shima tamai godiya yace bakomai

  Da kafarta ta karaso wajen mahaifan Nazeefa tana musu magiya akan duk abunda sukai musu suyi hakuri dasa hannunta, Sukace Su sun yafe cos da basu yafeba bazasu taba bari Su dawo gidan ba, Tace nagode, Duk inda taje Haleema yarta na biye da ita

Ta kalle Mansur Tace" akwai wani abune kuma? Yace I think tunda sun yafe bakomai Ko Umma tace hakane  bakomai, komai ya wuce

Ai tanajin haka riko hannun yarta tayi suka fice da gudu Dan taga tashin hankali, Mansur kamar zai kyalkyale da dariya ya fuske dai, Nazeefa kuma kasa rik'e dariyarta tayi ita KO tai dariya sosai

Tace Allah ya kyauta

     Suna fita napep suka samo Tace yakaita tashar da za ashiga mota aje abuja yace angama

   Duk a tsorace suke sosai Tace" Haleema muna komawa da kwana biyu Zan saida gidan mu koma wani wajen kar azo a Kara nemanmu,

Haleema Tace gaskiyane Mum Huh gaba daya jikina ba inda baya rawa mama

***
    Su Mansur kuwa ganin kar Su shiga hakkinsu da yawa shi da Abdallah sukace zasu wuce cos yanzu baban Nazeefa da baban mubeen da iyalanshi Kawai suka rage

Yasan they need privacy bakomai ne za ai a gabansuba Dan haka sukace zasu wuce gida

Su umma sukai Mai godiya sosai,

Bangaren Su mahaifan Mubeen kuwa ba Wanda ya Iya cewa komai Dan a kunya ce suke sunyi budulci

    Nazeefa ce ta rakosu har wajen tai musu Godiya sosai yace bakomai kinfi haka a wajena

Wani murmushi ta sakar mai ya dag'a mata gira yace I'll miss you my lady tace me too har zasu tafi ya juyu yace please dear SABR (be patient) please

Hummm kawai tace,

Mansur kallonta yayi ya girgiza kai, sukai shigewarsu mota

Tana tsaye suka shigar motor sukai wucewarsu ita kuma ta shugo gida

Tana shugowa gida fuskarta da walwala Dan ita tamanta ma halin da ake ciki

  Tozali tai da Su mubeen tuni chanza fuska ta hade rai..aranta Tace Mugu, Nifa saina rama abun dakai mun

    Binsu da kallo daya bayan daya tayi taji wani bakin ciki ya mamaye zuciyarta inama anmusu hukunci me tsauri

   Maganar mahaifinta taji  yace Ku mushiga daga ciki mana

   Sukace To

Me gadi kuma se leke yakeyi Dan yasan akwai drama yau

    Su Nazeefa ne a gaba Su kuma suna bin bayansu har suka Isa falon

   Kowa samun waje yai ya zauna kowa yai shuruu da abun da yake sakawa a zuciyarshi


Muje Zuwa



FOLLOW
VOTE
COMMENT


#Freshummmieyxeey

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now