SILAR GIDAN AIKI

1.5K 95 11
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

   *Ina ganin ruwan comment Ina godiya sosai*❣👌🏼

*PAGE 4⃣1⃣*

Dube dube yakeyi sosai yaga dai ba alamun kudi a wajen, Zare ido mubeen yayi yace kodai ba anan na ajiye ba? Kara birkita kayanshi yayi yaga beganshi ba, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun yace" dafa kanshi yayi yace tabbas ba kowa zai dauka kudin nan ba Haleema ce!
   Shiga dakinta yayi yace" bani kudin da kika dauka, Zare ido tayi hade da dafa karji tace" bangane inbaka kudinkaba dama ka aramun ne? Amsar data bashi yasa ranshi ya kara baci sosai, Ya sharara Mata mari sau biyu dama yanada cikinta

Kuka ta Fara, yace KO kukan jini zakiyi kiyi sekin fitomun da kudina

   Suna cikin hakane sega Dr bashir yana knocking kofar, Kara bigeta yayi sannan ya rufo dakin yasa key yazo ya bude ma Dr Bashir

    Zama a falo yayi, mubeen ya tashi ya dakko Mai ruwa da abunsha ya kawomai, yasha, Yace plz kabani sauri nakeyi, Ciro waya Mubeen yayi yace bani account number din nan take yamai transfer, Yacemai Nagode sosai, har waje ya rakoshi

    Seda yaga yabar gidan sannan ya dawo, ya bude Haleema yai Mata kacha kacha kuwa yace bazai Iya zama da barauniya ba, shi ya gaji gaskiya, Nan Take ya saketa Saki Uku batare da yayi shawara da kowa ba, Kurma ihu tayi da seda sasan mahaifiyar mubeen sukaji suka fito

Nan suke tambayar Meya faru Mubeen ya sanar dasu Abundatai Mai shine ya sake ta, Alhamdulillah mahaifiyasu tace" Shine daidai sai Ki Kira uwarki ki sanar da ita

Kuka Haleema takeyi sosai tazo gaban Mum tana cewa plz taba Mubeen hakuri,

Maman Mubeen ta kalleta tace se yau kikasan dani? Shekaranki uku anan gidan befi sau biyu sukazo Kika gaisheniba, Kara kuka takeyi sosai, Mubeen kuwa tasowa yayi yace ta Kama gabanta ko yai Mata duka tunda batada mutunci

    Hakanan ta tattara kayanta aranar ta koma gidan uwarta, koda ta koma bata tatar da mahaifiyarta ba ta sama waje tai tagumi ta Zauna.....wannan kenan

*****
    Mansur ne ya kira Abdallah yace" mai ya shirya gashinan zuwa ya daukeshi, yace alright bakomai sai kazo
  Part din mahaifiyarshi yaje ya gaisheta yace Mum nagama shiri yanzu zamu tafi akwai abunda nakeson yine kamar yanda na fada miki, Idan munada lokaci sosai zanje Chan gida na gaishesu
   Mum dinshine ta kura Mai ido tace" OK Beloved son amma da kabari driver ya kaiku saboda nisan hanya fa

Mansur yace Mum karki damu ba yau zamu wuce direct ba inajin zamu sauka a wani garin Mu kwana gobe Mu dauke hanya tace OK hakan yayi sosai, Allah ya tsare yace Ameen
    Fitowa yayi ya shiga mota be tsaya ko inaba se gidan Abdallah

Koda ya shiga yace Amarya ba zama zamui ba nazo Zan tafi da angonki an bani dama? Dariya tayi tace wane ni sai kundawo Allah ya tsare a kula da hanya, sannan Ta kawomusu abinci tace gashinan idan kunji yunwa Ku tsaya kuci

  Mansur yace woo kinason mijin nan naki, Abdallah kallon matarshi yayi yai mata kiss a daidai lokacin Mansur yakai idonshi, saurin kauda Kai yayi yace" uhm Nima na gaji zanyi auren nan na huta

***
Da daddarena Mum din Mansur turaki and his beloved dad suke hira, Mum tagumi tayi tace" kaga yakamata Mu matsawa Mansur fa ya fito da matar aure shekaru na tafiya, Dad dinshi yace nima abun na raina Bari yadawo Tace Ok....

    Kwanan Su Mansur 3 a garin, Kullun Matar Abdallah cikin waya da text suke ciki, Mansur yaga kamar ya toyemai hakki, So basukai ga zuwan garin Yan uwan mamanshiba sukace gobe zasu dawo cos yaga Abdallah a takure yake, Abdallah kuma yayi yayi dashi akan suje yace aa se Wani time

Tunda zasu dawo gaban Mansur se fadi yakeyi, Addu'a yakeyi amma gabanshi se Kara tsananta fa bugawa yakeyi, Kawai yace khairan inshaa Allah,

Abdallah yace meye yace bakomai, Nan suka dauka hanya suna tafiya suna hira, Abdallah ya Fara gyangyadi,

Mansur ganin Abdallah ya fara bacci se ya Kara gudun motor, Chan ya hango Kamar wata mata a tsaye a titi, Addu'a yake tayi dai Dan gabanshi Kara bugu da sauri yakeyi, Karasowa yayi ahankali lokacin Still Abdallah na bacci, Kurma Ihu Mansur yayi Allah yasa be sake sitiyarin motar ba da sai sunyi accident, Mansur  Cikin Ihu yace Aljanah, Aljanah a kunnan Abdallah, A firgice ya tashi yace tana Ina? Ganin Mansur ya tsayar da motor yasa Abdallah ya fito ya turashi dayan site din, Shi kuma Abdallah ya zauna a mazaunin Driver!

Karema Macen da Akace Aljanace Abdallah yayi saiyaga Tabbas Aljanar Mansur ce! Faduwa tayi a wajen tace ku temakeni wallahi ni mutun ce ba Aljanah ba

Abdallah ne da karfin hali ya fito amma bakinshi addu'a yakeyi, Tsugunnawa A gabanta yayi taga tabbas itace! Allah Mai iko yace

    Mansur kuwa Tsorone ya kamashi ganin Abdallah ya fita shima yai kokari ya fito, Karema fuskarta kallo yayi sosai yace" Abdallah she's d one, Aljanace meyasa ta biyomu nan? Yana magana tsabar tsoro seda yai in'ina Dan maganar bata fito da kyau ba

Kubani kuwa tace" Zan mutu, Mansur besan sanda ya tashi ya bude mota ya dakko ruwan faro ba, Idonshi cike da hawaye!

Abdallah kuwa in banda ikon Allah ba abunda yake cewa!!



Muje zuwa
Follow
Vote me on Wattpad *#Freshummieyxeey*

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now