SILAR GIDAN AIKI

2.5K 155 4
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

'''Life is too short to stress yourself with people who don’t even deserve to be an issue in your life.'''

_The whole page is dedicated for youuu *Naxeefy❤* kayi yanda kakeso my dear...I love you to the Moon back 100 times..though nasan you don't like reading Long writing but Dolene ka karanta rubutu nah😘❤ I LOVE YOUUUU_

*PAGE 0⃣9⃣*

Ya tsaya chak kenan ita kuma Nazeefa tana kokarin bude motar, hannunshi yasa akan hannunta Yaji wani shocking tini ya cire,

Juyawa tayi ta balla Mai harara tace" Ohh kaima Dan iskan ne ashe, inba iskanciba wani irin abune wannan, Ko ka taba ganin a musulunci inda akace Namiji ya taba hannun mace? Bakada hankaline ko meye? Sai kuma tai tsaki

Mubin kam Dan takaici kasa magana ma yayi, me yasa zai Bari wannan Yar yarinyar tana fadamai magana som ranta, yana cikin tinani ta katsemai

Kara bude bakinta tayi tace" malan Nace ka budemun kofa na fita ko

Ko sauraranta beyiba ya tada motarshi, Yaci gaba da tafiya Wani babban pharmacy suka tsaya, Kallonta yayi yace meke damunki? Batace komai ba tamai dai nuni da cikinta da kanta, Fita yayi ta bishi da kallo tai ja yar karamar tsaki

   Shagon ya Shiga yai musu bayanin duk abunda da yake damunta, maganguna masu kyau da tsada yasiyo Mata sannan yadawo cikin motor ya mika Mata yace" ungo, Fuskarta na kallon waje itako ta amsa ta jefar dashi bayan sit

Kallon mamaki yake Mata aranshi yace duk Son da nake miki I'll deal with you banzan yarinyar sai wulakacin tsiya, Dariyar mugunta yayi ya tada motor yafara tafiya ahankali

   Ahankali suke tafiya yasa sauti yana tashi kadan kadan, Nan jikinta ya rikice ta rik'e ciki sai kuka takeyi, tausayi ta bashi sosai, gashi yasan bataci abinciba, parking din motar yayi ya shiga wani Shago yasamo Mata kayan drinks da ciye ciye na kwalama, sannan ya samo ma Su Haleema Dan yasan sesun Mai mita inhar be siyoba

  Exotic ya bata tadan sha kadan sannan ya dakko magungunan daga back sit ya mik'a Mata tasha ba'ai 10mins ba ta Fara zufa alamun Magungunan sun Mata aiki

D'ago kanta tayi ta kalleshi tace thank you ya mubin, shima yai banza da ita kamar bejiba, Nazeefa taji yayi shuru tace" nagode Still yai banza da ita

Nazeefa tsaki tayi tace wai mutun kamar kurma Ana magana yana banza da mutane

Dariyar mugunta yayi da shi kadai yasan me yake nufi

Ahaka suka Isa gida Both of them Zuciyarsu ba dadi Dan haushin juna sukeji

***********
    Bangaren faeez kuwa tunda ya fita gida shima bawon Allah chemist ya nufa da yake yanada yan kudi ya siyowa Nazeefa magani, yadawo gida akace basanan Zuciyarshi sai zayyanomai abubuwa yakeyi, tsoronshi kar mubin ya wulakanta Nazeefa...
                   *****
   Mubin ne ya Shugo gidan yasama parking space yayi, Nazeefa zata fita kenan Ya kirata cikin wani Yanayi da ita kanta seda ta tsorata, kallon juna sosai sukai, Mubin yaji wani Abu na yawo a kirjinshi, kallon labbanshi tayi taga kamar yana shirin magana, Tuni ta tina matsayinta a gidan, Tai sauri ta Sauka ta nufa fallo, Mubin kuwa Binta da ido yayi a ranshi yana Allah ya mallakamai Wannan yarinyar,

Tana sauka direct Dakin Hajiya ta nufa taje tai Mata godiya, Hajiya tace to bakomai yau ki huta abunki tunda gobe ba makaranta tace nagode

*******
    Haleema daga jin mubin ya dawo tai maza taje tai wanka tai kwalliya, tazo tasameshi a falo zama kusa tai sosai tashi, adaidai lokacin ita kuma Nazeefa zata shiga kitchen ta kallesu, tsaki tayi tace wai mutane kamar yan iska Ashe sunji

Haleema ne ta tareta tace da uban wa kike? Tace da Wanda ya tsargu

Mubin ne ya taso yace"Haleema Dan soyayyar da kikemun ki saketa, wani ajiyar zuciya tayi tace dan dai kasa bakine dana balla yarinyar nan, sannan ta kalle Nazeefa tace mata village and dirty girl kawai

  Nazeefa kuwa murmushi tai Mata ta shigewarta kitchen ta dauka cup ta koma dakinta

Haleema kuwa kallon mubin tayi tace kasan Dan Kai nazo KO? Yaushe zamui hirane wai

Yace Mu fita compound din gidan KO sweetheart OK tace ya mik'e ita kuma tana biye dashi

Sun fita sun kusan one hour a waje suna hiran masoya, balle yanda Haleema ta kurama mubin ido sonshi Kara shigarta takeyi,

bangaren feeez kuwa sai suntiri yake a falo, Ko zaiga ba kowa, cikin ikon Allah yana fitowa yaga ba kowa dan haka Faeez da sauri ya fada dakin Nazeefa da ma yana dan shugowa sudanyi hira idan ba kowa, Magani ya dakko mata yace" gashi nasan yan gidan nan is hardly Su siyo miki

Murmushi tayi tace" Allah sarki nagode faeez, Kagama dazu muka je da ya mubin ya siyomun

Faeez yace" Badai yai miki komai bako? Tace ah a bakomai yace" to Alhamdulillah

Nan sukaci hira sosai  dashi ta farfada mai matsalarta sai bata hakuri yakeyi, sunsha hira kusan 30mins yace Bari dai na tafi Kinsan munada sa'idawa, dariya sosai tayi Dan tasan da Wanda yakeyi tace" mubin ya jika ba ruwana atoh

Shima dariya yayi yace ai gaskiyane, nidai na wuce Allah Kara sauk'i

Ya fito kenan Saiga Mubin sun Shugo da Haleema

Zare ido mubin yayi what??? Me wannan yaron yajeyi a dakin nan this is d 2nd time da naganshi

Gabanshine ke bugawa yace" Tabdijam.........


Muje zuwa
       
Please FOLLOW & VOTE ME ON WATTPAD #Freshummieyxeey

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now