SILAR GIDAN AIKI

1.2K 80 5
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

_*Where are you my Original Daughter* here is ur page kiyi yanda kikeso baby, Inayinki en matah #Hannah Aliyou❣_

*PAGE 6⃣1⃣*

Falon suka wuce, Iyayanshi zaune suke kan kujera shi kuma yana kasa yana wasa da yatsunshi, gabanshi se dukan uku uku yakeyi

   Dad dinshine ya kalleshi yace" Mansur meke tafe dakai? Fadamun da sauri dan Zan fitane

M.T ne ya gyara zama yace dad Dan Allah neman alfarma nakeyi a wajenku, Ku amince na aura Nazeefa inasonta! Dad dinshi Ya cire Glass din dake fuskarshi ya karemai kallo, tuni murmushin dake fuskarshi ya gushe, yace Ashe bakada hankali? What are you saying? Yarinyar data gama bin gidajen mutane zaka cemun ita zaka aura? Sam bazaiyuwaba! Karma in Kara jin wannan maganar a bakinka, Mansur ka sake tinani! amma banace akwai yarinyar da Zan hadaka da itaba? Kenan Allah kadai yasan abun da kuka aikata lokacin da ka kawota gidan nan! Zaka zo ka dameni kace wani zaka aureta ka shiga taitayinka

Mansur turaki tsabagen rikicewa kasa motsi yayi, Dan kallon abun yake kamar a film? Mum dinshi kuma na zaune tana ba Alhaji hakuri

Alhaji yace Sam bazaiyuba ya tashi ya shiga room dinshi, Wani Kwalla ihu Mansur yayi yabi mafaifinshi har daki ya na kuka, Rike rigan babanshi yayi kamar karamin yaro yana bashi hakuri akan ya amince

Dad dinshi a fusace yace" get out of my room daga temako zakace wani zaka aureta hmm

Mansur kasa tafiya yayi Dan ji yai kafarshi sunmai nauyi, Jiri kawai yake gani dakyar ya samu yakai kanshi daki Dan wani matsanancin ciwon Kai da yakeji

Yana zuwa dakinshi gado ya fada

Wani zazzabi yaji yana shirin kamashi, Dan beyi expecting wannan reply dinba daga mahaifinshi, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun yace" Tashi yayi ya rufe ko ina na dakinshi yadan samu yasha panadol extra Dan wani kanshi yaji yana Saramai

Dakyar ya lalubo waya, Kallon screen din wayar yayi yaga hoton Nazeefa, Hankalinshine ya Kara tashi Dan ganin yake tabbas daya rasa nazeefa gwanda ya mutu, Yarinyar da yakeso ta zama uwar y'ayanshi gashi dad dinshi naso yai Mai fuck up! chusa hannunshi yayi akanshi yana shafa gashin kanshi Dan wani irin yanayi yakeji, inama ace mafarki yakeyi dayaji dadi

Yana cikin tinanine Call din Nazeefa ya shugo! Kallon wayar yayi ya kasa picking Dan Gabanshi fadi yakeyi sosai!

    Haka wayar ta gama ringing be daukaba, Bin wayar yai da kallo kamar wani tababbe

Natsuwa yayi kome yake tinawa ohoo

  Call ne ya shugo wayarshi yana dubawa yaga Abdallah da sauri yai picking ya fara magana hello Abdallah kana inane?
Abdallah yace" Ina gida mana bazaka zo bane?

Mansur cikin wani irin murya yace I can't come Dan Allah kazo akwai Dan matsala ne, Abdallah koda yaji Voice din M.T yasan akwai matsala kam Dan haka yace Mai I'm on my way right now, Mansur yace OK sai kazo, yana gamawa ko sallama basui ba ya cilla wayar Chan gefe

*****
   Bangaren nazeefa kuwa tun safiyar yau data tashi, jitai itama gabanta na mugun fadi, gashi tun jiya basu sake waya ba dan haka tadan damu kadan dukda tasan he's doing fine inshaa Allah

Bangaren Mubeen kuwa! Bayan tafiyar Su Nazeefa ji yai kamar an kara dasa Mai son Nazeefa, Dan he's praying Allah yasa ta zama matarshi

Toofaaa.....muje zuwa ankusan kawo final.. lol

Kiran Faeez yayi daya aramai phone dinshi wayarshi ba data zaiyi browsing yaga ko yau akwai kwallo, Dan haka faeez ba tare da wani tinaniba ya dauka ya bashi

Yana bashi room dinshi ya shige ya Fara duba dial call!

Yaci karo da 6ter *Naazee* smiling yayi ya kwashe number sannan yai saving a wayarshi da *ITA CE* sannan yamai damai da wayan

*****
Mansur ne kwance a daki  yana Tinanin How his life is going to be without Nazeefa, knocking din kofar yaji anayi, Yace waye

  Abdallah ne yace nine, OK yace, dakyar ya tashi yaje ya budemai, Suna hada ido, M.T ya marairaice kamar Wanda ya dade yana jinya

Abdallah ya kalleshi yce" lafiya kuwa? Binshi da ido yayi har suka isa room din Mansur, Zam sukai Abdallah yace wai meke faruwane?

Mansur yai kasa kasa da murya yace BOSS ne wai be yarda na aura Nazeefa ba

Abdallah shuru yayi Dan maganar ta shige shi sosai, Sannan daga bisani yace amma meyasa? M.T yace kawai wai Dan na kawota gidan nan!

Abdallah yace huh! Me mum tace? Mansur yace batace komai ba

Wani iri yai da ido da seda Abdallah ya Dan tsorata🤣 Yace me mum tace,

Shuru yai mai kamar besan abunda yake cewa ba........






Muje zuwa

_Please my fans...Ina Mai baku hakurin daga gobe zuwa Friday zanyi busy sosai, so Bear with me, Ina zama less busy Zan maku typing.......thanks for your time sweeties inayinku💞_



Don't Forget to

Follow
Vote
Comment

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now