SILAR GIDAN AIKI

1K 72 5
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

*PAGE 7️⃣1️⃣*

     Sun Dade a hospital din sosai se hiransu sukeyi, kwasam Sega Hajiya Bilkisu da Sarki se su Hassan da Hussaini dasu Jameela

Mum Mansur ne tace Masha Allah dama yanzu muke hiranku sai gashi kunzo

  Hajiya Bilkisu tace Ayya, Nan ta gabatar musu da mahaifan Nazeefa, Kara gaisawa sukai sosai, Sarki yace Masha Allah ba shakka tabbas kuwa wannan ne Malan Nalado me flour, ya kake ya bayan saduwa, yace Alhamdulillah, hira suka shiga Sosai kamar dama sunsan juna
***
    Bangaren Mubeen kuwa tun dawowarshi gida kasa sukuni yayi, Ranshi sai rayamai yake kodai ya nema Ameerah ce cos Nazeefa yasan confirm tamai Nisa wata zuciya kuma tace keep on trying ai ba aure tayi ba, Da tinanin nan ya wuni,

   Bangaren Mansur kuwa  Cikin ikon Allah Jikinshi yayi Sauqi kamar ba shi ba

Magana yakeyi sosai, Dan sunsha hira dasu Hassan  sosai kowa hankalinshi ya kwanta

Cin abinci sosai yakeyi koda aka sake dubashi ba BP. heart din ma ta koma normal shape dinta, Dan haka Doctors din suka kira iyayanshi akan su daure su cikamai burinshi, so that ya samu yai rayuwa mekyau sukace in shaa Allah
   Washe Gari nayi suka sallameshi ya dawo gida

Mansur yaji dadi Sosai, Ana Sallamarsu ya Kira Nazeefa ya sanar da ita, Alhamdulillah tace"

Yace please zakizone? Uhmm uhmm tace tana magana tana shagwaba tace kasan bazan iya zuwa ba, Gidan fa cike yake da mutane, yace ina ruwanki dasu Dan kawai ta kwantar mai da hankali tace Alright Chan yamma zanzo

Wani murmushi yayi sannan yace  I love you Please be online muyi chat cos I surely miss you,

Smile tayi tace OK  love you too

****
Bangaren Mubeen Kuwa  dama Already da yan kudadenshi, Wani hikima tazomai na why not filin da yake dashi ya gini babban Makarantar islamiya da boko wanda za'a amfana ko bayan ranshi, cos yanzu yayi nadama sosai Abunda da zai amfane rayuwarshi kawai zaiyi

Wani Me gini ya Kira yake tambayarshi in zanyi gida kaza kana tinanin nawa Zan kashe? Me ginin yace Yallabai Ina zuwa na duba

Nan take yai calculating, ya kirashi ya sanar dashi, Dr Mub33n yace Alright gobe by 9:AM kazo hospital din da nake aiki ka sameni yace inshaa Allah

***
    Mansur da Nazeefa Chat sosai sukai irin na masoya

   Bangaren iyayan Mansur kuwa tunda ga hajiya bilkisu da Sarki, Dad mansur ne yace Alhamdulillah tunda kunanan.

Gobe in Allah ya yarda Zamuje Mu nema aurar Nazeefa cos naga sunason junansu,

Mansur na Chan ma besan abun da akeyiba cos yana daki suna tinanin bacci yakeyi Ashe yanata buga chats dinshi da muradin zuciyarshi

Hajiya Bilkisune ta dan hada rai tace Nazeefa kuma bayan munyi alkawarin Zaku auramai Suhailat,

Sarkine Mijin Hajiya Bilkisu yace ban yarda da hakan ba, me yasa kin fiye son kankine

Shuru tai kamar Mai nazarin wani Abu, Suhailat tanaji ance baza a aura Mata mansur ba ta shige toilet kuka tayi sosai kamar ranta zai fita, Ya zatai da son Mansur, Wanda ta dade tana ajiyarshi, lalle kam ramin mugunta idan zaka ginashi kayi dai dai Kai

Su kuma Hassan da Hussaini room din Mansur suka shiga suka sameshi yana Waya

Hussaini ya fizge wayar yace To romeo hassan yace ko kuma Ango ba! Nan suka Fara Mai tsiya sukace Angon Nazeefa yanzu Su hajiya suke maganar gobe za aje maganar Nazeefa

Mikewa yai zumbur yace are you serious? Sukace da gaske Wallahi

Rungume pillow yayi yana dariya yace I'll soon be ANGO, ANGON ma na Nazeefa Wow

    Hussain yace gaskiya kam I'm happy for you ko ni da banda Wanda Zan aura da ita Zan aura

   Hassan ma yace KO ni WallahI cos yarinyar tayi sosai,

Mansur yace eh din ya isa haka Adena kiran sunar matata Kar gabanta yaita fadi LOL

   Hussain Dariya yayi yace Kaji Mansur dinnan

Mansur yace hhh ni da nakeji kamar anyi ma

Dukansu dariya sukai, Hussain yace ANGO ANGO, Wani irin tafiya Mansur ya Fara yace Ku biyo bayana, Hassan ne yace Wallahi ana ganinka silent amma bakaji fa...

Hussaini yace kabarshi rudin soyayyane ke dibanshi, Mansur yace eh din naji dai


MUJE ZUWA

   DONT FORGET TO
FOLLOW
VOTE
COMMENT

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now