SILAR GIDAN AIKI

1.6K 89 7
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

*Much thanks my dear fans...Ina ganin sakonninku 😍*

*PAGE 4⃣2⃣*

Tana gama shan ruwan ta fadi a kasa sumammiya, Mansur and Abdallah na kewaye da ita, Mansur ne Ya kalle Abdallah yace" me yakamata muyi? Kodai Mu kaita asibitine yana magana muryarshi na rawa! Wait Mugani Abdallah yace"

Suna tsugunne a wajen kusan 30mins sukaga Nazeefa bata farfado ba Dan ta mugun galabaita, Abdallah ne ya taba Mansur Dan kallon da yake ma Nazeefa ya baci kamar zai cinyeta, yace Mu kamata musata cikin muto mukaita asibiti,

"Mansur ne ya sake baki yana kallonshi kamar wani tababbe Dan shi kwata kwata hankalinshi be jikinshi, Abdallah ne ya sake magana yace MANSUR, What's wrong with you? I said we should take her to the hospital kayi shuru! Mansur yace OK let's go, daukarta sukai suka sata a back seat hade da kayanta, Sannan suka shiga motor suna tafe Abdallah na driving

Mansur ne ya hade rai wai Dan me Abdallah zai taba ta, nan take yaji yana kishin Aljanar sa, Abdallah ya lura da hakan yai banza dashi

Tafe suke Suna hira jefi jefi, Nazeefa ta farka, Tace" Dan Allah Ku kasheni, na gaji da duniyar nan, A tare suka hada baki sukace astagfirullah, baiwar Allah meya faru haka?

Nazeefa kuwa inbanda kuka ba abun da takeyi, sunyi tafiya me Nisa tace Ku saukeni anan! Mansur ne ya juya sukai 4eyes dashi nan take jikinta ya Fara rawa, Tace Aljani!! Shikkenan nasan rayuwata tazo karshe, me yasa kake so ka cutar Dani, menai maka, ba rannan na baka hakuri ba

Dukansu was surprise da sukaji maganarta, Abdallah aranshi yace" Lalle ikon Allah sai kallo, they are meant for each other
   Cuku cuku ta farayi ta naso ta bude kofar ta fita, waigowa sukai sukaga alamun fita takeso tayi, then Abdallah yai locking all d doors,

Mansur kuwa se kallonta ta mirrow yakeyi, da sun hada ido da Nazeefa ta harareshi ta murguda Mai baki, Wata sa'in har kunkunai takeyi, Shi dai sedai yai smiling

Abdallah kam Sam be Lura ba, Se faman driving dinshi yakeyi

Sun shugo cikin unguwar su, Abdallah ya daga glass din motor, Allah yasa me bakin nan ne, Wanda sedai na ciki ya hango na waje badai na waje ya hango na ciki ba,

Abdallah ya kalle Mansur yace" yanzu ya zamui? Kaga I can't take her to my house saboda matata, yanzu ya zamui? Mansur yace" dama nace ka tafi da itane? A wajena zata zauna mana! Gabantane ya fadi tace na shiga uku

   Abdallah kuma binshi da ido yayi becemai komai ba

Nazeefa kuwa tai banza dasu, aranta tana tinanin wani Abu,

Har gida Mansur ya Kai Abdallah amma be shiga cikin gidan ba yace agaida madam, Abdallah yace" plz abokina take care ni banso Ace zaku zauna da ita ba why not ka sanar da mummy? Kasan zaman mace da namiji se ahankali KO?

M.T yace" look into my eyes ni Dan iskane KO katabajin wani Abu makamancin haka? Abdallah ya girgizakai yai shigewarsa, Itadai Nazeefa na kallonsu ta glass batasan me suke tattaunawa ba

Mansur ne yazo mazaunin driver, ya Fara driving ahankali, Nazeefa kuwa in banda addu'a ba abun da takeyi,

Tafiya ya soma tace" malan Ina zaka kaini? Waigowar da yai suka hada ido taji ta kasa karasa maganar Da zatai, Kallon jikinta tayi taga riganta duk datti, gasu sun yage, nan take kunya ya kamata, Aranta tana tambayar kanta meyasa bataji kunya da dayan nanan ba? Meyasa ta kasa karasa maganarta? Waigowa ya karayi yace" Inajinki me kike cewa?

Murza Hannunta ta tafari tace" bance komai ba, Mansur kawai Smiling yayi yaci gaba da driving,

Wani babban PLAZA suka nufa, yace Mata yana zuwa, Ya kulle duka motor Dan karma tace zata Fito

Fitan dayai tabi bayanshi da kallo tace" wow Guy dinnan ya hadu fa, Ashe akwai irinsu a duniya!

Wani babban shago yaje ya siyo Mata riguna dogaye a kalla Kala 10, da takalma da jakunkuna se hijab, da kayan kwalliya da turaruka masi kyau ya dawo yasasu a bot,

Shiga motor yayi ya duba agogon hannunshi yaga 6Pm ya kusa,

Nazeefa ce tace an Kira wayarka, dubawa da sauri yayi yaga Sweetheart❤ Ohh God yace Sweetheart ne bari nai sauri

    Yana cewa Sweetheart taji duk ranta ya baci, taji haushinshi for no reason

Tafiya kadan sukai suka shugo wani layi, Wanda kana ganinshi kasan KO a masu kudin se Manya Wanda suka Kama kasa

Wani babban gida taga sun nufa yana horn, aka budemai, Mansur yace" kinga wanchan gidan? Muna zuwa daidai wajen ki tsugunna ki sauri ki shiga

Kallonshi tayi tace tab a mike Zan shiga se kace munafuka KO wata Yar iska! Hade rai yayi yace nadai fada miki

A daidai wajen yai parking yace ki fito! Kamar xata fito a tsaye setaga hallacin da yai Mata qila ta silar shi ta sama jin dadi, se tai yanda yace Mata kawai

Tana shiga yace" Alhamdulillah, karaf a kunnanta! Kallonshi tayi ido cikin ido tace Hmmmmm

Koda Nazeefa ta shiga part dinshi, kulle part din yayi dankarma masu aiki suce zasuje Su gyaramai part din suga wata, Nazeefa kam dataga yasa key samun waje tayi a tsakar gidan ta zauna tai tagumi hawaye se zubo Mata yakeyi tace wani irin rayuwane wannan?

Yanzu haka rayuwata zata kare a wahala, wannan daga gani mugune, tsaki tayi seta farabin gidan da kallo ya hadu sosai

Muje Zuwa

Don't forget to Follow
Vote, Share
And comment

Yours
*FRESHUMMIEYXEEY*

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now