SILAR GIDAN AIKI

2.1K 141 7
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*VOTE ME ON Wattpad@Freshummieyxeey*

*PAGE 1⃣4⃣*

A tsaye bawon Allah nan yake yana kallon wayarshi, ganin fuskarta yayi ya Kara kidemewa, addu'a ya Fara yi sannan hankalinshi yadan daidaita, ya tsundama cikin tinani Saiga Abokinshi nan da yake a kafa yazo Sam beji alamun tafiyar mutun ba

Ji yayi andafashi ta baya, har zai zura da gudu sai yaji muryanshi yace Mansur Turaki nine fa!

Wani doguwar Nunfashi yaja sannan ya kalla Abdallah abokinshi yace" a tsorace nake wallahi let's go home

Abdallah ya kalleshi yace wani irin tsoro? Be a man mana kana abu kamar mace, idan mun tafi gidan wazamubar wa mutun anan?

Mansur turaki se waige waige yake yace bazaka ganebane ido hudu mukai da ita

Abdallah yace ita wa? Yace Aljanna yana magana yana Kara waige waige

Abdallah ya kwashe da dariya yace I need to see  this Aljanna! Mansur Turaki yace hmm you'll never see her kuwa!

Nan Abdallah daya lura M.Turaki a tsorace yake, sai yamai hikima sunata Dan hiran addini haka har ya kawar Mai da tsoron, suna Hira saiga masu gyaran motor sun iso Suka gyara musu sannan suka tafi gida!

Suna Isa gida M.T jikinshi ya rikice kamar me aljanu! Hankalin hajiyarsu ya tashi sosai, take tambayan Abdallah meye faru

Nan Abdallah ya kwashe komai ya sanar da ita

Yace" ina hanyane ya kirani wai nazo ya hadu da aljanah,

Hajiya Zainab ta zare ido tace aljana kuma? A Ina? Kaga saiyasa banaso ya fita shi kadai, Yace yes that's what he told me, Wai yana hanyane motarshi ta lalace shine ya tsaya kafin masu gyara suzo shine ya ganta

Hankalinta ya Kara tashi balle yanda M.T yake ihu yana gatanan...gatanan hannunta tasa A fuskarshi tana karontamai addu'o'i

Waya Hajiya Zainab ta dakko ta sanar da dad dinshi, yace OK yanama Hanya but yana ta makaki

Abdallah ne ya temakawa Mum suga shigar Da shi daki, Jikinshi sai rawa yakeyi wannan kenan!
   
                        ****
     Bangaren Nazeefa kuwa itama ranar wuni tayi inbanda waige waige ba abun da takeyi, Abincima dakyar ta samu ta gama Dan ranar Baban su Mubin zai dai dawo! Dan haka ranar ga tsoro ga Tasha wahala wajen girki

mubin ne yasha wanka yayi kyau Ana jirar isowar Dad in banda murmushi ba abunda ya keyi

Nazeefa kuwa tana daki da yake tasha aiki ta gaji,  itama shiga wanka tayi, ta fito tazo ta shafa Vaseline abunta, ganin bawanda zai shugo dakin tasa Dan vest dinta da wando kayan ya amshe jikinta sosai

Saboda lokacin Zafine, Shingida tayi a yar katifan dake dakin ta shiga tinanin iyayanta Ko sunada rai Ko sun mutu oho, Janyo akwatin ta tayi Dan Kara bincikar numbern wayan mahaifinta da zatazo aka    bata but she couldn't find it, Hakanan ta mayar da akwatin ta kwanta, Tino Aljanin datai acikin mota tayi kamar yana Mata gizo, Kwalla ihu tayi ta fita da gudu shi kuma a daidai lokacin Mubin ya zo wucewa zai shiga kitchen, fitowar da tai ta bigeshi dukansu suka fadi

Gaba dayansu wani Shocking sukaji a jikinsu, Nazeefa data kalle fuskar mubin Kara rikicewa tayi taga fuskarshi gaba daya ya koma na Aljanin data gani, kankameshi tayi sosai tana ka barni, Ka kyaleni plz bazan Kara fitowa ba

Mamaki mubin abun ya bashi gashi ta rikeshi gam kuma tana ya saketa me take nufi? Sundau lokaci a haka sannan ta sakeshi ta shiga daki, Mubin kuwa hankalinshi tashi yayi kitchen din da bai shiga kenan ba ya koma daki

Feelings (Sha'awa) sosai yakeji ya rasa inda zaisa kanshi, balle idan ya tino irin kallon datakemai seya kara rikicewa, sedayai sosan gaske sannan ya daidaita kanshi, tinowa da lemon din dake fridge dinshi yayi cos yana rage feelings tashi yayi ya bude Dan fridge din da yake dakinshi ya dakko lemon din yasha sannan yadanji relief but Son Nazeefa kuwa sai Kara ruruwa yake a Heart dinshi,

Ita kuma Nazeefa na shiga daki kulle kofarta tayi, kuka Sosai takeyi duk Taji ta tsana aljanin da ta gani Dan shi yai Mata causing din duk abun nan, Tsaki tayi ta share hawayenta

Sannan ta tashi ta chanza wani kayan, kwata kwata ta kasa natsuwa a dakin se leke takeyi ta labule, tsoron sosai takeji gabanta sai fadi yakeyi like something terrible is going to happen......

PLEASE COMMENT DINKU YANAYIN KADA










YOURS UMMIEY XEEY

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now