SILAR GIDAN AIKI

1.2K 71 5
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

*PAGE 6⃣6⃣*

  Washe gari Su nazeefa sun tashi tun asuba se shirye shirye sukeyi, Dan haka tai switch off din wayarta gaba daya, Makota sai zuwa sukeyi, Haka kawarta tazo se kuka takeyi wai zasu rabu tasan ta tafi dinnan se ansake ganinta,

Nazeefa sedai tai smiling tace Zan dinga zuwa inshaa Allah, haka suka tattara kayansu, Sukasa a gefe, Sannan Baban Nazeefa yace ki Shiga Chan gidan Ki kira maman Su Usman, tace to shiga gidan tai sai ga shi sunfito a tare sun shugo gidan Su Nazeefa, dad din nazeefa yace zamu tafi birni ga gidan nanan na baki halak malak, ki zauna da marayun yaranki, ga number wayatanan dana Nazeefa duk Abunda kike bukata ki bugo ki fadamun, Allah ya tsareku, mijinki mutumin kirkine ya temakeni sosai a rayuwa, malama lamunde ta fashe da kuka tace nagode kwarai, Allah ya saka da alheri Yace bakomai

Makota kuwa se Mai godiya sukeyi, Yace kuma zaizo nan ba da dadewaba a gyara babban masallacin unguwar da yake neman gyara

Nan ma sukace Alhaji Nalado Allah yaja kwana,  Allah kuma ya biyama bukatunka na alheri yace Ameen, Sannan Ya bisu da kudade masu yawa nan ma yasha addua yace bakomai ai Ana tare

Sannan Nazeefa itama taba kawarta kaya tabata kudade Tace ta kula da kanta, idan tana bukatan wani Abu ga number dintanan ta kirata cos bazata taba mantawaba lokacin mahaifinta nada rai Nazeefa gidansu take zuwa suci dadi kuma duk abunda babanta ya siyo mata seya siyowa Nazeefa,

ansha yan koke~koke Baban Nazeefa yace ai basun tafi kenan ba zasu dinga zagayowa inshaa Allah

Sannan suka Dan tsagaita da Kukan

   Bangaren Mansur turaki kuwa, Tun asuba yake kiran numbern Nazeefa shuru, hankalinshine yai matukar tashi, Tinani kawai yakeyi, jikinshi yadau rawa ga wani zafi sabon zazzabi ya kamashi

***
Su Nazeefa sun gama shiryawa Babanta ya dauka waya ya Kira Baban Mubeen yace gasunan yanzu zasu taho "yace OK

Kiran mubeen da faeez yayi yace Su kasance cikin shiri, nan da kamar 4 hours suje garrage su dauko Su Nazeefa, Faeez aranshi yace Alhamdulillah, Mubeen kuwa Daki ya shiga yai smiling yace Kwalliya zanyi cos kafin taga saurayinta nizata Fara gani...Lol

Sannan dad din Su mubeen ya kira Hajiya asmau Da faeeza yace Su shiga kitchen Su daura musu abinci dan they are on thier way, Faeeza taji dadi sosai saboda nazeefa zata dawo, Dan haka basu bata lokaci ba suka nufa kitchen, Farsusun gaji akai sannan aka soya wasu, sai jallof rice da sukai yasha hadi sosai KO ina ya biye da kamshi
Da wani hadadden Apple juice

After 4 hours
      Baban Nazeefa ne ya Kira Baban Mubeen yace gasunan suna gab da tashar moto, Yace Alright

Dad mubeen ya kirasu dukansu yace sunkusan karasowa, yanzu abunda zasui shine su dakko abincin duka Su tafi Chan gidan Su Nazeefan, idan sun saukesu then saisu Wuce Su dakkosu Sukace OK

    fito wa yawa gaba daya sukai, Mubeen ya saukesu sannan suka wuce Moto park da faeez

Suna Isa KO 20mins ba suiba saiga Su nazeefa, Sa Sauri sukaje wajensu sukai musu sannu Da zuwa sannan suka dauka kayan suka sa musu a bot

    Mubeen kallon Nazeefa kawai yakeyi

yaga ta Kara kyau, ta rage haske ga boobs dinta daya fito sosai da hibs dinta kodan ta ramene ne Oho, aranshi Alhamdulillah yace

   Tafiya sukai kadan suka shugo cikin unguwarsu

Wani tanfatsetsen gida nazeefa taga mubeen ya tsaya

Faeez ya fita ya bude Mai gate, Sake baki nazeefa tayi hardasu Umma suna mamakin Wai nan gidansune, A zuciyata nace Baku shiga cikiba ma tukunna

   Samun parking space yayi, Sannan kowa ya fita, Azuciyarsu sunata Alhamdulillah

Shiga falon sukai, Kowa bin dakin da kallo yayi, gidan ya matukar haduwa, duk kyan Gidan alhaji bawa me kada kwana casain to  gidansu nazeefa ya fishi kyau, Suna shiga dakin wani kamshi ta KO Ina abunka da sabon gida

Nazeefa ce ta Fara lekawa duka dakunan taga wow sunyi kyau ga dakinta Da take ganin yafi na kowa kyau, Falo da dawo tace gaskiya gidan yyi kyau Masha Allah

Babanta kuwa ya kalle Baban mubeen yace sannu da kokari gaskiya gidan ya yi sosai

   Dad mubeen beci komai ba sudai suna gefe

Nazeefa kuwa se rawan Kai takeyi Kamar karamar yarinya, Mubeen kam se kallonta yakeyi Dan idan taka behaving like small child Kara shiga ranshi takeyi

Duk giftawar KO motsin da nazeefa tayi se mubeen ya bita da ido, Dan yanzu ta cika ta KO Ina Masha Allah




Muje Zuwa

More Comment please

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now