SILAR GIDAN AIKI

1.1K 70 6
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad #Freshummieyxeey*

*PAGE 7⃣6⃣*

Biki nata matsowa, mahaifin Mansur yasa an gina musu gida kusa da nasu, Flat ne me 3 bedrooms gidan ya hadu matuk'a se wanda yagani

Tunda bikin ya matso Mansur kullun yana makale da nazeefa a waya ba abunda ke rabasu se bacci shima cikin baccin to mafarkin junansu sukeyi

Bangaren Mubeen kuwa, Tinaninshine ya rabu biyu yanason Ameerah amma wata zuciyar tana ka hakura da ita kawai ka nema wata, mubeen ne zaune a wajen ginin makarantar da akemai yaji bazai Iya hakuraba, shi duk abunda zai faru zaije ya sanar da ita yana sonta idan ma wani ya rigashine ya sani dan kar yai 2 zero, Daukar motarshi yayi ya tafi kofar gidan su Ameerah ya tsaya, wani yaro ya Kira yacemai please ya shiga ya ce Ana kiran Ameerah yaron yace tom

Shiga yayi yaron yai sallama yace wai ance Ameerah tazo, Nazeefa suna zaune da Ameerah suna hiran yanda bikin Zai kasance

"Ameerah tace Ni kuwa? Yace Ameerah akace, Amira bata yardaba dai tace ya mutumin yake? Yaron yace Farine dogo

Dukansu basu kawo Mubeen bane, Nazeefa da rawan jiki ta dauka gyale tace Bari na rigaki ganinshi idan yamun shikkenan ko kawata nasan zai miki kema

Ameerah binta da ido tayi tana dariya tace kawata bakida dama wlhi ganinan fitowa nima, AI bata jirataba ta dauka gyale ta fita

Kanshi na kasa dan kasa dagowa yayi sui 4 eyes, Sallama yai mata kamar haka, Salamu Alaikum gimbiyar Mata! nasan zaki mamakin ganina anan Kiyi hakuri

yaji anmai shuru

D'ago kan da zaiyi sukai 4eyes da Nazeefa

Tace Bro dama Kaine? Dan tsuke fuska yayi aranshi yana da yasan zai sameta da baizoba, Nazeefa kuwa kallonshi takeyi abubuwan da suka faru a da take ganinshi a idanta, Da sauri tabar wajen

Zata shiga cikin gidan kenan sukaci Karo da Ameerah, Har Ameera na tsokanarta tace kinga guy din yayi kuwa? Wani kirkiro murmushi tayi tace inkinfita zakiganshi

Nazeefa shugowa dakin Su Ameerah tayi, Waje ta samu ta zauna tafara tinanin yakamata tabar kishin nan, Mubeen bazai taba zama nataba, Kuma da take ganin shi mai laifine ai dukansune da laifi, tunda har itama zatai aure to why not tabar shi shima ya aura kawarta inhar tana sonshi

Kuma da ace matar natuba tana rasa miji tabbas itama kuwa baza'a auretaba so tacire komai a mind dinta, Kawai ta fuskanci gaba, Allah ha yafe mana gaba daya Ameen

Dakko wayarta tayi takira Mansur suka Fara hirar soyayya taji sanyi aranta, har yana tsokanarta saura kwana nawama? Tace kafini sani sukai dariya dukansu

***
    Ameerah kuwa tunda ta fita taga mubeen gabanta ya Fara fadi, Kasa tsayawa dakyau tayi, Sallama yai mata ta amsa muryanta na rawa

Murmushi yayi yace like you're not comfortable ko? Girgiza kai tayi alamun a'a

Magana suka suma ya sanar da ita manufar zuwanshi ne, shi da gaske yake aurenta yake so yayi, Aran Ameerah taji dadi sosai dama ba wani soyayya take soba indai miji ya fito da gaske ze aure ta shikkenan,

Amma tadan yi shuru agabanshi kamar tana nazarin Wani Abu

Malama Ameerah yace Ya akaine ko dai akwai takurane? Cemai tayi a'a kaga yanzu bazan yanke hukunci ba dole senayi magana da magaba ta na, yace hakane zuwa yaushe zanji amsarki?

Tace kamar Sati daya Yai murmushi yace Allah yasa muji alheri tace Ameen sannan ta shige gida

Shi kuma driving ya Fara yahau kan titi yana tinanin AI dakyar zata amince saboda yaga Nazeefa a gidan and he is sure ta fadama mata abunda ya taba shiga tsakaninsu

Yar karamar tsaki yaja yace tabbas ka zama na kirki ma babban abune saboda yau da gobe duk abunda ka aikata seya fito, Allah ka yafemun yace Sannan ya Fara istigfari har ya Isa gida be dena ba

Ameerah jikinta a sanyaye ta shugo dakin ta tadda Nazeefa na waya

Fizge wayar tayi ta kashe tace mayyar love bakya gajiya?

Nazeefa tace laaa dama Ana gajiya da abun da kakesone?

Ameerah tace a'a

Nazeefa tace kingani

Ameera  tace Amaryanmu kinsan menene?

Nazeefa tace a'a Ameerah tai shuru ta kasa fadan ma Nazeefa maganar

Wani murmushi Nazeefa tayi tace kinwani yi shuru ni nasan komeye, Ba auranki yakeso yai ba?

Maganar taba Ameerah mamaki sosai gashi ba dama ta karyatata, Tace Kamar kinsani cikin wani irin murya Tace Ni bazan Iya auranshiba saboda ke nasan you still love him shima haka so Ni bazan Kara fita bama gaskiya

Nazeefa ce ta dafa kafadarta tace wayace miki haka? Kinga sonshi idonane? Ko kingani a idonshi? Kawai kinsan Mu yan uwane dole akwai so dinnan amma wallahi ki aureshi bakomai indai kina sonshi.

    Kallonta tayi cike da mamaki, Bata taba tinanin hakan ba, rungumeta tayi dan farin ciki, Nazeefa tace bakomai kawata kin wuce haka
Allah ya tabbatar da alheri

Tace Ameeen


Mune zuwa

   _Yan uwa ya mukaji da wannan annobar, Allah ubangiji ya kawo mana karshensa, Allah kuma ya Kara tsaremu, Allah ya shiryamu shirin addinin musulunci, Mu yawaita istigfari👏🏼_

#FreshUmmieyXeey

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now