SILAR GIDAN AIKI

1K 68 6
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad #Freshummieyxeey*

*PAGE 8⃣0⃣*

Tun Ana jibi bikin yan uwa na nesa suka fara zuwa, gida kam ya cika da jama'a kowa se neman Nazeefa yakeyi sedai ace batanan,

   Bangaren gidan su Mansur kuwa shima iyalan Me martaba Sarki duk sunzo ciki harda hassan da hussaini, Su suhailat kuwa ance baza a zo da suba suna chan sunata fada tsakaninsu, Anata shirye shirye amma Sam hankalin Mansur yai matukar tashi yau kwana daya bege beloved dinshiba, Damuwa ya shiga sosai, kuma beson kowa yason halin da yake ciki, Su Hassan se damunshi sukeyi ina amarya sedai yace Na boyeta banso aganta Lol

    Daki ya shiga yanata neman numbernta gaba daya ta kashe, Aranshi yace Nazeefa so kike ki kasheni!

Bangaren Mubeen kuwa hankakinshi kwance, Yana faran ciki Ameerah ta amsa soyayyarshi Dan haka ya tashi ya shirya, kiranta a waya yai tamai kwatancen gidan yace gashinan zuwa, Tace OK

Ba'ai 30mins ba se gashi ya iso gidan, kiranta yai a waya ta fito, bayan sun gaisa yace ya shirye shirye? Tace Alhamdulillah sannan yace Ina Mai kara Godiya da Kika amince da soyayyata, Allah ubangiji ya barmu tare tace Ameen,

Mansur ne ya danno motarshi kan layin su Ameerah, tun dada nesa Mansur ya gane mubeen ne a wajen Dan haka ya fasa zuwa wajen Ameerah, aranshi yana wato nan wajen ya lallabo ko? AI gwanda hakan badai Nazeefa na ba kam,

Hakanan ya juya yaso Yaje yaji meke faruwa, wata zuciyar kuma tacemai ai kasan abunda Kai Mata, Samun waje yayi yai parking yana mai nadamar abunda yai mata ga wani feelings dake damunshi, shidai ayi ayi a daura auren nan ya huta lol,

Da sauri ya tada motar ya karasa gida, Daki ya shiga ya bude fridge din dakinshi ya dakko lemon yasha Dan feelings din da yakeji ra ragu, Hassan da hussaini suka shugo, zuru zuru yai da ido sukam sunsan manufarshi kwashewa da dariya sukai, Hassan yace Ango Ango! Mansur ya harareshi yace wlhi kun fiye sa ido, Dariya sukai sukace Kai kuma ka cika zalama ba! Yace eh din.

    Barin dakin yayi saboda tsiya suke tamai,Kiran abokinshi yayi Abdallah yace yana Ina? Abdallah yace Ina gida yace ganinan zuwa,

Koda yaje gidan Ina amarya yace? Yace ta raka Nazeefa wajen gyaran jiki,

Mansur yace OK, dama inata kiran wayartane a kashe kadan kiramun matarka se taba nazeefa mui wayar yace OK, kiranta yai jikinta na rawa da Iya kwarewa cikin salo da yanga tai picking, hello Sweet Heart
"Yace yes my love, yace Ina Nazeefa tace gatanan, yace kibata mansur ne keson magana da ita tace OK

Kara Mata wayar tai a kunne taji muryar Mansur, Gabantane ya fadi tadai daure suka gaisa seta Fara hello hello banji kamar network prblm

Mansur yace please kinajina, Tuni tai cutting din call din, tama kashe wayar Matar Abdallah gaba daya ta ajiye a jikinta tace zai Kira network ne

Mansur sororo ya tsaya amma yai ta maza bece komai ba, yace Abdallah zo muje mu amso dinkinmu dazu tailor din ya kirani yace OK Muje sukai tafiyarsu

***
   Cousins din Mansur ma sunzo maza da mata, A cikinsu akwai Ummie tana bala'in Son Mansur Dan ita Sam bata yarda da Mansur zeyi aureba, cos suna yawan waya komai take so yana Mata, ita ta aza sonta yakeyi...toofaa

Koda suka zo gidan kiranshi a waya tai tace Ina kake munzofa, yace da gaske sist tace zanma karyane hardasu Aisha, maryam da rukky, Yace ganinan zuwa yanzun nan naganku

Tace OK
    Ba'ai 30mins ba yadawo, yana shugowa yaga yan uwa sun zauna se hira sukeyi, ummine ta  mike tamai oyoyo ta rungumeshi, Gidan aka fara Ango ango

   Kakarsune ta fito tace Ina angon yace tsohuwa mai ran karfe, kindai qi mutuwa se kinga aurena KO

Tace yoo nan gani nan bari danma bance dani za'a daura auren ba, suka kwashe da dariya, tace Ina kishiyar tawa

Yace na boyeta saboda irinku, karku goga mata tsufa, tace Yaro a sannu dai, haka suketa hirarsu har dare tayi, Still yanata kiran amaryanshi waya a kashe

     Hakanan Mansur yai kwana biyu besa Nazeefa a idonshiba, ita ma dukda tanason ganinshi hakanan ta hakura, deep inside her heart itama tasan tana missing dinshi sosai

But yazatai hakan shine daidai saboda gudun aikata aikin dana sani, tasan Mansur sosai idan suna haduwa yana yawan Mata maganganu balle kuma yanzu idan yaganta AI kara rudewa zaiyi...

    Ameerah da Mubeen a yan kwana biyun nan sun bala'in shakuwa Kana ganinsu basai ance maka lovers bane idonka zai baka amsa!
***
    Ana gobe za'a daura aure Nazeefa ta bude wayarta, tana budewa Mansur ya kirata, Picking tai cikin yanga da kasaita tace hello cikin sanyin murya

A gigice yace my princess Sannan yai ajiyar zuciya yace Please kiyi hakuri Dan Allah inganki I'm badly missing you! Tace uhm Bata sake cewa komai ba hakuri yaketa bata sannan tace to sedai kazo anjuma da dare, Wani ajiyar zuciya ya sakeyi yace OK my one and Only

Fitowa yai tsakar gida anata hada hada yaci Karo da ummie, Tadan tsuke fuska yace what's wrong my sist? tadan juya taga ba Wanda ke kallonta ta Fara hawaye tace bakai bane!

    Yace zo muje ki fadamun waya tabamun kanwata, Fitowar waje sukai ya dauka mota suka tafi yace muje kisha ice cream ko? Da yake marainiyace yana sonta sosai dan tana bala'in bashi tausayi, ta zumburo baki tace ni ba ice cream nake soba Kai nakeso yaya! Kai nakeson aura meyasa zakaimun haka

Jiyai maganar tamai nauyi, Kasa tada motor ma yayi, tsayawa yai yana kallonta yace ummi, na dauke  as a sister nefa, Wannan abun da kikaga inayi nafifitakine akan kowa, Kinsan sauran har haushi sukeji ko? Sannan yai shuru

Fashewa da kuka tayi ta sauka a motar taje wajen kakansu, Tanata Mata kuka! Shi ko Binta da ido yai kar fa ta kwanto mai ruwa Dan za'ai drama ne wallahi, Tsaki yayi yai ficewarshi

Ummie kuwa in banda kuka ba abunda takeyi, dakyar kakansu ta lallasheta tai shuru

Gidan su Nazeefa suma ya cika fal, yan uwa da abokan arziki kowa ya hallara, wajen 4 Nazeefa suka shugo gidan, All eyes on her tai bala'in yin kyau kamar balarabiya, sassanunku tace musu kowa Binta da ido yayi Dan wani kyau datai

Shiryawa sukai suka wuce inda zasui bridal shower, Anyi cake, Meat pea, samosa da pepper meat ga drinks na roba da ruwa ansha anci Masha Allah, Kowa Cewa Nazeefa take tayi kyau

Bayan sun gamane suka koma gida, misalin karfe 8 na dare saiga Mansur

Kiranta awaya yai ta fito da kayan  bridal shower din, Kura mata ido yai, Yana Anya kuwa nazeefa ne!

Shugowa tai ta zauna fuskarnan babu Fara'a ta gaisheshi, ya amsa yace haba Mata na nace afuwan fa! Uhm tace, juyawa da zatai sui magana dukansu sukaji wani irin a jikinsu, Dan Nazeefa ma kasa motsi tayi, hannunta ya rik'e yace dear kinyi kyau sosai, tsintar kanta tai ta kasa cemai komai,

Dayaga batada shirin ma magana, yace kawai nazo nagankine kuma kinyi kyau nizan tafi sai gobe Zamu hadu!!! Gabantane ya fadi tai saurin dago kanta suka Kara hada ido

Sauka tai a motar jikinta duk ba wani kwari,

Shikam yai tafiyarshi yana smiling Kome yake ayyanawa aranshi shi yasani

tana shugowa gida tai kwanciyarta bacci yaqi zuwa itama ko tinanin me takeyi ohon Mata

Muje ZUWA

THANKS

DON'T FORGET TO.
FOLLOW
VOTE
COMMENT...

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now