SILAR GIDAN AIKI

1.4K 84 6
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

Afuwan 2days kunjini shuru Ina Dan busy ne ne❣

*PAGE 5⃣1⃣*

Ganin tinanin zanyi mata yawa ne yasa ta dawo parlour tazo ta zauna Kusa da mahaifiyarta sosai taje kamar zata shige jikinta, Tace mammah nah nayi missing dinki sosai fa, Ina sonki, rungomota tayi tace bayan mun miki laifi ko ince na miki laifi, inadai Kara neman yafiyarki, Cewa tayi laaa kamar karamar yarinya Tace bakuimun laifi ba nikam, Yauwa tace Mama munyi magana da Wanda ya zo dazu taqi fadan sunanshi

Da yake sun gane wanda take magana sai suma suka share

Taci gaba da magana Tace tace" wani shawara zaku yanke ya kamata musan abunyi, Malan Nalado yace to Alhamdulillah kawai Mu yafe musu, Yanzu ai tun ba aje KO inaba Allah ya nuna musu KO ya kikace Hafsatu?

Umma Tace" Ehnmm Hakane gaskiya, kawai a kyalesu Duk Wanda ya rike Allah zai ta ganin haske ne, sune a kasa

Wani Mikewa Tsaye Nazeefa tayi Tace umma da Abba bangane a yafe masu ba duk wahalan da suka jefamu, na tabbata harda wahala ya Kara sa kuka tsufa tana magana cikin shawaba tace  ni gaskiya ........ Ta zunburo baki ta tashi ta shige daki inyeee Su Nazeefa an zama butters lol

Binta da kallo sukai, Umma Tace ke yarinya ce, Bakisan meye duniya ba, Malan nalado kuwa binsu da kallo kawai yayi

    Hiran Su suka ci gaba, Nazeefa kuwa na shimfede a kan gado, Tinanin Mansur ta farayi, je tai inama suna tare, she loves him from the button of her Heart, gaskiya ba karya ita kanta tasan sun dace

    Bangaren Mansur din ma hakan take Dan gaba daya komai nashi ya maida Nazeefa, password na wayarshi, Na laptop Kai harta screen din wayarshi ma Nazeefa ce akai, sonta a jininshi yake sosai, he loves her irin totally dinnan, but idan ya tuno wani abun kuma sai yaji Anya iyayanshi zasu Bari ya aura Nazeefa, duk dadin da yakeji idan ya tina da kamar wuya a bari aureta se yai shuru yaita addu'a

Bayan kwana Biyu
Mansur ne ya Kira Abdallah yace su hadu a wajen A & B PLAZA Kamar karfe 10 na safe yace alright

    Kasancewar weekend ne ba aiki, Abdallah suna kwance da matarshi tayi bacci ya zame jikinshi ya shiga wanka, ya shirya yasa light brown colour shadda yayi kyau sosai, ya dakko hula ya saka,

Bacci takeyi taji kamshin turarenshi ya buge hancinta ta farka

Tsareshi da ido tayi tace banganeba Ina zaka kuma yau weekend?

Kusa da ita yazo ya zauna yace kiyi hakuri these days zanyi busy sosai, saboda muna binciken wani Abu ne

Tace banganeba kai ba Dan jarida ba amma kullun bincike

Rungumeta yayi, yace yes hakane amma kiyi hakuri I'll tell you everything Bari dai komai ya lafa kinji matata, Smiling tayi Tace OK bakomai, Halan kaida Mansur ne KO? D'aga Mata Kai yayi alamun eh tace dama ai nasani, Aminan juna, Allah ya Baku sa'a ya temakeko yace Ameen sannan yai ficewarshi

Napep yahau ta tafi chan, Yana sauka yaga Mansur a cikin motarshi,

Wajenshi ya Nufa suka gaisa yacemai ya Madam, Abdallah yace Alhamdulillah tana gaisheka

   Wani babban shago IPhone suka nufa, nan Ya siyowa Nazeefa waya IPhone latest one, sannan ya biya Company MTN da ZAIN yasai Mata layuka duka biyu Yai mata register,

Abdallah ne ya kalleshi yace yauwa Mansur ya aka karene da mutanan nan? Yace dama yanzu nakeson muje gidan tare dakai duk abunda suka yanke shine daidai

Suna cikin maganar ne telanshi ya kirashi yace angama dinkunan da ya basu yace wow da sauri haka?

Sukace yes ranka shi dade, yace OK to gashinan zuwa,

Direct shagon suka nufa suka amsa kayan, Sannan suka wuce gidan Su Nazeefa.

Me gadi yana ganin motor yasan na waye da sauri, Yaje ya budemai yace ya shugo dashi kawai, Nazeefa tace duk sanda yaga motor ya budemai ya shiga

   Parking space ya samu,  Nazeefa na ganinsu, tace Umma mutumin nan yazo Bari inje, Sukace OK

Fita tayi wannan karon gyalen abayar ta yafa, Tun fitowarta Dukansu suka bita da ido...Tsabagen kallo Mansur har yana sauke glass Dan gaba daya ta chanza bazakuce Yar aiki bace da! Mansur yaga Abdallah nata kallonta

Wani kishi yaji yace Malan take your eyes off wannan kaya nane!

Bin Mansur da kallo yayi yace da yake nima inada kayan ai, dukansu dariya sukai adaidai lokacin Nazeefa ta karaso,

Wani kallo da mubeen yai Mata jitai kamar ta nitse kasa Dan wani yanayi taji yanabin ilahirin jikinta,

Sannunku da zuwa tace sukace yauwa, Abdallah yace gimbiya sarautar Mata rufe ido tayi

Mansur yace kaga daga zuwanta zaka daman mun ita KO? Ita kam kunya taji ta rufe fuskarta

Yace well Nazeefa ba zama mukazo yi munzo nan akan maganar mutanan nan ya muke ciki dasu ne? Tace yeah jiya dama munfara maganar dasu umma baridai na kirasu

Mansur yace noo Bari Mudai Mu shugo, Tace OK

Tai tafiyarta Mansur ya bi bayanta da kallo yana lashe baki, Abdallah ne ya bigeshi yace gidan sirikan mu kake fa, sosa keya yace Ohh

   Fitowa sukai ya umurce  Abdallah daya temaka Mai Su shiga da kayan Daya amso wajen dinki

Abdallah na gani yace sannu Da kokari Na Nazeefa yace yauwa

Fito da kayan sukai Daga bayan boot suka nufa falon, suna zaune suka gaisar dasu suka amsa sannan su umma sukai musu godiya akan kokarin da sukai musu

Mansur yace bakomai, emm umma da Abba nazone Mu tafi Chan inda aka kai mutanan nan

Yace yauwa Dan nan Allah yama albarka,

Zasu tafine yace ga wannan kayan na kawo muku, suna budewa Nazeefa taga ai kayan da suka je tarane suka siyo har an dinka lalle Mansur

Nan Su umma suka mai godiya sosai, sukaimai addua sukace dama basu Dana chanzawa

   Sannan suka tashi suka tafii






FOLLOW
VOTE
COMMENT

freshummeyxeey🕴

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now