SILAR GIDAN AIKI

1.4K 94 12
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

   *Ina ganin ruwan comment Ina godiya sosai*❣👌🏼

*PAGE 5⃣2⃣*

Nan Su Umma sukai Mai godiya sosai, sannan sukai Mai addu'a sukace dama basu dana chanzawa sungode!
   Nazeefa kuwa na tsaye a wajen tinanin kokarin da sukeyi akanta take,

Sai taji muryan Mansur yace zasu tafi tace OK

Da zasu tafine Nazeefa ta rako su har bakin inda sukai parking motar Su, Abdallah ya bude site din gaba da zauna

Mansur kuwa bude mazauninshi yayi ya dakko ledar wayar ya mika mata yace idan kin shiga gida sai ki bude, Tace to yalladabai tana magana tana murmushi shi kuma yana binta da kallo hade da d'aga Mata gira

Tana tsaye a wajen seda suka fita sannan ta shiga cikin falo dinsu, Mansur kuwa inbanda murmushi ba abun da yakeyi Dan duk sanda suka hadu Kara kwarjini takemai sosai

     Tafiya suka Fara, Abdallah yace" ni harna Fara gajiya da soyayyan nan naku kawai ka fito kui aure nima na huta

"Mansur wani dariya yayi yace" ai soyayya bakaga komai bama tukunna se randa na mallaketa, Abdallah yace" Mansur kenan Ana ganinka shuru shuru ni kadai nasan halinka, "Mansur ya kyalkyale da dariya

     Nazeefa kuwa Tana shiga falo kusa da mamanta taje ta zauna, Ta Fara bude ledar da mansur ya kawo Mata, Zare ido tayi hade da wani ihu ta dafe kirji tace nice da IPHONE 11, Kai Alhamdulillah tana maganar tana Kara kallon wayar

   Mamantace tace mugani, ta mika mata Tace Kai amma wannan wayar dakyau take! Masha Allah, babantama yace mugani ta mikamai,

Nan take mahaifinta ya Fara tsoro yace nifa bancikason saurayi na maki kyautaba gaskiya, inda gaske yake Kawai ya fito, ta Dan hada rai tai kamar bataji me yake cewa ba

Wayarta taji ta Fara ringing tana dubawa taga ansa MY LOVE Ta san ba kowa bane Mansur ne Dan haka ta tashi ta shiga daki ta amsa wayar yace, love please idan badamuwa kuzo court kaza Ina jiranku ayita ta kare kawai

Tace alright gamunan zuwa ta kashe wayar tasaka a chaji, sannan tazo ta sanar da iyayanta ance suje court kaza ta fada musu, sukace to muje ke ba kinsan wajenba? Sai ki mana jagora Tace OK,

Fitowa sukai suka sama napep, sukaimai kwatancen inda zai kaisu yace badamuwa

Tafiya sukai na kusan 20mins sai gasu a babban koton, Suna shiga saiga Mansur da Abdallah suna jiransu, Sallama Su Nazeefa sukai musu sannan Su kuma sukai musu jagoranci har cikin koton

Suna shiga saiga Su Baban Mubeen da iyalanshi dasu Hajiya Hadiza Da yarta duk an tsaresu idon kowa kamar an musu duka Dan yayi Jajir

   Wani banzan Kallo Nazeefa ta jefawa Haleema, sannan ta dawo kan Mubeen shima ta balla Mai harara, kallonshi sosai takeyi sai taji idonta na shirin fitar da hawaye, a ranta Tace Mubeen Ashe Kai Dan uwanane ka wulakantar da rayuwata! Tana cikin tinanin hakan ne sai Alkali ya kirasu yace suzo yanason magana dasu...ya yanke Mata tinani

Yar karamar tsaki taja, mubeen kuwa na kallon lips dinta, hanjin cikinshi ya Kada

   Su suna gefe a ajiyesu

Su Nazeefa kuwa suna Magana da alkali, yace yau ne za yanke musu hukunci kun hakura ne KO KO kunasone a hukuntasu?

Malan Nalado Yace ah'ah mun yafe wallahi kawai abunda nakeso shine Ku kwacemun dokiyoyina kuje dashi duk inda yai ajiya ya fitomun da abuna tunda hakki nane, Nidai na yafe

Umma hafsatu ma Tace ta yafe itama

Nazeefa kuwa yanda ta cika ta batse Tace ita Sam bata yardaba wannan ma ba yi bane, sai an wulakantasu, Dan kasheta sukaso suyi, nan take ta magana ta inda ta shiga banan take fitaba gaba daya ta rikice

Da Su mubeen sun kalleta se hanjin cikinsu ya kada Dan sunsan abunda sukai Mata da wuya ta hakura

Umma da babanta daka Mata tsawa sukai, nan ta fashe da kuka wai ba ai Mata adalci ba da yanzu sun kasheta fa

Lauyan yace to Kawai kui hakuri yanda takeso haka za'ai ai yancinta za'a kwato Mata

Abdallah da Mansur kuwa suna tsaye suna kallon ikon Allah

Su Mubeen kuwa tuni ya gama tsurewa Dan wani cikinshi da yaji ya na murda mai Dan idan yai motsi da yawa zawo zai Iya zubowa,

Haleema ma idonta yai zuru zuru Dan tasan today na today zasusha kashine

Umma Tace Nazeefa bake mukewa magana ba?  Tace umma please kiyi hakuri suji idan da Dadi

Lauya ya gama rubuce rubucenshi yace to shikkenan Ina zuwa

Mansur ne ya kureta da ido yace Nazeefa zo kiji, waje suka fita, Allah yasa ba kowa yai kneel down ya roketa da Allah da annabi akan tayi hakuri,

Da sauri tace huh kayi hakuri ka mik'e kar wani ya ganka, yace bazan taba mik'ewa ba har sekince kin hakura

Hawayene ya zo Mata Tace bakomai na hakura, Amma kasan wahalan danasha kuwa

Yace nasani kiyi hakuri, ki tuna munawa Allah laifi amma ai yana yafe mana, Tace to shikkenan

Suna shiga court din sega lauyan ya fito yace meye final decision?

Kanta na kasa tace na ha kura amma se sun fitar mana dakoyoyinmu

Lauya yace angama

Kiran Yan saida sukai aka sasu a gaba sukai gida Dan ya bata takardun komai da komai







Kuyi manage na Gaji

Muje zuwa🤸🏻‍♀

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now