SILAR GIDAN AIKI

1.7K 97 5
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

PAGE 1⃣9⃣

Maganar da Nazeefa tayi Yai bala'in batama Haleema rai daurewa tayi tace" kinji kunya dai, Nazeefa tai tafi tace kedai kikaji kunya, me biyo saurayi har cikin gida Ashe bakida class, Haleema maganar tai Mata zafi takai Tafin hannunta kan fuskar Nazeefa ji kake Tass, Itama Nazeefa ta rama Tasss tasss har sau biyu
     Haleema tace ni kika Mara? Nazeefa tace yes who are you, an Mara din banma kinci darajar cikin gidane da ace a titin gwamnatine sekin fi haka dakuwa kuwa, Haleema ta janyo Nazeefa, zasu Fara dambe Saiga mubin ya shiga tsakiyarsu,  Haleema taji dadi kamar me Dan badan Allah ya kawo mubin ba tasan zata daku ne, cewa yayi meye haka kukeyi, Nazeefa tai tsaki ta wuce Daki
    
     Haleema tace" wallahi sai na gyarawa Yar aikin nan hankali harni Zata Mara! Mubin yace" duk laifinkine, yarinyar nan fa bata shiga harkanki kece kikeso Ki matsa Mata! Uhmmm tace" saina fadawa mummy, Rik'e Hannunta yayi yace please inhar kina So na karki Bari Su Hajiya suji, nandai yai Mata wayau yace" AI ba class dinki bane ma ace kinyi fada da Nazeefa!

Hakane tace" sannan ya riko hannunta sukai falo, drinks ya kawo Mata da snacks taci sannan sukai hira daga bisani tace tanajin Bacci ta shige dakinshi ta kwanta

    Dayaga tayi bacci ya fito falo ahankali kamar barawo, Room din Nazeefa ya shiga ya sameta A tsaye tana ninke kayan wankinta da tayi Rungumota yayi ta baya, afirgice tace Mai meye haka Mubin, banason irin wannan iskancin Gaskiya, ka fitar mun a Daki, yace" maganar da Kika fada dazu da gaske kina sona

Shuru tayi, Yace sai kince kinasona Sannan Zan fita a dakin nan! Rufe ido tayi tace" yes I love you....besan sanda ya rungumeta ba yace" Nazeefa na gode, Rungumeta dayai taji wani iri a jikinta

Rufe ido tayi, tace" mubin  please ka fita banason ganinka anan room din

Dariya yayi yace" i can't believe kina sone Nazeefa, Ashe zanga wannan ranar! I love you I want to spend d rest of my life with you sannan ya fita yana wani smiling

Ita kuma bawai sonshi takeyiba kawai dan ta batawa Haleema rai ta fada haka, aranta tace na shiga uku *SILAR GIDAN AIKI* na so ya janyomun wani Abu

Falo ya wuce ya zauna a kujera, ya zaro wayarshi ya Kira friend dinshi
Dr Bashir...yake sanar dashi finally Nazeefa tayi accepting tana sonshi, Tarkon shi ya kamata,  Wow Dr Bashir  yace'' I'm happy for you sai ka Iya allonka, kasan takunka!

     Yai kasa kasa da murya yace" yanzu Zan koya Mata wayau AI, wulakancin da tai mun a baya yanzu zata gane kuranta, Dr Bashir yai dariya yace kaifa kwararren Dan yaudarane abokina, ni dama dakace kanasonta nasan abunda kake mawa, that thing ko? Kwashewa da dariya sukai, Sannan yai cutting din call din

***
   Su Hajiya sunje sundawo boka yayi aiki sosai akan Mubin, ya dasamai son Haleema a zuciyarshi, ba fashi ita zai aura, hankalin Hadiza a kwance, sannan suka dawo gida

mubin ne zaune saiga Su Hajiya sun dawo, Hajiya Hadiza ta kalleshi tai wani murnushi tace" Son inlaw, Gaisheta yayi yace" kundawo? Tace" eh Hajiyarshi kuwa se tambaya suke ina Haleema yace tana bacci, sukace OK

Hajiya kuwa tausayin danta ya kamata wani irin son abun duniyane Ya rufe masu ido da har zasukai dansu wajen.malami but idan ta tina zasu karya asirin cikin sirri sai hankalinta ya kwanta

   Misalin 12pm Haleema ta tashi a bacci, da sauri ta fito falo taga hajiyarta tazo ta zauna kusa da ita 1 hour kawai suka Kara a gidan tace" zasu wuce Abuja bazasu Kara kwana ba, Da zasu tafi Alhaji ya basu 1Million kyauta sannan yai Mata godiya itama tace tagode

Dazasu tafi Haleema sai wani iyayi takema ma mubin alamu yai mata da ido yace" bamu kadai bane fa, sannan ta hankalta

   Nazeefa kuwa na kallonsu ta window tace" akin banza, Mubeen nawane banakiba,

Bayan Kwana biyu, Nazeefa ne Zaune tana nazarin Wani Abu, Mubeen yazo ya sameta yace" kizo ki rakani hospital Zan dakko wani Abu please, Kallonshi tayi tace" I can't salon Hajiya ta ganni kasan Bataso taga muna magana KO?Smiling yayi yace" karki damu ki fita Zan sameki a hanya

Haka KO akai, karya taje ta hadawa Hajiya ta amince, ta fito wajen
   Bata dadeba saiga Mubeen ya fito a mota ya sama waje yai parking sannan ta Shugo

   Slow driving yakeyi Wanda kana gani kasan Masoyane a cikin Car din,

Kallonshi tayi tace muyi sauri mana kar Hajiya tace na dade, Parking yayi yace dama magana nakeso muyi Kinga tunda kina sona Soyayyan Mu dole ya zama secret karki  yarda KO masu gadin gidan Su sani
.      shuru tayi na tsawon lokaci daganan ta Fara tinani

      Wajen idonta yazo ya hura ta dawo daga tinanin da takeyi yace why kikai shuru? KO akwai wani abune? Tace ah ah Karka damu xanyi yanda kakeso

    yace good My NAZEE.....wannan kenan

FOLLOW
VOTE
AND SHARE

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now