SILAR GIDAN AIKI

2.1K 121 6
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Follow me on Wattpad @Freshummieyxeey*

_Don’t feel bad if people remember you only when they need you. Feel privileged that you are like candle that comes to their mind when there is darkness._

*PAGE 1⃣3⃣*

Mubin ne Zaune a office dinshi yayi tagumi yana mamakin rashin Kama kan wasu matan, aranshi  yana Allah na tuba ai ko aure zanyi ban so na aura wacce ta kawo kanta gareni balle kuma yaran nan dako gama zama yanmata basui ba, Tsaki yayi ya dakko file din wata patient ya Fara rubuce rubuce

Babban Abokinshine ya shugo da yake shima doctor ne but from different hospital, Sallama yamai ya amsa yamai nuni daya zauna

Doctor Bashir ya kare ma Mubin kallo yace why are you looking so Dull? Kaga yanda ka rame kuwa? Kodai Kai rashin lafiyane?

Girgizamai Kai yayi alamun aa, Bashir ya Kara kallonshi yace" then what's wrong with you? M your frnd tell me koma menene koza Mu sama mafita..

Mubin ne ya tattara natsuwarshi guri daya ya Fara bashi labarin halin da ake ciki, Anaso a hadashi da wata shi kuma Yar aikin gidansu yakeso!

Bashir ya kalleshi cik'e da mamaki yace YAR AIKI fa kace kasan me kke fada

D'aga Mai kai yayi yace" ofcouse I love her kuma ita nakeson ko yaushe nadinga jina kusa da ita I mean na dinga hada shimfida da ita

Bashir murmushi yayi yace" Wow boy kace aure kake so haka! But me su mama sukace? Yace they did not agree saiyasa nadan shiga damuwa ai
       Doctor Bashir ajiyar zuciya yayi yace gaskiya akwai chakwakiya, amma ita Yar aikin tana sonkane? Girgiza Kai yayi alamun aa, Bashir yace" to wannan ai aikin banzane farko kafin kayi komai ka Fara Neman soyayyarta cikin ruwan sanyi sannan sekasan abunyi

Mubin yace Allah hakane abokina? Bashir yace" yes I'm serious ka jaraba ka gani Yace" tom shikkenan

Nan Sukasha hirarsu ta abokai Dan dama sun dade basu haduba,

*********
      Wani mota ne Chan na hango karshen titi anyi parking dinshi, taya daya ancireshi ansa wani karfe yadan rik'e wajen, Wani mutumine na hango a cikinshi da alamun ya gaji yana jiran wasu mutane ne, shingid'a yayi yana latsa wayar hannunshi, ga zafi ya addabeshi Dan haka yadan cire rigan jikinshi dagashi sai vest, vest dinma yadan dagashi sama kana hango gaggasar daya zagaye cibiyarshi, iska yaji ya Fara ratsa jikinshi Bacci ya kwasheshi

Bangaren Nazeefa kuwa Tasha Riga da wando ta dakko dogon hijab dinta ta saka zataje kasuwa danyn cefane, fita tayi tana trekking a kafa Dan bata samu abun hawaba tafiya takeyi harta tsallaka titi Mota tagani batai zaton akwai kowa bama, direct wajen motar ta tafi Dan ita a rayuwarta tana son kallon cikin mota, duk inda taga mota seta lekashi koda akwai mutane ne

Dan haka na nufa motar, ganin windows din motar a bude tasa Kai ta Fara leke, hango wani mutun tayi KO cartoon ne ko ba mutun bane Oho Dan kyan mutumin abun kallone, bacci yakeyi but zakace yana smiling, kallon daidai bakin tayi itama ta fara murmushi tace wannan abun da kyan kallo yake, bin jikinshi tayi da kallo dan wannan ne Karo na farko datasan yanayin jikin maza, Sedata gama kallon jikinshi sosai sannan ya farka daga baccin da yake Dan yaji a jikinshi Ana kallonshi, hada ido sosai sukayi na kusan 5mins sannan yasa hannu ya ja Yar vest dinshi, yace malama Dan Allah kiyi hakuri ki wuce anan, bansan me yakawoni nan ba karki cutar dani

Nazeefa kuwa najin haka tasa kafa ta zuga da gudu tana Aljanine Wallahi

Inba Aljaniba wazaizo karshen titi yazauna shi kadai,

Mutumun kuwa da sauri ya fito daga motar kafin ya fito hartasha kwana, dakko rigarsa yayi ya zira a zuciyarshi yace" da rabon zanga wannan aljanar ce

Dakko wayar yayi ya Kira abokinshi yace yazo akwai Matsala Dan yanzu yaga wata aljana da hijab, Dan be taba ganin me kyan taba

Hankalin abokin nashine ya tashi sosai yacemai gashinan Zuwa

*********
    Nazeefa da gudu da shiga cikin kasuwa, dasauri ta siya abunda zata siya duk saurayin data kalla fuskarshi saitaga ya Koma mata na aljanin da tagani acikin moto

Ahaka dai ta gama siyayyan duk a tsorace, da zata dawo gida machine tasamu direct har gida

Koda ta dawo gida a tsorace ranar tai aikin girki, Mubin kuwa na Lura da ita aranshi yace yarinyar nan akwai abunda ke damunta

   Bangaren Mutumin kuwa bayan tafiyar Nazeefa ba abunda yakeyi inba gumiba, lalle yau ya hadu da aljanah shi abun bacin ranma datagama kallon mai wajen al'aurarsa, Tsaki yayi amma daya tino irin 4eyes da sukai da ita saiya kara tsokata🤣





Lemme stop from here

Don't forget to share
And also comment and vote me thanks

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now