SILAR GIDAN AIKI

3.9K 194 4
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

~NOTE~ Na chanza sunan book din zuwa *SILAR GIDAN AIKI* saboda akwai me yin SANADIN GIDAN AIKI....love you All

*DEDICATED TO MOMIN NASRIN...* _Wish you a very happy birthday May life lead you 2 great happiness success and hope dat all your wishes comes true! enjoy your day...Allah ya Kara dankwan Love.....🎂🎂🎂🎂🎂_

FREE PAGE 0⃣3⃣

Washe gari tun asuba Nazeefa ta tashi ta daura ruwan zafi, Tana cikin kitchen ne sai ga Hajiya ta shugo ta dubeta tace" Har kinji saukin ne?

Kallonta tai idonta a kumbure alamar taci kuka tace" Eh Hajiya naji Sauki, Hajiyar ta ce" to Allah Kara sauki nan dai ta Dan kakkama mata Sukai gama break fast ta shirya zata tafi L.E.A primary school da aka sata

Tafito da sauri a harabar gidan taci Karo da mubin Robar abincin data boye tun jiya da aka dafa taliya da miyar manja da yasha kifi Ya subuto a hannunta ya fadi Sai kan kayar Mubin

Faeeza da faee kannanshi suna zaune a cikin motor suka hango dramar da akeyi, Faeeza tace tab yau yarinyar nan ta shiga uku kuwa, Faeez ya harareta yace to sai me? Kawai mutun be mistake a rayuwa? Faeeza tace to kaimun shuru malan

Mubin Yana ganin kayanshi ya baci Ya saukar mata da wasu zafafan Mari a fuskanta, Yaja hijab dinta yace" ke bakida hankaki KO? See what you did to me this morning,

Kuka kawai Nazeefa ta fara dan marin ya shigeta sosai, Batasan Sanda tace Sorry ba, Ya daka Mata tsawa yace Sorry for your self! Ya shiga daki

Jin hayaniya yayi yawane Hajiya ta fito Dan ganin meke faruwa, a bakin kofar shiga daki taci karo da mubin, Ganin kayanshi a 6ace yasa tasan me ya faru

Mubin ko saboda bacin rai yace" Mum kingani ko Wallahi sai na balla yarinyar ne, be jira yaji me zatace ba yai shigewarsa dakinshi ya chanza kaya, Nazeefa kuma tana tsaye a wajen ta rufe fuskarta da Hijab tana kuka, Hajiya ta karaso wajenta tace sai ki shiga motar ya rage miki hanya Dan nasan kunyi latti dukanku,

Kamar zataje bazata shiga, Sai kuma tai shuru ta tunKaro motor, sit din baya ta bude taga Gefe books din shine dayan site din kuma kannanshine twins *Faeeza da faeez* Dan haka ta bude sit din gaba tai zamanta,

Faeez face sorry Nazeefa, ta juyo da jajayen idonta ta kalleshi tace" bakomai Dan Allah ka tayani bashi hakuri,

"Faeez yace karki damu"

Mum na tsaye ya fito fuskarshi a murtake yace Hajiyata sai mun dawo, Tace to Allah ya tsare ya kikaye hanya yace Ameen,

Key yasa ya bude motor

Ya zauna kenan ya duba right hand dinshi yaga nazifa a zaune, Yasan aikin Hajiyarsune Gyada Kai yayi yace OK, bece komai ba me Gadi yazo ya bude masu get ya fita ya saita hanya

Faeez ne yace" yaya please kayi sauri munyi latti Wallahi, Harararshi yayi ta cikin Madubi, Sai ya gama bakinshi yai shuru,

Seda yazo bakin titi yai parking Ya kalle Nazeefa yace" to malama Sauka,

Tai karfin hali tace" AI makaranta akace ka kaini, Wani Shu'umin dariya Yayi yace" makaranta ko?

Ta daga Kai tace Eh

Yaga alamar da gaske ba sauka zatai ba yace" Dan ubanki ki fitan mun a mota, jin ya zage ubantane tai zuciya tace motor banza, Ta fita ta buga kofar da Karfi!!

Gaba dayansu binta da ido sukai

Mubin ko a ranshi yace" A sauka lafiya

Yan biyu kuma basuji dadin abunda yai mataba gaskiya, Nan ya seta motarshi ya fara gudu Dan both of them sunyi latti Dan shi ma kanshi yanada lectures 7:30 gashi yanzu 7:50 yaushe yaje ya sauke kannanshi balle har ya wuce dan haka ya Kara gudu da karfi

*********

Nazeefa kuma tunda aka ajiyeta ta share hawayenta KO banza yau ta gomama Mai, tafiya take a kasa abun tausayi gashi slippers ne a kafarta gashi garin anyi ruwa kafar tai datti sosai, Ta kalle kanta Tace" Ya Allah ka rabamu da wahala Ameen










Follow me on wattpad @Freshummieyxeey

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now