*MRS AMIDUD....?!*
_KURUCIYAR JAN PARIH_
Dedicated to my Aunty Nice😊
Page_1
Mu yan Bauchi ne, amma karamar hukumar misau, a misau d'in ma can wani ƙauye da ake kira da dabji, Iyayena da Kakanni na duk Fulanin can ne, sai dai Ni mareniya ce, amma me gata da galihu. Iyayena sun rasa rayukansu ne a wata tafiya da suka yi daga bauchi zuwa misau.
Inda suka yi hatsarin yar kurkuro wanda iya ke kira da yar kurkuro, a taki suka mutu Ni kad'ai ce na rayu. Kasancewar Mahaifiyata itace auta sai soyayyarta ya dawo kaina, inda Kakata ta roka aka bata Ni, amma da sharad'in da zaran na cika shekara biyu zasu zo daukata. Rimi rimi ta amince, abin dariya sai da nacika shekara biyu ta tubure tace."Wallahi bani kuma sake na rasa Jan PARIH, kamar yadda na rasa mahaifiyar ta, kuje amma ba zan baku ita ku sanyata a yar kurkura ba dan banza ana, shi kad'ai yana tafiya sai motsi yake."
Duk yadda Yaranta da suke bini suka so daukata taki firr, ita tana tsoron kar su sanya ni a yar kurkuro. Tun tasowata *Kaka Iya* take bani labarin hatsarin dake tare da yar kurkuro.
Yau ma kamar shekaru shida baya, dan duk shekara sai anzo gaban hakimin Dabji, naci kwalliya. Dan na ɗauki aniyar yau zan bar garin dabji ko Iya tana so ko bata so, nima zanje binni na kece reni, Aairah ta daina min feleke ita tana da dangi a can,😏🙄
A yanzun shekarata goma sha daya cif a duniya, naci ace ina makarantar Finramari amma Iya ta hanani wai kar yarda dan makaranta nasara sune suka kirkiri yar kurkuro, ta kashe min iyayena. Zaka sha mamaki dan garin mu yar kurkuro bata shigowa, sai dai a fidda kai da keken shanuwa. Sai ko keke da kuma keke me numfashi, yo naji shima suna kiran shi da wai babur, ranar da aka kawo mana shi, duk yan garinmu sai da muka b'oya.
Ina dalilin ina dan mafari, ai kuwa lokacin muna can dandali aka shigo mana dashi, kowa sai da yayi mamakin babbar keke, haka lallai nasara sai dai abar shi inda yake, kuma ba kowa bane yayi wannan tsiyar sai Ilu dan gidan liman dake yana wai daukar mutane zuwa wasu unguwar suna biyan shi.
Shine mara mutumci ya kawo mana, Babur me rai, wato da ya buga wata abu na jikinta, ai sai muka ji tace.
"Nanananana! Bammmmmm!" Kafin tace.
"Burburburbur!"Ai da muka dafe keya take aka shiga gudun fanfalalaki, domin bamu tab'a ganin wannan iftila'in ba, keke me numfashi,, kan kace me tuni dandali ya watsa, sai yan tsirara wanda suka san da abin sai dariya suke, Allah ya kiyashe mu da rayuwar duhun kai..
..... Yau ma mun same liman da wakilin hakimi kasancewar shi ba mazaunin Dabji bane. Rike kunnena tayi na kuwa saka mata kara, tace.
"Yar bante uba! Ko sun ce zasu tafi dake karki bisu, dan yan binni kashe mutane kauye suke, sannan kina ji kina gani za ayi cinikinki na dai gaya miki mu zauna abinmu ko."
Gyad'a mata kai nayi, ina kallon Wan mahaifina, Alhaji Muhmood Dabji. Bud'e min hannu yayi naje na shiga cikin babban rigarshi, na zauna.Bayan an bud'e taro da addu'a, Liman ya kalle Kaka Iya, yace.
"Iya shekara sha daya ya cika, ina baki manta ba, kece kika ce a bar Jan PARIH ta cika shekara sha d'aya lokacin tana da shekara biyar. Toh ga Muhmood yazo karb'an yar shi."Kallona tayi taga yadda nake lafe a jikinshi, tabbas tana daukar alhakin Muhmood, dan ita shaida ce wannan karon ne bai zo da iyalin shi ba, amma duk zuwa tare yake zuwa da Iyalinsa, kuma suyiwa PARIH sayayyar ban girma.
Karkace kai tayi irin ita bari ta gwada ko xan zab'i binsu. Cikin nuna ta tuna da haka tace.
"Yo Allah ya gafarta me rawani Baga Jan din ba, sai kin tambayeta ko tana bukatar zama dasu."Gyara zama wakilin hakimi yayi tare da mai da kallon shi kaina yace.
"Jal Parih zaki bi Baffanki ko zaki zauna da Iyarki"Kallon Kaka Iya nayi cikin tausayawa nace.
"Iyata kiyi hakuri nabiso ko da kwana d'aya ne sai na dawo nima ina son naje naga binnin nan, kamar.""Ke rufe min baƙi, sakarya toh wallahi santsin da ya kwashe ki ya kai ki can zaki gayawa, ince a binnin kika rasa iyayenki shikenan jeki binnin."
Mik'ewa tayi tana kad'e gyalenta muryanta na rawa tace.
"Muhmood Ni dai ga mareniya don Allah karka bari a cutar da ita, sannan kasa ido kanta kuje kawai karku zo gidana.".
Karku sha mamaki a gidan iya mu yaran kananun mun kai goma sha, soyayyar da take min na dabane, bata tab'a min fad'a ba, sai dai zata tsorarta dani abun me cutarwa ne.Tashi nayi na bi bayanta ina kuka, cikin raunin zuciya ta juyo tare da riko hannuna ta kai Ni gurin Baffana tace.
"Ku tafi idan na cigaba da ganinta zan iya karya alkawarin da na dauka"Shi kanshi Baffa dan alkawarin da ya daukawa Iyayena akan zai rike ni yasashi matsawa a bashi ni.
Gashi yana yawan mafarkin iyayena, suna matsa mishi yaje ya dauko Ni, ina cikin duhu.
Haka ya mike tare da musu alkhairi, sannan yasa aka kaiwa Kaka Iya abubuwan da yake kawo min. Dakyar ta amsa tana kukan zuci.
Gefe guda kuwa murna nake raina kal. Zabi binnin da ake min gori akai.Haka nabi dangi na musu bankwana, Iya kam shigewa tayi taki min magana da kuka na bar gidan, tunda na hau keken shanu nake raba idanuna, sai da muka yi tafiyar awa biyu sannan muka fito wata duniya, tun daga nesa nake hango shiftawa wasu ana a guje, jinjina kaina nayi cikin mamaki na kalli Baffana nace.
"Baffa! Naga wasu ana suna shiftawa a guje menene su."Kallona yayi cikin murmushi yace.
"Ai motocci ne!?"
Shiru nayi ina nazarin su, can a tuna ai Iya ta tab'a gaya min dayan sunan Yar kurkuro mato. Wanda yayi ajalin iyayena,
"Kutt ba dai hine mato ba!?"
Kallona yayi sannan yace.
"Mota ake cewa"Hannuna duk biyu na daura a kaina na fasa ihu, ina cewa.
"Kwarankwatsa bazan bika ba, dan ina zuwa nima kahe Ni zai yi kaga abu a cure.""Ikon Allah! Jan Parih ki shiga babu abinda zai same ki idan munje gurin motar."
Zan bud'e baki nayi zan yi magana sai ga wata yar karamar Y'ar kurkura tazo ta wucce fiiiiiiii, kuka nasa tare da cewa.
"Aradun Allah bani higa kaga yadda wancan yar kurkuro ta shika a guje, sai kace zata kai sako bangon duniya"Me Nura drive zai yi ban da dariya, muna isa gurin yar kurkuro, na tsaya a bayan Baffa ina kallon inda Yan kurkuro suke tsula gudu, sai kaji sunce shuuuuu kiiiiiiii, kai wannan yar aba akwai shai'dana. Kallon Baffa nayi shima Ni yake kallo yana tunanin yadda zan shiga yar kurkuro.
Nuna mishi inda yar kurkuro suke rantawa a guje nayi sannan nace.
"Shi wancan gurin taburma da ruwa ce aka shimfida."Kallon gurin yayi sannan ya ce.
"Parih ai kwaltace."
Wato tsabar ban fahimci maganar shi ba, ban san lokacin da na d'anne shi. Nace.
"Wayyo Allah na Kwarankwatsa bani kwantawa wallahi na yafe zuwa binnin"Duk yadda yaso na sauka a jikinshi naki dan gani nayi kamar zai cillani can,
Wata doguwar yar kurkuro ce yazo wuccewa cikin mamaki nace.
"Baffa a yar kurkuro akwai macizai ne?"
🤣😂 Low laf Parih na tambayar makapolo wai maciji ne