MRS AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
https://my.w.tt/XGvckkY6N6
Dedicated to my Aunty Nice😊
*_Alhamdulillah! Baka fahimtar waye kai sai ranar da ka wayi gari ka fahimci kana sanya farin ciki a zukatan al'umma! Anan ne zaka fahimci irin baiwar da Ubangiji yayi maka! Iya haka ma zan iya cewa tsarki ya Tabbata ga Ubangiji! Tsira da Amincin Allah ya tabbatar ga Nabiyu rahamati! Alhamdulillah! Mrs AMIDUDDAWLAH ya tafi inda ya kamata!😍😘 Nagode 🤝 sosai_*
_Fatan Alkhairi ga masu ilimin duniya 🙄 Yes karku tambaye Ni Amma Mrs Umar Tasan komai 🤣😜 karki damu idan nayi kud.... Keda Kakana zan biya muku Honeymoon a Wuhan ko Milan! Chaii na fasa kike Newyork_
28.
Kuka na fasa a lokacin da naji saukar ruwa a kaina, na shiga buge ruwan da yake bin jikina ina cewa.
"Wallahi na fasa bin su! Ku mai dani gida kawai tunda cin zalina zasu yi."Haka na gama wankan sannan nafito.
Kayan da zan saka naga ya ajiye min, wurgi nayi da kayan ina tura bakina na dauko wani riga da wando qaurt na saka sai bodyhook, komawa gadon nayi dan gana an gyara shi, matsar kwalla nake ina jan majina. Tare da matsar kwallar.
Shigowa yayi yaga wandon jikina, irin Crazy din nan ne.
" Bana hanaki wannan banzar shigar ba? Tashi ki saka wancan da na ajiye miki."
Hawayen da nake riritawa ne suka tsinke a guje, na kuma ware muryana na fashe da kuka.
"Ni wallahi bazan."
"Kika ce?!"
Ya daka min tsawa!
Sunkuyar da kai nayi, ina shashekar.Kauda kai yayi sannan yace.
"Sauko ki saka kayan, sai kici abinci!"
Tashi nayi na dauki abincin na ajiye sannan na dauki doguwar rigar na zumbula, na koma kan abincin na fara ci.Zama yayi kusa dani ya tattara min gashin kai na yayi.
"You Are so Beauty! Bani son kina wannan shirmen kinji. Ki nutsu bani son kina turancin nan kinji."Gyad'a mishi kai nayi, jan hancina yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Kina kama da Uncle Abtisham, kawai kalar fatar Aunty Amatul Islam, ki nutsu Iyayen ki Basu da wannan shiririn ta da kike yi kinji ko"Tari na fara ya sauki gabana ya bani ruwa na sha.
D'ago kaina nayi idanuna cike da kwalla.
"Toh Ya AMIDUD! Wy yu heti mi? I cee yadda kake luv yor Sita andi buroda amma mi yu heti mi!"Matsowa yayi gabana, ja baya nayi. Ina raba idanuna, idanuna na shirin zubda kwalla,
Riko hannuna yayi cikin nashi yana murza zoben zinarin da Mamie ta bani.
"Honey! Meye haka? Amma kasan haka bai dace ba. Tunda kasan balagagiya ce, yadda kake murza hannunta. Idan shaidan ya shiga tsakaninku fa"
Yadda take maganar sai ka dauka tazo tasame Ni muna masha a.
Tashi yayi ya bar Ni, ta kuwa bini da mugun kallo.
Murguda mata baki nayi."Singul hamama kawai!"
Na gaya mata.Kwafa tayi tana harara ta. Ture abincin nayi tare da jingina da jikin gadon, abincin da ban karasa ci ba kenan. Na shiga gyangyadi.
........
Bayan awa daya da rabi, yazo ya tashe ni, mamaki yayi ganin baki kallon shi dan haushi ya bani tunda ya tafi bai dawo ba sai da muka kusan tafiya sannan yazo tashina.Kawai sai na saka mishi kuka, tare da cewa.
"Ni kam ka kaini!"Zuwa yayi gabana ya tsaya kamo hannuna yayi ya manna akan fuskarshi cikin wani irin damuwa.
"Me yasa ba zaki gane abinda nake nufi ba?! Me yasa ba zaki hakura ba! Muje can duk abinda aka miki in bai miki ba, ki kira Mamie ki gaya mata kinji."Janye hannuna nayi, ina goge fuskana da bayan Hannuna. Jan hancina nayi sannan na tura mishi baki.
"Ni dai ka gayawa matar ka babu ruwan ta dani.""Shi kenan! Fitinanniya."
Haka muka fito, raina a jagule dan Allah ya gani bani son barin ƙasata. Ina kewar ahalina tun ban bar kasar ba.---
Karfe ɗaya na dare muka isa Abu Dhabi, tunda muka isa ko hutawa bamu ba, suka sani a gaba muka fita. Sayayya yayi mana. A manyan Mall na cikin garin Musamman Bunjur Arab, sai wasu guraren bude ido. Dukda dare ne bai hana matar shi yin hotuna dashi.Komawa gefe nayi ina kallon su, zuwa yayi ya d'ago Ni nima yayi hoton da ni, ganin duk hotunar da yayi dani baki dariya. Sai ya saka wayar a kunne ya shiga magana.
"Mamie gamu a abu Dhabi. Toh gata!" Ya mika min wayar, cikin farin ciki na amsa nan na washe baki na shiga basu labarin inda nake, karshe ta hadani da Aarib da Amrozia da Buhayyah.
Cewa suka yi na kashe kiran muyi video call. Kallon shi nayi yana hira da matar shi, amma idanun shi na kaina.
Mika mishi wayar nayi, cikin jin nauyin zan rike shi a karon farko a rayuwata.
"Ko zaka bude mana data ne zamu yi bidiyo cal"Karban wayar yayi ya kunna min datar sannan ya mika min, zama nayi na juya musu baya.
Nan muka shiga hira da ihu, kamar muna tare.Nan na fara kafta musu tsiyar wato mugayen turancina mana.(😲🤣🙄😜🤸)
"An teli yu! Dey kontiri e fit mi! I bi lek meka no lib di kontiri!""Wowwww kice garin ya haɗu!" Inji Buhayyah.
"Hmm! Mey total sifice I dan ko min endi, bikos ebir yuya iz fine min,"Dariya muka saka sannan Aarib yace.
"Bani cikin da mugun turancin kin nan wannan koda Bature aka yiwa na rantse zai iya mutuwa bai sani ba! Don Allah ki daina karki yi a rashin sani karannunkan su. Su hau cizon jama'a a rashin sani!"Cikin jin haushi na juya ina kallon shi kamar zan yi kuka nace.
" Kaga Aarib ko?"
Banza yayi dani kamar baya gurin, aikuwa na saka mishi kuka. Zuba min ido yayi ganin yadda nake kukan.Mika min hannu yayi na mika mishi wayar ya kashe satar sannan ya saka wayar aljuhun sa.
Suka ci-gaba da hiran su, kallona matar shi tayi. Tare da min gwalo ya ganta amma yayi fuska kamar bashi ba.
Zama nayi na cigaba da shasheka na, ya rasa yadda zai dani.
Tashi yayi cikin fushi yayi kaina ai kuwa na kare fuskana da hannuna, jikina na rawa.
"Honey! Muje karka wahalar da kanka akan wannan mara hankalin."
Tsaki yayi ya bar gurin ni kuwa ban san sun tafi ba. Dan na zata har lokacin yana tsaye zai mare Ni ne.
Haka suka tafi masauki suka bar Ni sai da na cire hannuna. Babu su babu alamar su.
Da sauri na fita! Naga kowa sai sabgar gaban shi yake da karfi na kira sunan shi.
"Ya AMIDUD!!!" Cikin wani irin kuka. Tare da kaiwa iska duka.Na duba gabas da yamma, kudu da arewa basu su ban san lokacin da wani irin kuka ya kwace min ba na kuma buga kafaffuna a kasa tare da kiran sunan shi.
Babu su babu dalilin su.
Shi a nashi tunanin matar shi zata tawo dani, ita kuma a nata muguntar ta barni na b'ata. Ita ko a jikinta tunda na hana ta rawan gaban hantsi.Sai da suka isa masaukin su ya juya yaga bana tare dasu dan ranshi ya b'aci sabida abinda nayi mishi. Na kukan banza.
"Ina Jal take?!"
Tsaki yayi sannan tace.
"Oho taki biyo m."Bai gama jin abinda ta faɗa ba ya fita da gudu.
Toh Allah yasa a dace.....🤸
Yau kam kar a cinye nama na danye
Oum Muwaddah🤫