15

2.4K 395 40
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to my Aunty Nice.

Page_15

   Wato Jalal da Hansatu kamar su cinye kansu dan masifa, dan sosai suka gurji amarci kam dan sai da aka hana mu zuwa shashinsu tunda naje naga suna wasan kwarzo abin ya dame Ni nazo na gayawa Mamie ta make min baƙi na, sai ban kuma Magana ba.

           Muna samun hutun na d'aga musu hankali sai sun kai Ni gurin Iyata, aikuwa aka fara shirya min kayana, tare da tsaraba kai har da abin kwadayin da ake samun na zuwa makaranta.

   Ranar Laraba Jalal da su Buhayyah suka raka Ni har cikin Dabji, yan garin mu suna gani na aka fara murna "ga Jan Parih ta dawo,"

   Murmushi nake dokawa kawai dan nasan nayi kewar Dabji. Muna isa kofar gida dan a keken shanu aka shigo damu, sai ga Iyata ta fito da gudu na dira, sai da Jalal ya riko ni. Tuni na isa gurin ta, na fad'a jikin ta tare da fashewa da kuka.
"Iyata Alqur'ani na damu dake"

   Goge kwalla tayi sannan tace.
"Parih na! Kullum dake nake kwana nake tashi sannu Y'ar nan"

       D'ago kai  tayi sannan tace.
"Ku shigo ciki barkan ku da zuwa."

              Saukar min da kayana suka yi sannan suka shigo cikin gidan.

       Taburman kaba aka shimfida musu, shiga daki tayi ta dauko musu ruwa, ta ajiye musu a sabon kwashinta sannan ta kuma kawo musu kindirmo, ta ajiye musu.

            Ta kuma tura aka sayo sugar, aka zuba kafin wani lokaci, su jummalo sun cika gidan mu har dasu Aairah.

   Bayan su huta Jalal ya dube Ni kamar zai min kuka yace.
"Baby Parih! Sai nazo daukar ki kinji"

    Dariya nayi sannan nace.
"Toh ai wancan katuwar Matarka itace ke kiran ka baby, Ni kuwa ai ba baby bace."

        Dakyar Jalal ya bar garin dabji dan ya wani narke min sai salo da fi'ili yake min.

      Bayan na kwanta a jikin Iya ina kallon fuskarta nace.
"Mey Iya i mis yu"
  Kallona tayi sannan tace.
"Me kika ce!"
  Dariya nayi sannan nace.
"Ina kewarki!"
" Da wani Yaren?!"
      Dariya na kuma sakawa nace.
"Da Yaren nasara"
  
A firgice ta ture Ni daga jikinta tace.
"Na shiga uku! Wato sai da Muhmood ya kai ki gurin shaidanun nan ko"

      Dariya nake kamar me yadda ta firgice sai kace na koyo wani masha'a, tashi nayi na bud'e inda aka zuba min kayan tsaraba ta, sannan na fita.

    Fita nayi da gudu ina cin chocolat din da na buɗe bakin shi.
     Can dandali na nufa, inda na sami su jummalo ana labarin irin kyan da nayi wai kamar bani ba.

   Ina zuwa suka zagaye Ni suna kallona kafin suka shiga jefa min tambayoyi.

    Nan na shiga basu labarin Birni nace jummalo.
"Ef i taili yu, de hawus d'in da muke, ibi laki tangaran, gahi da fanfu, jummalo  yo mu ba taliya muke kiran, sufa acan bini sofageti  suke ce mihi: "

     "Don Allah Parih toh ya sifagetin yake?!"

   "Hai-hai-hai! Sofagetin ake cewa  ba sofageti ba"

    "Ai toh amma! Da baki nan Aairah taci amanarki ta kula Iroro."

     Zaro ido nayi sannan sannan nace.
"Jummalo. I suwai ef i kachi Aaira, i go fass a hedi"

       Zuba min ido tayi kamar ta fahimci abinda nake nufi sannan tace.
"Me haka yake nufi?!"

  Dariya na saka cikin jin dad'i nace.
"Nusent a dey tali yu, duk cikin bini nu bodi fass min ingilse"

Kina wuta Jin yadda suka rud'e da ihu nayi murmushin jin dadi abinka da kauyawa.

     Ashe daga nan dandali anje an gayawa Iyata ai gani can Aljanun nasara sun shige Ni sai wani yare nake,

  Sai gata da kanta tazo komawa sani gida ina ganinta nace.
""Iya wata de firobilan!?"
Kuka ta kuma sakawa tace.
"Yanzun abinda Muhmood zai min kenan ya kaiki  aljanun nasara sun shigeki  Cikin gafara da nunawa miki bani kaunar tafiyarki amma kika kafe yar nima me kama da aljanun gaskiya."

            Cike da jin haushin yadda take fada tana kiran sunan Baffana ya sani tura baki na nace.
"Kaka Iya, waiti konse yu, she bi a de sifiki ingilise."
Kuka tasaka sosai.

"Wayyo Allah  na shiga uku, Ke Pari wannan mugun alkaba'in da kike fa, duk a zuwa binin kika koyo" tace min,.

       
Tura baki nayi cikin kuka nace.
"Kaka Iya iz but lai daya, babu aljanus a kaina, na oli Ingilishi"
"Wayyo Allah  na shiga uku meye kuma ledas Parih aljanun ashe ba d'aya bane har dasu ledas"

   "Iyah nifa bani da aljanun da kike fada."

    Gyad'a kai tayi cikin jimami tace.
"Hakkun! Baki da su ina ma zaki samu! Tunda sun miki mugun kamu aike sai gidan yar me ganye itace tafi dacewa da laluran ki"

        Kuka na saka mata nace mata lafiyata lau amma taki sai da suka je gurin yar me ganye suka yi ta zane min kafaffuna.
"Kai dan tsugudi! Dan kaburburan! Lagwas maza ku ficce a jikinta."

   Murmushin mugunta nayi sannan nace.
"Weririri! Yasin bamu fita ai mun kai mu dari akanta, kuma sai mun karo wasu darin ke yar me ganye zaki daina borin karya ko sai na bankad'e miki ahirinki a garin! Sannan duk wanda yace Parih ta zauna a garin ga Alqur'ani sai mun haiyen mihi kafa da hannu mu kuma mai da mihi bakin hi keyar yi, sannan mu dauke ta zuwa sama jannati wato birnin almatsotsai! Inda fadar burburasa yake mulki, Keeee Iya kaka ki godewa Allah kin manyanta da yau sai mun saki murmuhi da hakori d'aya, kuma ef i silafi yu, yu go rimanba mi"

            Yau jumma'a kuyi hakuri da wannan. Kuyi Vote sannan kuyi dariya kada'n.

Oum Muwaddah

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now