MR AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
Dedicated to Aunty Nice.
Page_7
Spain...
Madrid....
Shine babbar birnin Spain, zaune suke a gefen Coach dinsu sai tsara musu yadda wasan zai kasance yake, duk wannan maganar da Ake bai sashi d'ago kanshi ya kalli me horonsu ba, asalima ya b'ata shiru ne, sabida tuno alkawarin da yayiwa Aunty Amarya nacewa idan ya dawo zai amshi auren Yar abokin Daddynsu ne yake damun shi. Matsalar shi d'aya ce yarinyar da ake so ya aura ta cika rawan kai shi a tsarin shi ya samu macen da zai sanya doka tabi, yana bukatar mace renon shi wacce sai yadda ya lankwasa ta. Ba wacce zai sha wahala da ita ba.A haka suka shiga filin wasan suka. Wannan shine wasan su na karshe, a wannan kakar wasan bana, kuma suna gamawa zai tarkato kayan shi zuwa Naija.
*****
Bauchi State Nigeria.Kallon tuwon shinkafa tayi tayi kyau fara da ita, sai ɗaukar ido take.
Ba tare da dogon nazari ba takura sokawa tuwon finger ta darasi rabin tuwon ta raba gida biyu sannan ta shiga yanka tuwon kananu sannan ta fara riga wata mahaukaciyar loma. Ta kuwa cika bakinta da tuwon miyar kukan na bin bayan hannunta ta kuma zabtar wani tuwon ta cika baƙinta sannan tace.
"Yoh ai miyar nan gwanin dad'i yaƙe! Dama lokacin da ake miyar naga Iya talatu ta d'and'ana miyar sai da yawunta ya kusan dig'a a cikin tukunyar dahuwar"Shiru falon yayi dan basu san me zasu ce ba, ta gama cika musu kunne da kuka yanzun kuma tazo tana musu surutun banza.
"Ai lokacin da kika fita daga madafin naga wancan yar gajeruwar ta cika abu a kwano takai kofar gida."
Kar ku manta baƙinta cike yake da tuwo, take wannan surutun.
"Ai sau biyar ina ganin lokacin da take d'and'ana miyar."
Lashe hannunta tayi har bayan hannun ta kuma lashe bakinta, tare zurma hannun duka a baƙinta ta lashe wannan ta kuma cewa.
"Alkur'an sau ba adadi ta dangwali miyar"
"Kinsan Allah kici tuwonki ko kuma nazo na taka bakin kin nan mara kunya da goshinta kamar na jinjirin jaki."Wani irin kallon ta auna mishi kafin ta cika baƙinta tace.
"Toh ula uban ifiritai! Da wani katon kai kamar tukunyar girka! Ko nace ka kulani ne mutum sai mugun fushi kamar wanda aka zage ubanai""Ke bani cikin rashin kunya! Sa'anki ne da zaki dube shi ki zage shi, maza bashi hakuri "
Inji Aunty Amarya, dan ta rama abinda Jalal yace mata.
D'ago kai tayi kamar zata fasa kuka tace.
"Toh baki ji abinda yace min bane"
"Kaniyar ki, da abinda yace miki"Tashi tayi ta shure filet din tabar falon, ta koma can gefe ta zauna, tana wani kwaɓa fuska kafin su an kara ta fashe da uba ihu wai nan tana kuka.
Hajiya Adawiyah da take cikin d'akinta, ta fito da sauri.
"Ke Parih lafiya kike zumduma ihu haka!"Sai da taka wani kugi kafin tace.
"Zagina suka yi wallahi sai kin mai dani gurin Iyata."Duk yadda Aunty Amarya taso kare kanta ita da Jalal Parih ta hanasu domin suna bude baki da niyyar magana zata fasa ihu me karfi dan dole Hajiya Adawiyah ta rarrashi ta, suka koma cikin d'akinta.
*****
Washi gari da safe, bata karya ba ta tashi ta sulale zuwa waje.
Kallon gidan tayi da kyau, hango yar gajeruwar Yarinyar nan tayi taga ta shige cikin ciyawa, wato flower da sauri itama bin bayan Yarinyar tayi har bakin wani kofa, taga yarinyar tashiga.Tura kanta tayi ta juyo muryan Jalal yana cewa.
"Yawwa nan zaki rike min" sai magana yake yana nishi.
Aikuwa ta burma musu kai, da sauri suka buga tsalle kowa ya kama maboyar shi.