19

2.2K 440 23
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to my Aunty Nice.

  _🤭🌹 Wadatacce zuciya itace wacce take jibanta al'amarin masu kyautata mata! Kyakyawar alaƙa itace me cike da so da amincewa! Yarda da girman kuskure ke kai mu tundun na tsira! Kusancin makomarmu itace maidu'in nisanta aiyukar Asha! Ya Allah Ya wadatamu da Rahaman shi 👏🏼_

Page_19
Ganin yadda nasaka su a gaba ina cin dan wake yasa shi, daure fuska tam sannan yace.
"Ki tashi kije ki saka kayan ko kuma ba zane ki babu abinda ya dame ni"
  
"Duka!!" Nace har sau biyu, mik'ewa yayi tare da zare belt din wandon shi, mik'ewa nayi da sauri na bar falon, ina buga kafaffuna a kasa, ina shiga daki nayi kwanciyata dan ko hannu ban wanke ba nace.
"Ji min d'an jaraba daga dawowa zai fara takura mutum"

  Ban san lokacin da barci yayi gaba dani ba, sai dai naji ana jan kafana, ga wani sanyi da nake ji yana shiga ta kafana, buɗe ido nayi nagan ni a wani lambu me kyau, sai kamshi gurin yake. Ga kayan ciye ciye, an zuba a wasu kwandon azurfa, sake jan kafana akayi na kalli inda ake jan kafar, ware idanuna nayi ina son nayi magana bakina yayi nauyi, kura musu ido nayi cikin farin ciki, zuwa suka yi kowane su ya zauna kusadani.
       Shafa kaina tayi tace.
"Jal Parih! Me yasa kike kuntattawa iyayen rikonki! Ta hanyar abinda bai dace ba! Ko baki son muma musami salama ne! Kin manta damu ko guzirin baki riko mana! Kinga Uwar rikonki na kuka saboda halin da kike ciki"
Ta nuna min Mamie na share kwalla, riko hannuna yayi sannan yace.
"Ki daina azabtar da zuciyar da ta ginu da kaunarki! Kinji muna muna miki fatan Alkhairi"

         Gani nayi suna matsawa a hankali, sai lokacin na samu damar bude bakina nace..
"Mamana! Abbana!"
A firgice na farka, naga Jalal yana ƙoƙarin saka hannunshi a cikin rigana,  kura mishi ido nayi sannan nayi maza na rike hannunsa, dan duk wasan banzan da muke bani barin shi ya tab'a min kirjina, har gwara Faseelah. Takan tab'a tace.
"Wai! Parih kinfi mu wallahi"

B'ata rai yayi sannan yace.
"Ki bari mana kullum nazo tab'awa sai ki hanani, kice akwai lokaci, toh ga shi Ya AMIDUD yazo kuma nasan zai sa miki ido dan yanzun Mama take gaya min! Kuma muna da partyn Abokina kisan yadda kika yi ki fito"

Kwace hannun shi yayi sannan ya fita, tare da sake murmushin mugunta, yace.
"Kamar yadda kika lalata min komai na nima sai na lalata miki baki gobe! Kinsan an had'ani da macen da bana so sai dai na more jikinta! Kika ja min mahaukaci ya min dukar mutuwa kice zan kaunace ki?! Sannan kika ja min na ji ciwo ta hanyar daura min macijin roba! Hmm Yau Insha Allah zan gama komai kuma ki bar gidan nan! Rashin kunyar da kikewa mahaifiyata ya kusan karewa! Kawayen da kike tare dasu ni na turosu rayuwarki"

   Ya ficce a gidan tare da sake murmushin farin ciki, wannan shine burin Jalal kenan ya tarwatsa rayuwar Parih, kamar yadda tasa aka aura mishi, Hansatu.

         Wasu jaka na gani a inda ya tashi, sannan na mike tare da gyara zaman rigana, na zazzage kayan naga kananun kayana, tsaki nayi na wurga gefe.

   "Nusent kawai! Ko Uwar me zai yi da tab'a min kirjina, mi Nu go fil tak nusent"
Ni daya na tayita masifa, kamar yana gurin, tashi nayi nayo wanka. Sannan nazo na kwanta akan idan lokacin tafiya yayi sai na fita.

   Karfe sha biyu saura na farka, naji gidan tsit, dan haka nasa kayana na fito, babu kowa. A hankali na murda kofar fita a gidan na fita daga falo, da sauri na fita na same shi yana jirana a bakin get,muna zuwa ya mikawa baba dubu biyu, sannan muka fita.

   Kallon shi nayi sannan muka shiga motar shi da take wajen, yace.
"Yau zaki bani damar na tab'a ko ina!"

      "Hmmm! Mamie zata min duka"

        "Ban ciki da iskanci! Sauka min a mota ko na baki mamaki"

       "Ai ba sai ka min wulakancin zan san ka dauko Ni ba, sauke Ni nima na koma gida"
      Zaro ido yayi waje cikin jin haushi yace..
"Karki min rashin kunya!"
Ni kuwa na murguda bakina nace na nawa kuma"

Make min bakina yayi, naji zafi sannan nace.
"Allah ya isa min!" Dan har yanzun bakina bai mutu ba, kuma bashi zai hana idan da Mamie zata titsiye Ni na faɗa mata gaskiya abinda muke dashi ba.

        "Ni kikawa Allah ya isa?!"
"Eh anyi maka sai me?!"
  "Yau zan ga karshen rashin kunyarki"
     "Ka jima baka ga karshen ba, mugu kawai"

        Haushi ne ya kama shi yayi gangara gefen hanya tare da fincikoni, Ni kuwa Allah ya bani Sa'a na kwad'a mishi mari,, abinda ya kuma fusata shi kenan Yasaka hannun shi ya yaga min rigar jikina, wanda ya bayyana bra din da nasaka, a tsorace na kai mishi cizo, kafin ya dawo daga zafin na balle kofar zan fita, ya janyo Ni na kuwa kwala kara tare da fincike jikina na aruntuma a guje.
. fitowa yayi cikin d'aga murya yace.
"Ki dawo na kai ki gida! Dan wallahi kika kuskura na kamaki zan miki wulakancin da baki tab'a tsammani ba"

   Jin haka ya kuma jefa Ni cikin tsoro, ban san inda nake jefa kafana ba, kawai dai abinda na sani ina gudun ceton raina, kuma insha Allah sai na tsira daga nufin Jalal.

       Gashi dama riga da skirt na saka a jikina iya cinyata, kuka na fashe da shi ina gudu ban masan ta inda zan fara ceton kaina ba, karfina ne ya kare gashi na gaji, kawai na tsaya kawai har ya kusan cimma Ni, sai ji nayi an fisgoni tare da toshe min baki, hawaye ne ya zubo min sakamakon ban san waye ya janyo ni ba, haɗuwar jikinmu ya bada wani irin spark wanda yasa muka d'ago kai kallon juna muka yi, ban san lokacin da na fashe da kuka ba ina ƙoƙarin kwace kaina......

            😎🙄 Gwanen sunce mune jahilai masu musu Hassada da bakin ciki! Sabida rigar daukaka da suka saka. Vote! Abin tausayi nayi typing k'wark'warah wallahi ya goge 😭

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now