MR AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
Dedicated to my Aunty Nice.
Page_11
Tashi tayi abinta ta bar falon, ta nufi kitchen, lek'awa tayi taga Baba talatu na saka kafi zabuwa. Rike baki tayi sannan ta juya sai da ta kusan fita daga gidan tace.
"Iya Talatu ki daina mana barbad'e a cikin abinci"Kuma da karfi ta fad'a sannan ta ficce a gidan.
Hanyar dakin Jalal ta nufa, yaji yana magana kasa kasa, lek'awa tayi ta hango hansatu bisar shi.
Komawa tayi ta zauna tana kallon kofar dakin shi, har AMIDUD yazo ya wucce bai ce mata Komai ba, itama bata ce dashi komai ba, sai ma kauda kanta da tayi, tana kallon can gefen gidan.
Har ya wuce sai yaji bai yarda da ita ba, dawowa yayi ya koma d'akin shi yaje ya zaro wayar rediyo, bata aune ba ya tsula mata a gadon bayanta, sai da ta fasa ihu tare da sosai gurin tana cewa.
"Wallahi na tuba! Bani kuma leken su da maka aman da nayi"Da gudu ta bar gurin tana ihu sai ka rantse dukar mutuwa.
Sai da kowa yafito a gidan, suna tambayar lafiya.
Jikin Mamie ta shige tare da sake wani Irin kuka, me cin rai tace.
"Mamie! Kice mihi bani kumawa, kar ya kuma dukana akwai zafi."Dariya Aarib yayi cikin mugunta yace.
"Madalla yau an kawo mana ƙarshen fitinar"..... Bayan shigowar ta ne ya tsaya kallon kofar d'akin Jalal, bugawa yayi, a firgice Jalal ya ture Hansatu. Ya leko ta taga.
"Waye?!"
"Fito Ni ne!"
Wandon shi ya dauka ya saka sannan ya janyo rigarshi ya zura, buɗe ban daki yayi yace.
"Kishiga ban daki ina zuwa."
Shiga tayi ya rufe sannan yazo ya buɗe kofar dakin, shigowa AMIDUD yayi yana duba ko ina na ciki d'akin..
Sannan ya duba kasa, ganin inner wear duk sai jikin Jalal ya dauki rawa.
Takaici ne ya kama AMIDUD ya gyara tsayuwar shi sannan yace.
"Gatan da ya nuna maka ne ya lalata ka ko?! Me kake bukata?! Idan auren kake so ka sami Daddy da maganar ko kayi ƙoƙarin haka bai kulaka bane"
Girgiza kai yayi tare da sunkuyar da kanshi kasa yace.
"Wallahi Yaya na sami Mama da maganar ta hanani ta kuma gargad'e da kar na kuskura na gayawa Mamie ko Daddy, Ni kuma bazan iya cigaba da tsare kaina bane, muka fara sama sama da hansatu kuma gashi yanzun munyi nisa"
Dafe goshi AMIDUD yayi sannan yace.
" Kacewa Ita Yarinyar ta fito taje tayi wanka, wanka kai ma kuma kayi kusame Ni da dare.""Toh" yace mishi a sanyayye.
****
Da dare sai da aka kai ruwa rana da Aunty Amarya kafin ta amince Da maganar Auren Jalal, dan tace bai isa aure ba..........
Washi gari tana tsaka da barci aka tasheta, dakyar ta bud'e idanu hanyar ban daki Buhayyah ta nuna mata ta wucce koda ta shiga tafi minti arba'in a ciki sai da yazo ya buga tayi wanka tafito,Doguwar riga tasaka sannan ta lab'a mai wai tashafa sannan ta fito falo, tana fitowa ta nuna mata gurin cin abinci taje taci kamar zatayi kuka, tana idarwa ya nuna mata hanya suka fita, tun da tashiga motar ta kifa kanta har suka isa sunshine nan ya kaita aka mata tambayoyi, bata sani ba, karshe shi ya basu amsar ya kuma roki alfarma a bata aji hudu na primary, sannan suka mishi lissfin komai ya fito tare da ita, dan ya fahimci har da gudummawar jahilci yake haukata.
Suna fitowa daga makaranta dake bai shiga da motar shi ba, ya yana gaba tana baya, kallon wani yaro yayi yasaka yara a gaba sai make su yake, a karanbana tana zuwa ta samu wani bulala ta fyada mishi a tsakiyar kai, sai ta ya fasa ihu, ta yar kamar ba ita ba, sai da take kusada me yalo ta tsaya tare da marairaice fuska tace.
"Ayya! Bawan Allah bani mana guda d'aya."Murmushi mutumin yayi ya dauki uku yasaka a leda ya mika mata, tana karb'a tace.
"Nagode,"
Ta zura da gudu dan har ya tadda motar ita yake jira, kallon ta yake da abinda take, shi ba me yawan magana ba, amma zuwan shi yarinyar nan tasa shi magana. Dole ya zaneta idan suka koma gida.
Sorry maneji....