12

2.4K 282 29
                                    

MR AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to my Aunty Nice.

     

Page_12
Da gudu ta isa jikin motar ta shige, tana buɗewa ta shige tare da jan murfin motar girifffff. Manyan kenan, juyawa tayi ta kalle shi tare da washe mishi haƙora Tace.
"Zaka ci?"

   Yadda ya tamke fuska ya sata shiga hankalinta, ta fara cin yalon kamar me cutar yunwa.

   Tana taunar yalon kamar tanayi a kunnen shi, tsaki yayi tare da buga mata tsawa.
" Zaki daina tauna nan ko sai na watsaki waje."
  Cak tayi shiru tare da gayyato wasu fake hawayenta ta shiga cewa.
"Don Allah! Karka wurgani waje yar kurkura ta take ni! Dan Iya kaka tace hine ya kahe min iyayena, kaga kai su Baffana da Mamie suna nan Ni kuma bani da."

  "Zaki min shiru ko sai na wurgaki"

         "Uuuuu! Da gaske kake Yaya dan gayu"
     A fusace ya juya tare da zare mata ido.
"Yo ai wannan zaro ido sai kace wanda aka tsikara maka allurai ba adadi"

   Make mata baki tayi, ta kuwa rike bakin kafin ta fashe da kuka, irin me cika kunne nan,  suna isa gidan ya taka birni kamar zasu hantsila.
   "Yo ka hwasa min baƙi ma balle dunguren yar a kurkura, kawai ka buɗe min yar a kurkura ko nayi maka sayi a ciki."

         "Idan baki da hankali kiyi mana"

    Tallahi zan yi"
   "Allah ya baki Sa'a sha-sha-sha"
    Kallon shi tayi kafin tace.
"Alqur'ani bani ce shen me ruwa uku ba"

  Zaro ido yayi wato ba ita bace.
Sha-sha-sha ba,
   Fita yayi ya je zargo bulala tana fahimtar yaje nima ai kuwa ta balle motar tafita da gudu, zuwa cikin gidan.

              Bata tsaya ko ina ba, sai gadon Mamie da takalminta ta haye. Jikinta na rawa dan bata manta bulalar da yayi mata ba.

           Dake ta wuce yan gidan a falo, basu samu da susan meke faru ba. Shigowar shi da bulala yasa suka fahimci shi ta tsokano.

     "Karka fara dukar min ita! Wallahi bani son mugunta! Haka kawai daga dawowar ka ka zaneta yanzun kana harin dukarta na biyu raina zai ɓaci matuka gaya."

"Mamie! Zagina tayi fa, nace mata sha-sha-sha tace min shen me ruwa uku!"

    Dariya duk suka saka a falon,
"Uban me kukewa dariya"

Tsit suka yi,.

   "Wallahi jeka zaneta Son! Karka raga mata."

   Mamie zata yi magana! Aunty Amarya ta hanata, dan dole ta shiru ya shige dakin ya shiga tsulla mata bulalar, duka biyu yayi mata amma sai ka rantse zaneta yake kamar me, a na ukun ta daka tsalle. Ta cacume mishi riga, fuskarta na kan cikin shi, sai wani irin kuka take sakewa, sake bulalar yayi tare da tureta ta fadi.

Fita yayi daga d'akin ran shi na kara ɓaci.

        Buhayyah da Allah ya daura mata  kaunar Parih yana fita tana shiga dakin, ta sameta shame-shame.

"Wayyo Allah Mamie kizo"
Gaban Mamie ne ya fad'i, dole ta mike taje, tana shiga ta sami Parih sai nishi take zaka rantse wani mugun duka aka mata.

    Da sauri Mamie ta isa gareta,
"Wayyo Allah na! Ni kam ku kai Ni gurin Iyata, Alqur'ani da ya zuba min bulalar shi cewa nayi an sake Ni da igiyar rama ce."

     Kware cinyar ta tayi wanda suka yi jajjur sabida farin fatar ta.
         Rarrashin ta Mamie tayi sannan ta fita, ta same shi ya shigo daukar kofi, aikuwa ta shiga fad'a sosai.

        Shiru tayi tana gamawa yace.
"Kuyi hakuri!"
      Wannan dabi'ar shi ce da zaran tayi fada ya bata hakuri (🙄🤔 Ban da yaran mu na yanzun kina musu fad'a suna kallon cikin idanun ki Allah ka shirya mana zuri'anmu tafarkin addinin Muslunci)

          Jikinta ne yayi sanyi dan itama yasan halin shi bazasu  kuma kara cewa kome ba.

      ........
    Rikicin da Parih tasaka musu ba iyaka, dan rigima take Sosai ita sai dai A maida ita Dabji, kuma abin dariya tana ganin AMIDUD zata had'iye kukan ta, domin kuwa tana tsoron kar ya kuma zaneta.

   Satin sa biyu aka kai tambayar niman auren shi da Lamisah, sai Jalal da Hansatu dan Daddy yace babu inda zai nima mishi Y'a sai dai ya auri wacce ya b'ata.

         Ranar monday dakyar Parih ta tashi daga, shima sai da Aka ce ga Ya AMIDUD shine ta tashi tare da bare musu baki tana kuka, a haka tayi wanka, da aka kawo mata abin karyawan taki ci wai ita bazata karya da taliyar Bature ba, ita gaya zata ci.

       Zan iya ce muku gabaki d'aya Parih ta hana kowa sukuni, sabida zata boko, da ya tuna inda zata kuma sai ta fashe da dariya,  wai dan kar tayi rigima Mamie har da saka mata caferi son, da snack, koda aka kaita taga sun juya sun barta da ta rasa ihu, sai ga yara ƙanana suna mata dariya.
   Dakyar aka jata zuwa cikin makarantar.

    Ranar da babu abinda ta tsinana sai kuka, tasaka jakarta da aka bata tare da basket ɗin ta, tana kuka.

            Ana tashi sha biyu da rabi tazo gurin me yalo, tana zare ido.

      Ɗauka yayi ya bata, tana amsa tace.
"Nagode! Baba me yalo."

      Tana juyawa sai akan Idanun AMIDUD, sunkuyar da kai tayi tana motsa bakinta.
    Har ta shiga cikin motar juyawa yayi ya kwad'a mata rankwshi, har ta ɓare baki zata yi kuka, ya zaro wayar caji. Had'iye kukan tayi sukan tayi.

  Goge kwalla tayi suna shiga cikin gidan ta wurga da kayan tace.
"Wallahi bani komawa makarantar arna."

        Duk yadda aka so ta fahimta taki sai da Baffanta yasa baƙi, bata ga abinda aka samata a jaka ba, sai da aka zazzage nan taga kayan dad'i ta lakuci chocolat tasaka a bakinta tana lumshe idanu tace.
"Yoh Mamie indai kullum zaku na saka min wannan abun Alqur'ani bani kuma cewa ban zuwa makarantar"

             Haka tayi ta surutu, tana gama ci ta tashi, tabi kofar baya, dan taji anata aiki a can inda Jalal da AMIDUD zasu zauna da matan su, tana shiga bata tsaya ko ina ba sai inda ya kayan motsa jikin shi, irin karafuna nan.

   Tana zuwa abinda ta fara, hayewa kan wani karfe, tayi nan ta tab'a can karshe dai sai da ta balla mishi wani karfe sannan ta mai da tare da barin gurin, bata tsaya ba ta nufi kofar baya wanda ya zagaya da ita dakin shi, tana shiga taga wayar shi da laptop din shi, dake akwai nasu Buhayyah suna game, tana zuwa ta shiga goge mishi files tare da ɗaukar wayar shi tana hoto ita nan, wango robar ice cream tayi, dira tayi ta bud'e ta fara sha, tana jin motsin ta sake robar ta bangaji mirror sai da turaren shi ya fado ya fashe.
   Tuni ta ficce tare da sake kofar garammmm.

   Jin motsin ya sashi fitowa daga ban dakin, yaga a min shi d'aya d'aya da daki, ga turaren shi a fashe.
  Ga Ice cream da aka bude sai wayarshi da take ya she a kasa, da ga laptop din shi a kune.
   Komai dai a wargaje.
  Zama yayi ya dade goshi Yace.
"Parih! Dole na zane ki kai wannan yarinya ta zama fitina"

Shiryawa yayi sannan ya fito, ta tsaye a kusada Jalal da yake waya da abokin shi, ta dauko macuci roba ta rab'a mishi, Zaro Ido AMIDUD yayi....

🤔🤔🤔🤔😏😝 _Wallahi ayin mahaukaciya ce_

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now