MR AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
Dedicated to my Aunty Nice.
_HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION_
Page_13
Kafin yace wani abu, tuni ta rab'awa Jalal macijin nan a kafad'arshi, ta kuma ce mishi.
"Kaii! Wayyo ga macijin a jikinka"A firgice ya juya kafad'arshi kawai yayi mugun gamo, aikuwa ya sake wayar shi me kirar LG, sai da ta ɓare gida biyu.
Ya kuma buga ihu tare da watsar da key din motar. Ai kuwa ya fadi a sosai sai da yaji ciwo.
Dariya tasaka sannan tace.
"Kutt! Sai kace wanda aka sanya mihi maciji me rai duk ya tsorata"Duk da ran AMIDUD yan ɓaci amma bai hana shi dariya ba, musamman yadda Jalal ya birkicewa.
Tana ganin AMIDUD ta falla a guje, tana kyakyatawa.
"Sannu! Kaji wannan Yarinyar kai jama'a zan zaneta"
"A'ah! Kyaleta, yarinta ke diban ta wata rana bazata yi ba."Ya karkad'e jikin shi sannan yace.
"Bro muje!"
Duk yadda AMIDUD yaso yayi magana Jalal ya hana shi, sai ma shiru da yayi mishi.
Tunda Mamie taga ta manno a guje ta fahimci ta lakato AMIDUD shine ta arto a guje.Tana shiga d'akin ta shige cikin cikin drowe.
Koda ya shigo ya gama nimanta bata d'akin yaji haushi, haka ya kyaleta. Ya kuma kai kararta gurin Mamie.
-----
An sanya miki su cikin wata uku, dan haka suka fara shirin kai. Ranar da aka gama hada kayan su dake duk sayayyar a nan bauchi akayi tunda muna da manyan shaguna irinsu (Nasiru Bababa! Iron d'an gombe! Zubairu da Aminu! Lutaye brothers! Arabia super market! City store! Jifatu! Ga laushi da sauran shaguna, ina ga babu amfanin zuwa Kano ko Dubai 😎🤣)Parih bata gida aka kawo kayan tana makaranta, suna gama had'a kayan za a kai ta shigo tayi wurgi da jakar da basket ɗin, sannan ta zubawa kayan ido ta kalli Mamie tace.
"Wannan fantimotin waye?!"Murmushi Mamie tayi sannan tace.
"Wancan na Jalal ne! Wancan kuma na Yayan ku, za a kai gidan su Lamisah."Sam bata ma fahimci me Mamie take cewa ba, kawai abinda ya biyo bayan, shine zuduma musu ihu da tayi ta fara wurgi da komai na falon itama sai an mata kayan aure.
Gabaki d'aya ta tashi hankalin mutane, tayi birgima har ta godewa Allah.
Shigowar AMIDUD bai wata wata ba ya dauke ta, sai dakin shi.
Sai da ya kaita cikin d'akin shi sannan ya direta, ya kuma ciro bulala, had'iye kukan tayi ta koma can gefe.
"Ke zo nan!"
A hankali ta rarrafo inda yaƙe, kura mata ido yayi sannan yace.
"Me aka miki kike kuka?!"
Cuno baki tayi sannan tace.
"Nima aure za a min!"
Zaro ido yayi waje sannan yace.
"Ke ban da jaka irinki waye kika tab'a ganin anyi mishi aure shekarunki nawa ne ma tukun?!"
Kallon shi take kafin ta sunkuyar da kai kasa cikin murya me ban tausayi tace.
"Goma sha biyu!""Wawuya! Dakikiya! Banza sha-sha-sha mara kan gado keda zaki tsaya kiyi karatu kina tunanin irinta jahilai! Da wannan jakuntar zaki yi aure, sannan Uban waye zaki aura, kin ma tab'a kallon kanki a madubi! Sakarya idan kin fasa kuka a miki aure ke ba yar halak nace, ke har mace ce da zaki kira kanki a miki aure jeki jikin madubi ki ga kanki, wawuya"
Hankad'ata yayi jikin madubi, tayi kamar zata fad'i rike jikin madubin tayi tana kallon warware gashinta wanda suka zubo har kafad'arta, waye ne yake zubo mata kuka na kara cin zuciyarta. Duk da rashin hankalinta tashan bakar magana saboda ita din renon tsohuwa ce, kuma wacce ta iya sarrafa harshe, ta kuma iya magana. D'aga hannunta tayi ta tattara gashin kanta, sannan ta share kwallar dake sauka a idanunta, d'ago kai tayi taga yana gutsira chocolat na roxy, a hankali ta isa gaban shi ta saka hannunta amsa, sannan ta juya ta fita, ta kuma juya ta sake mashi murmushi, tace.
"Yau Ni kasa kuka! Sabida ka tsane Ni! Yadda na amshi wannan alewar Insha Allah sai kazo da kafarka gurin jaka! Dakikiya! Sakaryan nan! Niman alfarmata! Aure kuma Insha Allah na ajiye shi daga gobe zan fara karatu Ni dai wanda ya fasa. Ya rena kan shi."Tana fita ta sake chocolat din ta juya zuwa can bayan gidan ta zauna ta fara kuka sosai, dan tunda take ba a taba zagin, irin wanda yayi mata dole ma take gurin Iya kaka, dan tana mugun kewar ta.
........ Tunda yayi mata gori iskancine ya ragu sosai, ko zaman falo bata yi abinda ya dame mutanen gidan kenan suka sata a gaba da tambaya karshe ta fashe da kuka, tace.
"Ni kawai ku kaini gurin Iyata kawai dan ina jin kamar zan mutu idan ban ganta ba."Shiru duk suka yi, har shi kansa sai da yaji ba dad'i.
"Toh kiyi hakuri idan kuka yi hutu za a kai ki kinji ko"
Inji Alhaji Muhmood,
Gyad'a kai tayi, tana share kwalla, tashi tayi har ta kusan zuwa bakin kofar dakin su ta juya taga ita suke kallo, cikin muryan kuka tace.
"Mamie! Ko kuna da hoton Mama na da Baba na!"Mikewa Jalal yayi duk iskancin da take mishi bai gani ba, yaje inda take ya dawo da ita, zaunar da ita yayi sannan ya fita can sai gashi hoton kato a hannun shi ya mika mata, duk sun yi kura, cire hular kanta tayi ta goge kurar. Ta kura musu ido kuka ne ya kwace mata..
"Nima da suna nan da babu wanda ya isa kirana jaka dakikiya!"
Tashi tayi ta bar falon tana kuka, kowa juya ido yayi kan AMIDUD dan sun san tun shekaranjiya da tafiya da ita ta sauya baki daya, sai kuka ita da take kukan banza yau ta daina sai kukan takaici da b'acin rai.Tashi yayi ya bar falon, a hankali kowa ya watsa, Bin AMIDUD Mamie tayi ta same shi yana aiki a laptop din shi.
"Nagode sosai da abinda ka aikata min! Ƙasa marainiya kuka har tana jin rashin iyayenta yasa ake wulakantata!"
"A'a! Jal Parih da hankalinta abinda nayi kuma, babu kusakura a cikin sai ma taimakon da nayi muku! Ina gaya miki zaku ga canji".
"Wani can ji kuma? Me zaka gaya min wanda kariga da ka aikata! Wallahi baka min Adalci ba da kabar mana ita haka babu wanda aka haifa akan dai dai! Kowa yana kuskure amma ka zauna kaci zarafinta, Allah ya bamu yawan rai"Tana gama fad'ar haka ta juya tafita, daga dakin murmushi yayi kawai yace.
"Bazaki gane ba Mamie na"Tun daga lokacin bai kuma sakata a ido ba, asalima ya daina ganinta. Abin ya bashi mamaki sau d'aya ya ganta tana shiga mota zata makaranta.
Sati Daya da da mata gori, ta shigo gidan a gajiya daga islamiyya, ta kalli Jalal da yake zaune tace.
" Buroda! Pilisi gibi min yo wata"Shiru falon ya dauka sakamakon turancin Parih, murmushi tayi sannan tace.
"Sitof lukat mi! An tak tu yu!""Wow! Parih" turanci ne haka"
Satar kallon Inda AMIDUD tayi sannan tace.
"Eh kasan wasu suka niman raunin kane dan su cutar da kai kuma Allah yafi su kifi na ganinka me jakar koma! Babu wanda aka haife shi da iyawa! Dan haka daga yau karatu zan yi sai na haɗa ilimi akan halayyar mutane. Dan ina shirme bawai bansan me nake yi bane."