MRS AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
Dedicated to my Aunty Nice😊
*_Ohni Y'a su! Deejarh Ciroma! Surukata Falhat! Da sauran wadanda English Grammer din Parih ya shake ina muku fatan Alkhairi irin Sosai din nan! Abeg i no go fi tak give road meka fass😎🤣 Toh nayi shiru kar nayi magana a kiramu! Kunsan abinka da D'an karkara Ana kyauwun tare😁_*
24.
"Honey!! Kaji abinda wannan saryan take gaya maka!""Dalla ki min shiru, ke kuma na Kuma jin kinyi wancan jahilin turancin sai na kareraya kafarki na zubawa karanuka su cinye, b'ace ki bani guri."
Tura mishi baki nayi, ina kunkuni. Har na kai bakin kofa, na juya tare da cewa.
"Ebirbodi foo give mi! Bikos i mek ol up yu hangiri!"D'ago kai yayi, ya kalle ni jinjina kai yayi sannan ya zare towel ɗin wuyar shi. Cikin fusata yace,
"Bari na nuna miki ina fushi!"Nufo Ni yayi aikuwa na shige d'akina da mugun gudu. Tare da rufe kofa garammmm!
Juyawa yayi bai kalli inda Matar shi take ba, yayi wucewar shi dakin su. Dan Iya jin haushi yaji kuma yayi imani ba laifin parih bane na Lamisah ce.
Ganin yadda ya yanke fuska ya sata jin ba dad'i, bin shi dakin shi tayi ta same shi yana cire kaya zai shiga wanka.
A hankali ta isa gaban shi, muryanta na rawa tace.
"Honey! Kayi hakuri. Allah ina tsoron haduwarku da Yarinyar ce, ina jin zafinta sosai gani nake kamar zata dauke min kai ne!"Dakatar da ita yayi cikin Fushi sosai.
"Kamar ya zata dauke ni?! kinga nayi kama da Yaro ne da zata dauke ni?!, wani iri dauke ni zata yi?!"
Rike hannunsa tayi, cikin tashin hankali. Hawaye na zuba daga idanunta tace.
"Allah! Zata iya mace ce! Kuma Kanwar kace! Baya ga haka akwai aure a tsakanin ku. AMIDUD. Wallahi nasan ko baka sota dan kyau da halittar jikinta ba, zata dauketa ta hanyar amfani da girkinta. Ni dai don Allah karka kawo min ita a matsayin matar ka, dan mutuwa zan yi. Idan ban mutu ba! Zan shiga wani halin rayuwa. Don Allah."Jikin shi ne yayi mugun sanyi, riƙe hannunta yayi cikin na shi.
Tsabar yadda yaga tana kuka har jikinta na rawa, zaunar da ita yayi a bakin gado yayi, yana murza yatsunta, bai hanata kuka ba. Ji yayi zuciyarshi ta gama narkewa, ya kura mata ido. Lashe bakin shi yayi cikin nutsuwa sannan yace mata.
"List to me! Bani da niyyar kara aure! Sam ni bani ra'ayin tara mata, ki rike alkawarin a bazan tab'a miki kishiya ba. ki ajiye wannan a ranki, surarta girkinta duk basu gaba na. Ni kece a gabana. Ina sonki ko baki da komai zan zauna dake a haka Ni dai ki cire zargin da kike min.
Sannan ki lura Yarinyar nan Spain zamu tafi da ita, kamata yayi ki jata a jikinki yadda zata gaya miki damuwarta da wasu abubuwa. Bawai kina biye mata ba, idan baki manta ba na gaya miki Mahaifinta shi ya cika min burina na zama ɗan kwallon da ake alfahari dashi a Afrika baki daya, duk inda Na shiga a duniya Dabji ake kira.Please and Please, ki daina zafaffa kishinki akan Parih, sabida ba kalar matar da nake so bace, koda ina da ra'ayin aure balle bani dashi ke kad'ai kin wadatar dani, don Allah bani son kina zagin iyayenta.
Idan kika daurata da wannan halin duk inda kuka shiga zata kunyataki! Ni kuma bani da ikon magana sabida laifinki ce."
Mik'ewa yayi zai shiga ban daki har ya shiga sai ya leko sannan yace.
"Ki lallaba ta ku shiga kitchen, ki mana abinda zamu ci, kema ki iya in ba haka ba."Ya kashe mata ido, tashi tayi tabishi da gudu ya rufe Kofar ban dakin cikin shagwaɓa ta shiga buga kofar tana cewa.
"Buɗe in ba tsoron ba! Allah tunda kasan baka da gaskiya ba.".Buɗe kofar yayi cikin zafin nama ya fincikota zuwa ban dakin, kasan shower ka kaisu, ya bude musu ruwa.
Hannun shi na kan cikin ta, juyata yayi. Suna kallon Juna, cikin sanyin murya yace.
"Kece tafarko kece ta karshe! Bani fatan wata alaƙa ya hadani da wata macen bayan ke! Ina son na kasance dake har karshen rayuwata."D'ago kanta tayi tana kallon pink lips d'inshi.
Hannunta takai beard ɗin shi tana shafawa, a hankali har ta sauko dashi kirjinshi. A sannu ta shiga shafa inda yayi guru a jiki shi, wato irin budadd'yar jikin nan ne, (body building irin jikin Salman Khan 🤣😂 tarin tsokoki)"Kina son su ne?!" Ya jefa mata tambaya.
Murmushi tayi, sannan ta hade bakin su guri guda, a hankali ruwa ke kara sautin sumbatar juna da suke yi.
Cikin wani irin yanayi, suke abinsu. Tunanin AMIDUD ya tsaya cak a sakamakon tab'a kirjin matar shi da tayi, take abinda ya faru jiya ya dawo mishi, ba tare da ya fahimci abinda yake ba. Kawai ya kuma dulmiya a duniyar t-b-t.
Ganin abinshi na shirin wuce iyaka ne tasata kwace bakinta ta ture shi tana dariya da sauri ta fice a ban d'akin, dafe goshinsa yayi yana kuma hasko abinda ya faru jiya, ga kuma zafin kan da ya haɗawa kanshi da wanda Parih da Lamisah suka haɗa mishi,
.......
Cire kayan ta Lamisah tayi sannan ta daura wani b'ingililin towel ta nufi dakin Parih.Tana shiga ta same ni a bakin gado, sanye da doguwar riga.
Kallonta na fara tun daga kafafunta har zuwa kan towel din.
Ban san lokacin da dariya ta kwace min ba.Wasu sirarar kafanta irin na wannan yan gwaigwai din nan.
Rike cikina nayi sannan nace.
"De yu no, hauw yu luk?!"
B'ata rai tayi sosai, rike bakina nayi sannan nace.
"An sori! But yu luk lek babi, irin an gwaigwai din nan, wanda ake sakawa a Mbc. Meye ma sunan su, akwai katun dinsu sindirela! Da silifin biyuti! Da kuma, Biyuti an di bilasta!""Dalla rufe min baƙi, wawuya kawai. Jaka idan ma an turo kine dan ki rabani da mijina karyanki tasha karya. Wallahi sai kin bar min mijina, karya mara zuciya."
Dariya nayi, sannan nace.
"Oho dai! Kije ki tambayi mijinki akan me ya ajiye ni, ya sake Ni Naje nayi rayuwata kamar kowa mana, sannan idan turo Ni aka yi! "Rufe baki na nayi sannan na cigaba da cewa.
"Kije ki tambayi shi! Nawa yaji piraz na burodin da ya tab'a, ef yi no yu no, coman gara way mey firandi!"
*_Allah sarki! English ana cin mutuncin ka a bakin Parih 🤣😂 Akwai kura da Nagode 🤝 sosai Maman Abdul ga gaisuwarki nan_*Karku manta da Vote!