17

2.3K 389 18
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to my Aunty Nice.

Page_17
      Zura mata ido nayi ina kifkifitawa, shi kuma ya tsaya sai kallonta yake, gyad'a kai nayi sannan nace.
"Hmmmm!"
     Juyawa tayi muka kalli juna, yadda muka zubawa juna ido yasata jan bakin tayi gum tayi shiru, murmushi nayi sannan nace.
"Bari naje na nimo masu keken shanu! Su fitar mana da kayan mu"

        Ajiye ludayi dumar yayi sannan ya mike tare da goge bakin shi yace.
"Muje!"
     Kallon kwanun shan nayi, sannan na  buɗe ba zan yi magana yace.
"Muje nima naga gari,"

     "Toh mun fita" nace mata,
   
    Mun fita tare mun sami masu kuran amma ya hanamu dawowa dan yawo muka yi ta yi a saman kuran, har na gaji nace mishi.
"Mu tafi rana tana yi"

        "Ko kin gaji dani ne?!"
"A'ah kawai na fison mu isa gida da wuri ne!"
   
"Hmm" yace min, muna isa ya sauka sannan yasaka hannu zai sauko Ni na dauje sannan na diro daga keken, muka shiga cikin gidan muka kwaso kayan mu, zuwan d'an gidan wakilin hakimi ya sani zuwa gurin shi nace.
"Toh Ni dai zan tafi a rike min amana kuma duk wanda yaci amana ta, bashi karewa kalau"

   Washe haƙora yayi sannan yace..
"Ai bazaki tab'a kamani da laifi ba, i Lobi yu"

  Dariya nayi sosai sannan na kauda kaina nace.
"Meye kuma i Lobi yu?!"

     Caraf a kunne Jalal birki yayi a gaban mu sannan yace.
"A ina kika ji kalmar?!"

  Nuna mishi d'an wakilin hakimi nayi sannan nace.
"Samari na ne shi"

  Hararar ya kwad'a min sannan ya juya gurin haruna yace..
"Kar na kuma ganinka! In ba haka ba zan kai ka bauchi a daure min kai, ke kuma wuce mu karasa kwaso kayan wato har soyayya kika fara, daga zuwa hutu. Sai na gaya wa Ya AMIDUD ya dawo daga kasar da yake yazo ya zane min ke tunda baki tsorona, kinsan me yake nufi da kalmar cewa yayi zaki mutu"

     Dafe kirjina nayi ina zaro ido sannan nace.
"Na gata kaina bani kuma barin wani ya gaya min"

        Muna gama kwaso kayan naje jikin Iyata na saka mata kuka nace.
"Iyah a dey mis yu!"

    Cikin tausayawa jikarta, dan tasan ta had'u da iftila'in rayuwa, yatsina fuska tayi sannan tace.
"Allah ya kawo miki karshen wannan iftila'in da ya shiga rayuwarki, amma akwai matsala"

        Haka muka bar garin cike da kewar juna, ina share kwalla na har muka bar garin.

     Hannun shi naji akan nawa, d'ago kai nayi ina kallon shi, janye hannunsa yayi, tare da shafa kan shi.

   Har muka isa gurin motarshi, aka zuba kayan har cikin motar, tunda ya buɗe min gaban motar na zauna, shima ya shiga ya tadda motar sannan ya mikawa me keken kuɗin shi, kafin ya tadda motar, ya janyo hannuna ya daura kan motar, yana tuki da ita. Zaro ido nayi kafin nace.
"Raba ni da Y'ar akurkura"

   Sake hannuna yayi sannan ya lakuce min hancina,  kafin yace.
"Ina kaunarki!"
Ya fad'a a hankali, dariya nayi sannan nace.
"Nima haka, amma me haka ke nufi?!"

           "Bazaki gane ba sai nan gaba idan kin kusan gama school!"
            Gyad'a kai nayi sannan  nace,
"Kana da kirki! Kuma kafin wancan mummuna kyau!"

  Ware idanun yayi sannan yace.
"Ya AMIDUD! Sai na gaya mishi"

Dafe hannun shi nayi cikin sanyin jiki nace.
"Kayi hakuri! Bani kumawa."

      "Shi kenan!"

     Komawa nayi na cigaba surutu tare da bashi labarin abinda ya faru dariya yake, har muka iso darazo anan naga doya da kwai nace sai na ci.
Ya kuma saya min,

          Karfe biyar muka iso dan koda muka iso bai kai Ni gida ba,  sky crown ya kai Ni muka sha kankara me dad'i.
  
Dakyar ya kama hanyar gida duk sai ya diririce, yace.
"Parih! Karki gayawa kowa mun zo nan kinji, kuma karki gaya musu na"
Sai yayi shiru kamar zai fashe da kuka.

    "Ai bazan gayawa kowa ba, indai kullum zaka na kawo Ni shikenan babu wanda zai ji abinda ke faruwa kaji."

     Lakuce min hanci yayi sannan yace.
"Ni zan dinga kai ki makaranta ina dauko ki, sai muna zuwa musha abin dad'i"

  Gyad'a kai nayi sannan muka cigaba da tafiya, har muka iso gida da murna su Amrozia da Buhayyah tare da Aarib.....

Kuyi hakuri bamu da wuta🙄💁🏻‍♂️ dan haka kuyi hakuri, Kayya Yasin ku kara Vote.

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now