MRS AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
https://my.w.tt/XGvckkY6N6
Dedicated to my Aunty Nice😊
49.
Sam bai da nutsuwa haka ya fita, bai dawo ba sai dare.Yana shigowa yasan ban fito ba ya shigo.
Duk yadda naso kaucewa dan karya lallabani, nayi karshe haka ya rungume ni nayi kuka har na godewa Allah nace.
"Ina jin yunwa?!"
Fita yayi ta kofar dakin, ya je kitchen ya dafa min Indome, sannan ya, kawo min da tea.Ban d'aki ya shiga ya haɗa min ruwan wanka, na shiga da taimakon shi nayi wankan sannan na fito.
Mika min pant dina da pad yayi na saka, sannan ya saka min wata yar rigar shan iska, ya zauna ya shiga bani abincin ina ci a hankali.
Idan naji jiri sai na maida kaina jikin shi a haka, har na koshi.
Ya bani magani nasha tare da kwantar dani.
Fita yayi da kayan yaje ya dawo, wanka yayi sannan yazo ya kwanta a bayana, a hankali barci ya tafi damu bayan yayi mana addu'o'in.
.......
Washegari.
Ya rigani tashi, dan haka bayan yayi sallah, ya taimaka min nayi wanka nazo na kuma gyara jikina na kwanta.Barci me nauyi ya dauke mu, bai tashi ba sai karfe goma saura, daga shi sai Boxes da shimi.
Lamisah tana falo, ita da Sabriyah suna tattaunawa kawai suka ganshi ya fito daga dakina ya manta ma shikam.Wuce su yayi abinci cikin tashin hankali. Ta mike tare da bin shi kitchen ɗin.
"AMIDUD! Daga dakin Parih kake?!"
Ta tambaye shi.
Kai tsaye yace mata.
"Eh sabida matata ce! Ko kin manta naga miki Mrs Amidud zata zo! Kuma zata dauke bukatar mijinki! Toh Parih ce! Kuma bawai amarya bace, kece amarya dan ita aka fara daurawa aure wata uku kafin baki! Dan haka am so sorry dana gaya miki a lokaci ƙurar....."Da gudu ta fito daga kitchen din Ashe ta dauki wuka, shima bayanta ya biyo,tasamu ta shiga d'akina zata dabb'a min ya fincikota ya falla mata mari, sannan ya turota waje!
" Nazata kina da a hankali ne! Ashe bababr Mahaukaciya ce ke! Lamisah baki dauke hakkina na aure ba, idan kika sami cikina zubdawa kike yi, ban san dadin abincin ki ba, ce miki akayi zan cigaba da cinki ne babu me dad'i daga gareki, ban tab'a sanyaki Abu kiyi ba, Amma ita final shekaranjiya na zubda mata cikin da bata san dashi ba.
Amadadin tayi dogon fushi dani addu'ar shirya ta min, amma ke sau uku kika zubda min cikina ban san meye dalilin ki ba. Maza ki hada kayanki ki wuce naija zan zo. Ke kuma Sabriyah ki tattara kayanki ki wuce gurin mijinki!"
Shigowa yayi ya same ni a zaune ina kallon shi, fita yayi ya dibe can sai gashi da jaka yazo ya debi kayanmu.
Ya hada kome, sannan ya zo ya samun kaya da takalmina, muka fita.
Airport muka wuce, daga can muka tashi a jirgin Pakistan.
Karach muka sauka, anan ya kaini asalin gidan da aka haife ni, inda ya kaiwa tsohuwar da ta sanya min sunar Jal Pharih!
Tsuhuwa Gul Nasreen, tare da Ƴaƴan ta da jikokin ta.
Anan ya gaya mata ai nayi bari ne. Murmushi tayi tasanya aka nimoe mata wasu itaccr
Ta fara dafa min ina sha, tare da sawa ana min dilke, ga wasu hadi na musamman wanda yaji madara.