16

2.3K 316 35
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to my Aunty Nice.

_😎🌹😍 Yardan Allah da Manzo Allah yana tare da Yardan Miji da Iyayen! Albarka Iyaye yana zagaye da wanda ya yardan da biyayya🌹 Soyayyarku a gare Ni daga Allah ne Ni kaina ina mamakin Yadda Allah ya had'ani da dattawa masu halin girma da mutumtaka 😊 Nagode Mommys da Auntys! Allah ya bar zumunci sonsoriya Domin Allah_

Page_16

Jinjina kai tayi cikin tashin hankali, alamar ta gamsu da Yaren karshe da na mata, cikin jimami tace.
"Da alamu aljanun da suke jikin Yarinyar nan dirka dirkan ne, domin ita d'aya sai nishi take bari na tattara ta mu koma gida, tunda nan gurinki abun yaki."

Wani sowa na saka tare da mik'ewa nace.
"Wififififi?!"
   Sannan na sauke ajiyer zuciya karya na kwanta warwas, ko nace hannu sakayau. Dakyar Iya kaka tattaro Ni muka nufi gida, muna tafi nake atishawa, ina zance.
"Zanci namar kaza"
   "Muje yar naje y'ar nan! Aiko me kika ce zaki ci za a yanka miki"

     "Toron agwagwa zanci!"
"Aiko d'an maraki kika ce zaki ci zan baki muje Allah ya baki lafiya."

   Wato a cikin yan kwanaki da nayi a dabji naci kaji da agwagwa da zabi, sai zuma da nasha son raina."

           Ina da kwana ashirin sai ga Jalal yazo, munsha yawo dashi da zai koma kamar dai ranar haka yayi ta min rigima Ni kuwa ina ta dariya har ya tafi.

      Spain....
  Shigowa yayi a gajiye yana zub'ewa yayi a cushin.
      "Misah!!"

  Ya kirata,  yadda ya fita  hakan ya dawo ya same gidan sai a hankali, tattara komai na falon yayi sai gata tafito daga ita dai wata doguwar riga barci, mika tayi sannan tace.
"Honey! Ka dawo?!"

       Girgiza kai yayi sannan yace.
"A'ah tsirowa nayi!  Kalli gidan nan har kunyar shigo da abokaina nake, Tsabar kazamta da son jiki wai duba ko ina da kome a watse sai da na tattara Haba don Allah"

   "Ayya! Honey, na gaji ne kuma ai kaine kake gajiyar dani shi yasa nake rama barcin jiya! Kuma batun gaskiya Ni ban iya aiki ba, sai dai ka nimo mana me aiki"

         Kamar ya rufeta da duka ya kalleta cizon lips din shi yayi sannan ya mik'e tare da tattara kayan shi ya shige dakin shi wanda kullum yake gyare, sosai yake bakin cikin lalacin Lamisah dan shi da farko ya zata ciki ne da ita, sai gashi ashe lafiyar ta lau.
        Tana ganin ya shiga daki itama ta koma d'akinta.

       Haka suke rayuwar su abin tausayi, dan kullum yana hanyar gidan abinci ko shi ya girka musu, gashi abinci a kasar Turai musamman namu na gargajiya masifar tsada ne dashi dan sai kaga dan mulmulen tuwo sai kaji kudin shi kamar zai kaika wani yanki na daban.

           +++
  Ana gobe hutu na zai kare sai ga Dan wakilin hakimi yazo, zance gurina. Iya kaka kuwa sai murna take wai Jikar ta tasami mijin aure.
                 Cab'a kwalliya nayi kamar zani gasar kyau Ina fitowa na tsaya. Cikin Mugun turancin kare dangi nace.
"Barka da zuwa my suwetin hat, kasan weya tugeda"

   Gyad'a min kai yayi cikin jin dadi ya samu yar binni mana ya washe haƙora yace.
"Hmm! Me kika ce?!"
Gyad'a kai nayi sannan nace.
"Amma Haladu ance min kana zuwa binnin kuma ai kanajin turanci"
    D'aga min hannu yayi kamar wanda aka kama yayi laifin yace.
"Dan datse, ko yas da go bani ji"

    A tsorace na zaro idanu nace.
"Alqur'ani! Bani soyayya da kai sai ka koye Yes da go"

     Na juya mishi baya ina murguda mishi baki,  kamar wani sauna haka yayita rokona sannan nace.
"Kaga Ni yanzun makaranta nake bani aure yanzun sai nayi ilimi nima na rama wulakancin da aka min."

    Cike da bakin cikin yace..
"Amma baki ga Aairah an kai baiko ba."

             Tsaki naja tare da shigewa nace.
"Kwarankwatsa! Allah sai ya saka min taci amanata."

              Karshe haka na barshi a waje cike da bakin ciki, dan wallahi ko kashe ni, za ayi bazan tab'a yarda na aure yi auren cin amana ba.

  Ina shiga dakin Iyah na fasa mata kuka, ina gaya mata abinda ke faruwa dani itama dake ta iya taya b'era barna tace.
"Barni da yar banza me kama da Banu ƙasa-ƙasa"(😂🤣💁🏻‍♂️ ji wani zagi wai banu ƙasa-ƙasa)

       Sosai nasha kuka, tun a daren Iyah ta had'a min tsaraba da zan kai bauchi, manshanu, zuma, kwai, da daddawa, bankono, citta, garin dakka na geron kunnu, sai kukar miya, garin kub'ewa. Sai zabuwa da kaji uku, sai soyayye nama wanda ta zuba mishi yajin me dad'i. Wanda aka had'a da adinar mota,. Sosai aka hada min tsaraba.

     Da dare ina barci ya kama kafata ta kunsa min lalle har da hannu, washi gari da safe bayan nayi sallar asuba na sameta a madafi, ina zuwa ta mika min miya a ludayi nasha ina yatsina fuska, sannan na tashi na shiga wanka, ina gamawa Jalal na shigowa gidan, dariya na mishi sannan nace.
"Wannan uwar sammakon! Ko ana ka kwana ne?!"

    Girgiza kai yayi sannan ya gaida Iyah bashi kujera nayi ya zauna, sannan na dauki kunnu gwab'el na ajiye a gaban shi wanda akayi da dafaffiyar madarar saniya sai kindirmo saboda yayi kamshi ga kamshin kanunfari da citta da yake tashi. Ajiye mishi nayi a gaba, sannan na amshi nawa na, kosen da aka sayo min na ajiye mishi.
  
   Saka ludayi duba yayi ya fara sha, lumshe idanunshi yayi sannan ya bude akaina kafin yace.
"So sweetest"

   Washe baki nayi da jin sabon kalmar turanci wato.
*Son suwetie"

   Gyad'a kai nayi nace
"Hmm! Ya matar ka? Kuma Yasu Mamie na da Aunty"
  
"Kin hanani sakat shi yasa nazo na maidaki gida da kaina na"

Zaro ido nayi sannan nace.
"Ta ina na hanaka sakat ga tulaliya Matarka Ni babu ruwa na kar ka ja min bugu"

        "Kai Jalalu, zan baka aika ka kaiwa Muhmood ka gaya mishi a nimawa Parih magani domin magirkan ifiritai ne bisa kanta ai ranar da kuka zo an sha artabu, dan ma Allah yayi Ni da kashi d'aya, sai da nayi ta buga su da kasa kafin suka tafi."

    Sake baki nayi ina kallon yadda Iyah ke gundura zance, sake baki nayi ina kallon ta, cike da mamaki har da nuna min ita din jar wuya ce.....
  Ko ya zata kaya gobe😂🤣💁🏻‍♂️

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now