36

2.8K 505 34
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

https://my.w.tt/XGvckkY6N6

Dedicated to my Aunty Nice😊

𝓜𝓪𝓲_𝓓𝓪𝓶𝓫𝓾❦︎

  

36.
     Ina zaune a gurin har muka fara barci, yana can yana fama da sugular shi.

    Dakyar ya fito har ya shiga wanka, kawai sai a lokacin ya tuna ko ina d'akina.

               Da sauri ya sauko daga sama, ya nufi d'akina yana budewa yaga bana ciki ga kayan da muka dawo dashi a falo.

    Fita yayi waje yana nima na, can ya hango ni, zaune munata zuba gyangyadi.  Yana zuwa Abinda Ya fara shine d'aga karen daga cinyata ya kai cikin gida, ya ajiye min shi a d'akina.

   Cikin tafiyar shi me cike da kuzari, ya iso gare ni. Durkusawa yayi yana kallon yadda na tsuke bakina, had'iye yawu yayi sannan ya kai yatsar shi saman lips dina ya shafawa.
   Wani irin kasala ce ta sauko mishi, a hankali ya furta cewa.
" Nayi ƙoƙari! Lamisy gani nan zuwa gareki."

Dauka ta yayi ya nufi cikin gidan dani, gyara kwanciyata nayi tare da sakala mishi hannuna a wuyar shi.

         Yana shiga falon ya tadda, Lamisah tsaye tana kallon shi, kishi ya gama rufe mata ido, kamar zatayi kuka tace.
"Honey! Tunda muke da kai baka tab'a daukata ba, kai ko ranar farkon mu na Amarci baka dauke ki ba, dukda kafi kowa sanin yadda ka same ni, amma shine kake daukar yarinyar da ba matar ka ba..!

      Jan kuka tayi cikin damuwa da bakin ciki ta cigaba da cewa.
"Tsabar rashin tsoron Allah ka dauko balagagiya a kan hannunka, Wallahi idan ban kasara Parih ba, shegiya Uwata da Ubana suka haife ni"

     Ko kallonta bayi ba, ya wuce dani dakina, ya kwantar da ni,

       Ai tunda ya kwantar da ni ya dawo, suka kwana suna rigima, da safe ya samu ya shawo kanta, kafin ya fita dan sai da na gama mishi abin karyawa na koma na kwanta.

              Ina barci naji anata hayaniya, fitowa nayi naga wasu yan mata dogaye dasu.

          Dake daga Ni sai dogon wando blue Black, Sai farin shirt me hoton heart a kirjin. Gashina a hautsine kamar anyi yaki akaina.

          Zuba min ido suka yi cike da mamaki, banyi tsammanin suna jin Hausa ba, domin basu min kama da yaren hausa.

                  "Keeee! Ina kika samo me kyau sosai haƙa?!"
         
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace.
"Kanwar AMIDUD ce! Aka kakkaba mishi muka zo."

            "Gaskiya yarinyar tayi min."
       Ina jinsu nayi wuce kitchen abina, dan ban son kallon kurilla.
      
    "Lamcy! Uban waye ya baki shawaran kawo wannan Yarinyar, bayan kina kallon yadda take. Kina hauka ne zaki barta a gidan ki."

Murmushi tayi sannan tace.
"Hmm! Iyayen shi suka hada ni da ita, kuma kinsan honey da bin iyaye. Shi yasa bai musu ba, muka tawo da ita gata bata da kunya, kullum fada suke dan haɗu like water ne Fire"

       "Amma anyi babbar mahaukaciya, uban waye ya gaya miki dan basa shiri, zai hana komai. Ina ruwan rashin shirinsu bayan kota wani hali zai iya mallakar ta."

     "Kai Wannan ma bazai tab'a faruwa ba, domin kuwa ya gaya min bazai tab'a min kishiya ba,asalima baya kaunar yarinyar. Me zai yi da ita, nasan halin Honey ba kowacce irin mace yake so ba."

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now