MRS AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
https://my.w.tt/XGvckkY6N6
Dedicated to my Aunty Nice😊
*_Hmmm! Gaskiya Al'amarin duniya da ban mamaki yake! Koda yake bazan yi mamaki ba dan Yau zan gundira muku wata Yar labari 🤫😜 sai dai karku ƙaryata Ni! Domin Ni dai jirgin Suna nake nima! Da ma ba komai bane 🙄🤭 Dijarh Ciroma! Mrs Umar! Don Allah karki karya tani!😂☹️☹️! Wai dama nayi mafarki gani a cikin masu kudin Duniya! Irin su Bill nd melinda gate! Karku damu! Idan suka bani miliyoyin dollar 🤣😂🤸 zan toh kun dai fahimta! Deejarh Ciroma! Me haka yake nufi dan mafarkin har dasu Uncle Dan gote! Dasu Tahir Mangal saura wata tace bata fahimci Yaren da nayi ba!_*
__________________________
Deejarh Ciroma wai meye mafarkina yake nufi! Ke zaki bani amsata tana gareki 🙄🤭
_________________________29.
Komawa gefe nayi na zauna, ina kuka takure kaina nayi tare da sake kuka, d'ago kai nayi ina kallon yadda kowa ke rayuwar shi.
"Yan mata!" Aka kira ni ta gefe na! Zubur na mike dan wani mutum ne shi ba mace ba shi ba namiji ba.Yarfe hannu yayi yana rangwad'a yace.
"Karki damu zan taimake ki ne! Ko baki son taimakon"Barin gurin nayi da sauri na fara tafiya hawaye na zuba daga idanuna. Gashi nasan mun kunsan tafiya.
Ganin mutumin na bina, na kuma kwala kirawa Ya Amidud! Tare da buga kafana a kasa ina kuka.
"Auu! Yar nan! Almatsotsai gareki?!"Ya jefa min tambaya, banza nayi dashi.
Can na samu inda babu yawan mutane na zauna tare da dafa kaina ina kuka.
Shi ko mayyen sai surutu yake min.
.......
Kamar mahaukaci haka ya dawo gurin, yana nima na. Sai a lokacin wasu suka fahimci ashe dan kwallon nan ne na real Madrid!Aikuwa suka tsayar dashi akayi ta self,
(musamman Snapchart 🤣😂 Yana kara min kyau wendi i get miliyan 60 i go fee bayani).Dakyar suka kyale shi ya cigaba da kuma na. Tambaya yake wasu suce basu ganni ba wasu su wuce shi.
Wayar shi ya ciro ya fidda hotunar da muka yi yana nuna musu, nan ya hadu da wani yake gaya mishi yanzun na bar gurin nayi baya. Bai gama jin maganar yayi hanyar a guje yana gudu tare da duba Ni. Idan hankalin shi yayi dubu sai da suka tashi. Ran shi yayi masifar b'aci.
Yana cikin gudun yaja birki ganin yadda na kifa kaina ina kuka, sai wannan mata mazan da yake kusadani.
"Jaaaaaal!" Ya kira suna na a hankali. D'ago kai nayi dan ban zaci zai zo gurin ba.
Kauda kaina nayi na kuma dake kuka me cin rai. Har jikina na rawa, hararar Mata mazan yayi da sauri ya bar gurin, shi kuma ya karaso gurin da nake ya zauna.
Matsawa nayi tare da ture shi nace.
"Filis libi mi a lon!"
"Bazan tab'a barin ki ba, dan kin shigo rayuwar AMIDUDDAWLAH!"
Kuma matsoni yayi cikin masifa na juya zan mishi tsiwa. Yadda naga idanun shi sunyi jajjur, ban san lokacin da na fada jikin shi ina kuka ba.