MRS AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
https://my.w.tt/XGvckkY6N6
Dedicated to my Aunty Nice😊
*_Kun Fara ko? Yan Sansanin Mai_Dambu😎😂 Alkawarin da AMIDUD ya dauka bazai tab'a karyewa ba dan haka kujawa Tauraruwan ku kunne! Ta fita idanun Mijin Lamisah dan mutuwa zata yi idan ta rasa shi😏🙄 Na dai gaya muku😜 I tinki yu gais yu ondastan wata i sae! Ina jinjina ga d'aliban English 😝_*
Ina tausayawa English 🤨😪😭
25.
Ai kuwa a fusace tayo kaina, kamar kububuwa fuuuu.Mik'ewa nayi tare da buga tsalle ina zare idanuna, nace.
"Yanzun don Allah! Dube ki fa! Rabcecciya irinki, ko nace zundumemmiya haka sake kice zaki yi fada da yar miciciya irina! Don Allah ke baki ji kunyar kanki ba?!Wai ma tukun wannan fusatar na me?! Luk i go get yor time! Filis i dan't hab time two faiti jus lib mey rum!" Na nuna mata hanyar.
Dariya tayi sosai sannan tace.
" Jaka jahila! Wacce bata san abinda ke damunta ba, kuma wallahi idan kika shiga rayuwar mijina sai na hallakaki."Dariya irin me cusa haushin nan nayi, sannan nace.
"Dama akan wancan sikagon kike magana! Ai wallahi ko a jikina Ni mijinki ance yana gaba na ne! Mutum fuskar shi kamar dodo, shi yasa hadaku yayi amfani shi dunkunkuna kuma zilaziya! Filis comat foo mey rum! Ef nut a go box yu!"Zaro Ido tayi waje, ganin yadda naja layi tare da dunkule hannuna! Irin yar caskalen nan.
Ai bata fasa ba ita burinta ta dake ni, kuma dama kuma kuri ce! Ba wani iya fadar zan yi ba kawai sai na yanki jiki na fadi na shiga matagungun! Ina wani botsarewa ina kaffafewa ina botsarewa.
Tsoro ne ya kamata ta fita da gudu tana kiran mijinta, tana fita na mike abuna. Na kad'e jikina na gyara zama na a kan gado.
Kaman wasu yara suka shigo dakin har suna bangaje juna, d'ago kai nayi cikin mamaki nace.
"Lafiya kuka shigo min kamar wasu zakuna?!""Honey! Wallahi aljanun ne da ita? Yanzun ta fadi a nan tana fisge fisge. Kuma"
"Kinga bani son shirme! Bana son haka. Kinga yadda zuciyata ta tsinken kuwa, kizo kin firgita Ni"
Yana gama fad'ar haka ya bar dakin dariya na saka mata nace.
"Yi dey pile weti mi, hmm a go tichi yu leshon. Coman Gara way, i rifintin agan"Babu yadda tayi iya dani haka tafita daga d'akin.
Tana shiga nasu tasame shi yana shiryawa, zama tayi ta fashe da kuka. Me cin rai ajiye turaren Black men yayi akan mirror sannan ya tawo gurinta.
Zama yayi a kusa da ita, tare da riko hannunta cikin nashi.
"Don Allah! Karki yi abinda zai tab'a kimar ki, a idanun yarinyar. Na fison ki ja girman ki bane kulata, yanzun ki gyara jikinki zan je na sakata tayi abin karyawa. Ki daina kulata"
Jin shi kawai amma a ranta sai ta wulakanta PARIH a gidan yau din nan matuƙar ya fita ya bar gidan.
Fita yayi ya barta a cikin ɗakin, ya nufi d'akin PARIH. Doka kofar yayi, ya dame ni a zaune.