Page-9

2.4K 319 24
                                    

MR AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to Aunty Nice.

'''Kaunarki Na daban ne Ummu ilham ga shafi nan baki ke d'aya 😍'''

     🙄
*Na lura da maganar Auren Parih ya dame ku Yo ita ko a jikinta😒💃 saima rawa tane*

Page_9️⃣

      Washe hakori tayi sannan tace.
"Baffana! Ince idan nayi auren anan zan zauna!?"

     "Ai dole ma ki zauna a nan!" Alhaji Muhmood yace mata.
"Toh Baffana waye min!"
      Tasaka hannu a habb'arta!

   "Eh toh! Nima ban san shi ba, sai Allah ya kawo miki."

   Shiru tayi dan tunanin ta duk ya kulle, can tace.
"Toh ita wancar doguwar waye Zata aura?"

    Shiru yayi yana kallon Mamie, girgiza kai tayi sannan tace mata.
"Ai ita matar Yayan kuce!"

   Tura baki tayi kamar zatayi kuka tace.
"Toh wallahi a nimo min mijina ko kuma na hanasu auren"

  Zaro ido waje suka yi, tare da jinjina kaurin kan Parih dakyar suka lallaba ta, ya bar falon.

          Bayan tafiyar Lamisah tayita mita, ita bata ga wani abin burgi a jikin Lamisah ba.
"Haba ku baku ga yadda take ba mutum sai kace sanda rake"

   
       Babu wanda ya kulata haka ta gama mitarta har tayi barci a gurin.

       Bayan sati uku sai gasu Fahhamah da Fahmeedah, sun zo huta dake suna karatunsu ne a Jigawa.
           Anan suka kasa hakuri da Parih kullum sai sun maketa ita kuma ta lalata musu abinsu me kyau, idan suka yi magana Alhaji Muhmood ko Hajiya Adawiyah  su musu fad'a, haka zasu zauna da Jalal suyita mita suna zaginta, idan tazo wuccewa suka ja mata tsaki d'aga kafada take tace.
"Oho dai Allah kad'ai ke kaunar kura(🤷🏻‍♀️) haka zaku ganni ku barni sai ma nayi aure na barku da cizon yatsa" (💃)

          Tana gaya musu haka zata wucce ta Barsu da masifa.

       -----
Yau tun safe ake gyaran gidan ana dafe dafe, ga shi sai sintiri ake, koda ta samu tayi sallah bata zauna a cikin gida ba, waje ta nufo tana tsaye a bakin gefe sai kallon mutane take, can ta juya taga Amrozia da Aarib sun wuccewa da Jalal abin karyawan shi, dan tana fitowa shima ya fito zai je aika, tana ganin sun koma ciki ta juya taga dandazon almajirai.
   "Ku almajirai! Kizo nan."
Da sauri suka zo tace.
"Ku tsaya na kawo muku abinci ai kuma rabonku ne ya tsago"
     "Eh" suka ce mata, haka ta je har kofar Jalal ta dauko abincin da ta juye musu tass sannan ta mai da mishi kwanon ta rufe tayi cigaba da tsayuwar ta, dai dai lokacin da ya dawo bai ce mata komai ba sai ma Binta da yayi da ido, ta kuwa murguda mishi baki.
               Kauda kai yayi yana jin haushi a ran shi idan ya kamata sai ya mata abinda bazata manta da shi ba.
                 Wani mahaukaci ne yazo wuccewa sai cewa yake.
"Yesu! Yesu!! Yesu!!!"

             Sai da ta shiga cikin gidan sannan taje kofar Jalal tace.
"Kai! Dukundukun angon tsaka nice na juyewa Almajirai abincinka."

  A fusace tafito aikuwa ta arce waje da gudu, ya kuwa bita, makalewa tayi a bakin kofa, yana fitowa tace.
"Yecuuuuuuuu!"
  Ai mahaukacin nan ya wulwula dutsen dake hannun shi sai goshin Jalal, sannan ya kuma biyo su, ta shige gidan a guje ta rufe shi a wajen mahaukacin ya rufe shi da mugun duka yayiwa Jalal Ni kuwa ina shiga na manta da wani can a waje, hayaniyar jama'a ya fidda Baba me gadi. Yaga irin ta'asar da akawa Jalal.

     Dakyar ya kimkime shi zuwa cikin gidan, daga nan aka wucce dashi asibitin rimi.

          Sai wajen biyar aka dawo dashi lokacin gidan cike yake da baki, Parih nacan dakinsu tana barci dan tunda ta dawo cikin gida takama barci, dakyar ta tashi tayi sallah, tana idarwa ta koma.
       Hayaniya mutanen gidan ya fidda ita, sanye take da riga da wando na barci sky blue, sai gashinta da suka yi tsage tsage.

   Ko kallon su batayi ba taje ta dauko abincinta, ta zauna a gabansu dan bata fahimci suwaye bane tana buɗe abincin taga kuskus, kallon Mamie tayi kamar zata yi kuka tace.
"Allah bani cin tsakin nan, ranar haikeni yayi yau ma kuma naci Alkur'an mutuwa zanyi."

       "Kije abaki tuwo!"

   Mik'ewa tayi can suka ji ihun ta, tana buga kafa  a kasa tana cewa.
"Wallahi bani cin wannan tuwon baki dashi."

     Mik'ewa yayi yazo inda take ya kura mata ido, kafin ya yanke fuskar shi yace.
"Dauka! Ki cinye ko na miki dukar da kika sa mahaukaci yayiwa Jalal."

         D'ago kai tayi zata masa gardama yace.
"Now!"
    Dangwara abincin tayi ta fita da gudu, zuwa waje.

         Tayita kurma musu ihu, tab'e baki Aunty Amarya tayi sannan tace.
"Wallahi Son Yarinyar bata jin magana, kuma ana magana Alhaji yayi ta fad'a wai bamu ganin maraicin tane, shi yasa bana magana na zuba musu ido."

    Jan waya caji yayi ya fita zuwa wajenta tana zaune ta cusa kanta a  tsakiyar cinyarta.
"Zaki tashi ko sai na zane ki"

     Ciro kanta tayi taga bulala, zaro ido tayi ta mik'e jikinta na rawa dan ba'a tab'a fuskarta ba, sai dai Iya kaka taja kunnen ta.

            Tsoron dukar ne ya rufeta dan dole ta koma tunda ta shiga daki, karshe zazzaɓi ne ya rufeta ta kwanta.

          Tayi kuka har idanunta na yaji. Tana yi tana cewa.
"Mayye kawai mumuna dashi! Daga zuwan shi yasani kuka sai nagaya wa Baffana wani yazo ya sani kuka,har yace zai zane ni"
  Jan majinarta tayi abinta tana kuka tana jan majina har barci ya kuma saceta.

        ......
"A'ah AMIDUD! bana so karka kuma kai idan da adalci yar Abtisham bata cancanci duka ba, koma meye tayi babu ruwan ka, taya zaka dauki bulala kace zaka zaneta gaskiya banji dadi ba."

    "Kiyi hakuri Mamie! Amma kuma Mamie wannan abinda kike mata wallahi babu gata a cikin ta sai don kai taya zaki zuba mata ido, tayi abinda ta gadama yau badan Allah ya kare ba ai da mahaukacin nan ya kashe Jalal."

        Sosai ya nuna musu  basu kyauta ba amma mamie taki,

         ...... Da dare da ake zo cin abinci a nan ne suka haɗu da Jalal, kallon shi tayi ta fashe da dariya tace.
"Ka ga bakinka kamar an aunaka da danki! Himili guda! Ina ruwan rangwangwan sai kace budurwa jab'a"

    "Kee!"
Ya daka mata tsawa, juyawa tayi ta kalle shi, da taga Baffanta a kusa da ita, komawa kusada shi tayi ta murguda mishi baki, tare da cewa.
"Baffana kaga wannan d'azun bulala ya dauka zai zaneni! Ni dai ka kaini wajen Iyata"

      "Kul! Kar na kuma jin kince mishi Wancan shine yayanku Amiduddawlah! Kina ina ya dawo"

    Tashi tayi daga gurin cin abinci ta koma falo ta fasa kuka, diban Abincin Mamie tayi ta biyota har falon.

          Zama tayi kusa da ita tace.
"Parih zoki ci abinci nasan baki ci na rana ba"

   Kallon Mamie tayi sannan tace.
"Ina son ganin Babana! Nima"

    Jikin Mamie yayi sanyi ta hanyoyi jikinta, sannan tace.
"Parih baki Son gaskiya! Idan an miki fada sai ki gudu baki san Abbanki bazai yi alfahari barin baya ba, Yayanku ne AMIDUD karki kuma ce mishi wancan, kuma ki daina tsokana kinga garin tsokanarki an fasawa Jalal baki har da kai"

Dariya ta kyalkyala sannan tace.
"Wallahi baki ga yadda bakinshi yayi ba kamar na saniya"

🤣🤣🤣🤣🤣😂 _Wannan yarinya ana  yabonki sallah kin kasa alola_

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now