MRS AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
https://my.w.tt/XGvckkY6N6
Dedicated to my Aunty Nice😊
𝓜𝓪𝓲_𝓓𝓪𝓶𝓫𝓾❦︎
🤪🤭
𝘈𝘭𝘲𝘶𝘳'𝘢𝘯 𝘤𝘰𝘮𝘮𝘦𝘯𝘵𝘴 𝘥𝘪𝘯𝘬𝘶 𝘯𝘢𝘯 𝘩𝘪𝘬𝘢 𝘻𝘢𝘪 𝘺𝘪, 𝘯𝘢𝘴𝘢𝘯 𝘥𝘢 𝘺𝘢𝘸𝘢 𝘴𝘶𝘯 𝘨𝘢𝘮𝘢 𝘻𝘶𝘣𝘢 𝘪𝘥𝘰 𝘴𝘶𝘨𝘢 𝘠𝘢𝘥𝘥𝘢 𝘈𝘮𝘪𝘥𝘶𝘥 𝘻𝘢𝘪 𝘬𝘸𝘢𝘤𝘪 𝘬𝘢𝘯𝘴𝘩𝘪 𝘢 𝘬𝘶𝘭𝘪𝘯 𝘨𝘰𝘳𝘢𝘯 𝘥𝘢 𝘑𝘢𝘭 𝘗𝘩𝘢𝘳𝘪𝘩 𝘵𝘢𝘺𝘪 𝘮𝘪𝘴𝘩𝘪...... 𝘐𝘕𝘈 𝘚𝘖𝘕𝘒𝘜 𝘏𝘈𝘙 𝘒𝘜𝘓𝘓𝘜𝘔♡︎
39.
A hauka ce Lamisah tabi Ya Amidud da ido, kamar zata rufe shi da duka, Alqur'an ya razana amma dake namijin duniya ne.
Tsaki yayi cikin b'acin rai ya rufe ta da bala'i.
"Ban da sakarci me zan yi da yarinya irin Pharih! Yarinyar da ko wanka bata iya yi ba, zuwa nayi daukota ban san me ya faru ba naganta kamar mahaukaciya, koda na tambayi malam sai suka ce haka kawai ta yanki jiki ta faɗi tana birgima, amma dake baki da lafiya kina zargina zan ci amanarki!Toh idan nace zan yi auren zaki hanani ne? Ba yau ba. Ba jiya ba ba gaya miki wallahi bana sha'awar wata mace bayan ke! Me na nuna na rasa, gaskiya idan kika cigaba da abinda kike min zan iya sauya akalata akanki Please muyi rayuwarmu kaman baya. "
Dake wawuya ce bata san karatun d'a namiji ba, ita miji na sonta, ba zai tab'a mata kishiya ba dan hauka. Nan suka wuce abinsu, ko ta kaina bai bi ba.
Tunda na shiga daki nake kuka, Insha Allah daga yau bazan sake barin shi ya tab'a Ni ba.
Sallah nayi sabida dan gaban mu kadan akwai wasu yan Karachi, har sun gina masalaci da islamiyya, tun da na idar da sallah na kwanta.
Cikin barci naji anyi sama dani, buɗe ido nayi na sauke akan shi. Siririn tsaki nayi tare da hantsilawa na diro a gadon. Cikin ido na kalle shi sannan na kauda kaina. Zan sauka a gadon.
Riko Ni yayi ya hadani da kirjin shi, kauda kaina nayi domin idan na kuskura muka haɗa ido tabbas akwai matsala dan idanun shi akwai wani sirri na musamman, wanda da zaran na kalle shi tabbas zan iya mika mishi kaina salin alin."Fitar min a d'akina kafin na kira wancan mik'irar gwafar."
Ɓalle botirin rigarshi yayi ya zagayo inda nake, nayi maza na koma da baya. Ina me b'ata rai cikin masifa nace.
"Karka kuskura ka tab'a ni! Wallahi Allah sai na maka rashin kunya!"Kafe Ni da ido yayi ganin nayi magana babu wasa a cikin shi.
"Zan tab'a ki. Ina son ganin rashin kunyarki" ya faɗa cikin nuna ya isa,
Takowa yayi na sauka a gadon, cikin b'acin rai nace.
"Karka tab'a ni!"
Tun karo ni yake cikin jin dadi, yana son ya tab'a ni yaga abinda zanyi.Kwalla ne suka fara zuba daga idanuna, murya na yana rawa na fara magana.
"Duk abinda kake min ka cigaba, aron lokaci Allah ya baka shi yasa kake wulakantani, ai Ni a tunanina. Ba matar ka ba kai kanka na fi karfin ka tozarta ni, Amma kana ji a gaban ka matar ka ta kirani da karuwa."Gaza karasa kalmar nayi tare da fashewa da kuka, sosai har jikina na rawa.
"Wallahi da a gaban a gaban iyayena ne babu wanda ya isa ya wulakanta ni, amma tunda nazo kaine ka tab'a ni don ranka Insha Allah bazan kuma bari..."