14

2.4K 515 29
                                    

MR AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to my Aunty Nice.

      _HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION_

    Talla! Talla!! Talla!!!

Assalamu Alaikum.

*Masoya labarin RUMASA'U naji kokenku akan ayi sauk'i ana zaman gida ba kud'i tam na amsa uzirinku dan abar dubawa ce a saka makon hakan na jenye daga 300 zuwa 200 dik mai so zai iya turo kudinsa ta 0468069082 Safiyya Haruna GT Bank. Ko mtn card ta wannan number 08132166848.*

Ina godiya da tarin k'auna masoyan asali.❤

*Pls sphere.*

Page_14
  
Shiru falon yayi,  sannan ta amshi ruwan hannun shi ta fita daga falon wuce dakin Mamie.

             Tun daga lokacin Parih ta maida hankalinta kan abinda take sai dai wani lokacin tana tab'a rigima musamman idan ta tuna gida anan ne ake yinta dan ta ringa kuka kenan.

         Abinci kuwa idan ba dumame ba bata cin komai da safe, ganin taki shiga hidimar kowa. Sai abin ya dame su dan har sun fara jin ba dad'i, suna hira a falo da Jalal ya shigo, kallon inda yake bata yi ba tace.
"Mey buroda, lemi go tu mamie rum"

      Kunshe dariya Amidud yayi tare da komawa inda ta tashi ya zauna, yana kallon yadda ta tsuke fuska yana dariya.
  
Barin falon tayi har tayi nisa tace.
"Oho dai! Mummuna wanda kowa yafi shi kyau."

Zaro ido yayi yana mamaki kafin yace.
"Yar kauyen dabji kawai"

   "Oho dai kaima can ne kauyenka! yu niba git eni bileje fas dabji"

     Mik'ewa yayi ta kara a guje.
   Duk yadda yaso daurewa sai da ya dara musamman yadda ta arta a guje.
 
    Dariya Jalal yake har da rike cikin shi, yana kallon AMIDUD yace.
"Yaya ka kyale Parih in ba haka ba zatayi ta baka ciwon kai"

        Murmushin gefen baki yayi sannan ya cigaba da kallon kwallon da ake, yi.

            +++
   Duk abinda aka sami shi rana tabbas yana zuwa, ranar talata gidan su Lamisah suka fara hidimar inda suka fara da wasu kanaun biki.

      Ranar juma'a suka yi walima baki daya, ranar Asaba aka daura auren Amiduddawlah tare da Lamisah, sai Abdul Jalal tare da Hansatu. Bikin ba laifi yayi kyau, ranar Lahadi aka yi wuni da bud'ar kai.

         Biki da sati Daya, aka bawa Parih basket takai musu abinci takaiwa Hansatu har suka yi hira da ita sannan ta dauki na gidan AMIDUD takai musu abinci tana zuwa bakin kofar taga shi da abokan shi.
       Turuss ta tsaya kafin ta karasa gurin su tana tafiya tana cin magana tana isa gurin su suna hira shi da Aashiq Ali da Aarzam tace.
"Yaya pilisi a go koros yi hedi da baskit d'in"

   Dafe goshinsa yayi goshinsa yayi cike, baki cikin sabida
Aashiq Ali da Aarzam suna tare da shi su kansu kwashewa sukayi da dariya turanci.
 
Ita kam ko a jikinta, sai ma cogewa da tayi cikin fusata yace.
"Zaki wuce ko sai na balla"

"Pilisi gibi mi rodi zan wuce"
Nace mishi, tsawa ya buga min sannan yace
"ee Get out banziya kawai ansaki turancin dole ne"

Murguda baki na nayi sannan nace.
"Nu bodi fafet"

     
   Dariya suka saka tare da rike cikin su Aashiq Ali yace.
"Ya Salam no body perfect"
Gyad'a kai nayi ina murmusa mishi,
   Rike haɓɓa nayi sannan nace.

Bat wai kuke  foon fou mi"
Rike baki Aarzam yayi, na kuma cewa.
"Bi kos i sifiki ingilise beri wey"
A fusace Ya Amidud ya Mike yayo kaina.
          Ana na watsar da abincin na shiga gidan ina hali, kallona Mamie tayi tace.
"Yau ma kun kuma raba halin ba?!"
   Tura baki na nayi sannan nace.
"Tunda akayi bikin shi yake jin haushi na sauka ce nice nasa shi auren tabarya da zanin"

    "Kul! Kar na kuma jin haka dan yayanku ne, jibi ma zasu tafi ku huta da masifar shi"

         Shigowa yayi muna kitchen dukkan mu muna taya su aiki tunda su Fahhamah sun koma makaranta. Hararar ta yayi sannan yace.
"Mamie ki jawa Mahaukaciyar Nan kunne taje gaban abokaina sai tsinkani take"

   Dariya nayi sannan nace.
"Wai sauka lafiya ruwa eat monki"
   Sake baki suka yi suna kallona, make keyata Mamie tayi tace.
"Ke kam Allah ya shirya ki"

      "Amin" nace tare da fashewa da dariya sannan na fita.

Ana gobe zasu tafi shine Maman Nibra suka zo, inda suka haɗu a d'akin mu ina sallah suna hirar su naji matar dan kwallon tana cewa.
  "Allah Sabriyah na kasa sabawa da Sex kullum abun kamar sabo nake ji shi yasa da zaran yazo min nake cewa bani da lafiya, shine yake cewa min idan nayi hakuri Mrs AMIDUDDAWLAH tana nan zuwa dan haka na daina mishi yanga da abinda yana dab da mallakar wani nan kusa lokaci yake jira, Sabriyah ina jin tsoron kar ya samu wacce zata fini juriya da hakuri ya manta da Ni da duniyata don Allah Kiyi wani abu kinji"

    Shiru Maman Nibras tayi sannan tace.
"Ai kuwa hakuri zaki yi kina shan fruit,  sannan kina kula da kan ki tunda kinga Allah yayi shi fitinanen ne a sex"

    Dama can nayi Sallama ina nad'e maganar sune kawai Sannan na ficce daga dakin na nufi dakin Mamie inda suke zaune nace.
"Mamie meye ne Ses?!"
"Ses?!! Kuma"
Watsa hannu nayi nace.
"Yanzun matar wancan take gayawa Maman Nibras wai yana hanata barci da ses kullum da."

  Dauke wuta suka yi baki daya an rasa me magana. Sai shine ya daka min tsawa.
"Ke dalla fita ki bamu guri, Sokuwa wawuya kawai."
Da sauri na fita daga d'akin ina tura baki, karshe dan kunya fita yayi Mamie bata sallame shi ba, yaje har dakin mu ya kira matar sa suka tafi daga nan ban san ya suka kare ba, Ni dai Mamie tayi min fada tace wai abinda na faɗa kisa yake dan haka koda wasa kar na kuma fa cike da tsoro na gyad'a kaina.
      
         +++
Ranar da zai tafi ina makaranta, duk sun rigani dawowa, Ni haka kawai dan bakin ciki ya sani a lesson. Koda na dawo nasamu ya tafi da matar shi  murna a cikina kamar zan yi me gida ya rage daga Ni sai mu sauran yan gidan yanzun kuwa shiri muke da Jalal har da Hansatu.

       💁🏻‍♂️ Hmmmm idan naga Voter zan iya kaiku har page na 20 idan kuma ban gani ba, Insha Allah Jumma'a na ajiye rubutun sai Bayan sallah Insha Allah....
https://my.w.tt/QRdLU7uaI5

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now