Page-8

2.6K 417 20
                                    

MR AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to Aunty Nice.

   _Fatan Alkhairin gareki Hafsah Abubakar Mu Sosai Sarkin kishi🤪😜😂 Keda Parih_

    
Page_8
Riƙe baki Bana talatu tayi tana mamakin Parih, tab'e baki tayi cikin masifa tace.
"Yar banza Y'a me shegen fitinar tsiya daga zuwa ta dami kowa da surutun bala'i."

     "Hmm! Baba talatu ai mako me sauki ne saura kiris ta yanke min shan ruwana a gidan nan."

  Zaro ido Baba talatu tayi cikin garaje tsce.
"Ke yar nan garin ƙaƙa?!"

  "Dan naje gyarawa Jalal dakin shi da"

    Kura mata ido baba talatu tayi sannan tace.
"Anya hansatu! Kuma ba tayar baya bace."

    Shiru hansatu tayi, kafin Bana talatu tai magana. Suka jiyo muryanta.
"Ke tulaliya bani hanya kin wani tokare kofa kamar giwa! Sai tarin tsokoki! Yawwa me abinci, gulmata takawo miki ko?"

     "A'ah Fara!
       Zaro ido tayi ta kalli gefe da gefenta, ta ga abubuwa abinda ya duba aikuwa ta fasa ihun tana buga kafarta a a kasa.
  
Da sauri Alhaji Muhmood ya shigo shida Hajiya Adawiyah suna tambayar su.
"Lafiya!"
   Cak tayi shiru kamar wani abu bai faru ba, tace.
"Ku Tayani duba kafad'ana akwai inda fufuke yake dan nima ina son gwada tashi sama ne"🙄

    Ta ware idanu akansu tana jarin me zasu ce.
"Waya ce miki mutum yana da fukafukai"
   Juyawa tayi irin ta fuskar nan ta kalli Baba talatu, ta kwad'a mata harara sannan tace.
"Baga me abinci ta kirani da Fara ba."

       Girgiza kai Alhaji Muhmood yayi sannan ya bar kitchen ɗin, Hajiya Adawiyah ta kalli Baba talatu tace.
"Sunanta Jal Parih"

Cab'e zance tayi da cewa.
"A'ah Jan Parih dai ko"
    Dafe goshinta Hajiya Adawiyah tayi sannan tace.
"Toh naji! Baba talatu kindai ji sunanta."
  Kafin ta rufe baki Parih ta fice daga kitchen ɗin ta nufi inda ta ajiye tukunyar tuwon ta, a Tsakiyar center table ɗin falon, ta hau ta zauna tare da lankwasa kafarta, tana cin abincin.

                  "Parih! Sauka kici abincin a kasa mana ai nan an ajiye shine ɗan kwalliyar falon."

           Kamar zata yi kuka tace.
"Wallahi da kinsan daɗin da nake ji na danne sama ina cin abinci sai kin jinjina min! Kin ma tab'a cin abincin a samar nan?!"

   
             Girgiza kai tayi tace.
"Toh aini dake ba d'aya bane, ke karama ce Ni kuma babba ce kinga ina hawa fashewa zai yi ke kuma babu abinda zai same ki."

    Ware idanu tayi waje tace.
"Ince ba a mutuwa dai!"

    Itama ware mata idanu tayi sannan tace.
"Mutuwa kai! Ai mutuwa ma d'aya kika ji, kana faduwa akai sai mutuwa ko shurawa baka yi."

  Kafin ta idar da maganar tuni Parih tayi masauki a kasa tana raba idanunta.
        "Hajiya!"
"Mamie dai! Kamar yadda yan uwanki suke kirana"

Gyad'a kai tayi sannan tace.
"Mamie!"
     Kura mata ido Hajiya Adawiyah tayi musamman yadda takira sunan mamien,

"Ina jinki"
          "Tunda na sauka ince bani mutuwa"
"Parih kowani mutum da kike gani dole ya mutu dan ita muke jira! Koda ciwo ko ba ciwo idan ajali tayi kira dole kaje"

"Toh Ni dai lokaci na bayi ba, dan sai na tsufa."

    "Toh Parih ai babu wanda zai so ki mutu baki tsofa ba."
    Haka tayi ta jefawa Hajiya Adawiyah tambaya ita kuma tana gaya mata abinda ta sani.

        ****
   "Lamisah! Ina kike kai jama'a a haka kike tunanin wancan miskilin zai karbi aurinki da shegen nawarki nan ki fito"

      Sanye take da doguwar riga ruwan hanta, sai farin gyalen da ta yane kanta, tayi kyau ba laifi a hankali take takawa har inda Mamarta take, tana murmushi. U
"Ummi kiyi hakuri"

    "Muje kina b'ata mana lokaci."
Fitowa tayi suna jera tana tambayar Uwar.
"Ummi ina zamu"

   "Gidan Alhaji Muhmood! Kisan Amiduddawlah ya kusan dawowa! Kuma ina son naje na daina  Hajiya Adawiyah."

Shiru tayi sannan tace.
"Ummi dole ne sai dani zamu je?"
"Ke bani ciki da rashin hankali idan bazaki ba koma sakarya kawai."
    Haka suka shiga motar tana sababi, har suka kusan isowa gidan.

        ..... Tunda suka iso ake shirya musu gabansu Lamisah sai sunkuyar da kai take, Uwar kuwa ta zauna sai gyata karya take.
"Ai Hajiya! Da kyar ta biyo Ni wai kunya take ji."

   "Karya ne! Wannan me idanun kamar ta budurwa kare, sam bata kama da me jin kunya ba, yadda take kallon namar kazar gabanta"

      Dukkan su suka d'ago kai suna kallon Parih, wacce ta jagalgala fuskarta da Eyeshadow.

        "Parih bana hanaki shiga maganar manya ba"

    Sunkuyar da kai tayi cikin karamar murya tace.
"Kuyi hakuri bani kumawa Amma Mamie Alkur'an batai kama da wanda take jin kunyar ki ba, wai ma tukun su din suwaye? Ita din wacece da take jin Kunyarki?"
   
    Jan hannunta Buhayyah tayi suka koma dakinsu, Inda tabar Amrozia tana fushi ta farfasa mata Eyeshadow ɗinta, Buhayyah tace.
"Ke itace zata auri Ya AMIDUD"

    "Kutt! Wannan me kana da muciya da zanin ce, zata yi aure i dai haka ne toh lallai noma sai an daura min aure"😏😒

    "Ke lafiyarki Parih! Ina ke ina aure idan Mamie taji zata fasa miki baki."

      Murguda bakin tayi sannan tace.
"Allah da gaske nake sai an daura auren dani."
   Duk yadda Buhayyah da Amrozia suka so hanata fita haka tafito, ta tsaya musu tsagege tace.
"Mamie! Nima aure zaku min"
  Dafe goshin Mamie tayi, sannan ta daka mata tsawa.
"Fita ko na zaneki yar nima fitinanniya kawai."

   Amadadin ta shige cikin gida waje tafita da gudu, ta shige jikin flower tana kuka.
           Zama tayi a gurin tayi ta kuka.
  Bayan fitar ta Hajiya Adawiyah ta kalli Mahaifiyar Lamisah tace.
"Kuyi hakuri! Daga kauye aka kawo mana ita, ina ga zaki tuna da mahaifinta, Abtisham."

   "Haba ina ta kallon fuskarta ashe Yarmu ce! Kamar tayi yawa, Allah sarki Allah jikan iyayenta, Ai zaman kauye shi ya maida ita haka."

     "Eh wallahi gata nan tunda yazo sai hana mana Gwari take"
   
Haka suka hira har aka fara kira sallah, sannan suka tashi zasu shiga dakin Hajiya Adawiyah, Mahaifiyar Lamisah tayi ita kuma Lamisah ta shige dakin Aunty Amarya!

            ...... Tun hudu da Parih ta fita take kuka bata daina ba, karshe fitowa tayi daga cikin flower ta zauna, a inda Alhaji Muhmood yake parking, ta zauna tana kuka motar shi, na shigowa gidan kuka ta kara har ya iso yayi parking, kuka take.

  Da sauri ya fito yazo inda take, yace.
"Parihna! Waye ya tab'aki"

    "Baffana! Aure za'a min, wai nace a min Shine Mamie tayi min fada"
     
    Dariya ta bashi, girgiza kai yayi sannan ya riko hannunta yayi yana murmushi har suka isa bata daina kuka ba.
 
Suna shiga falon da Sallama ya nemi guri ya zauna, Aunty Amarya ce ta fara fitowa, tana fitowa taga yadda Parih take shashekar kuka.

         Karban jakar shi tayi tare da mishi Barka da zuwa, can sai ga Mamie ta fito, nan taga Parih tana kuka. Nan take tambayar ta lafiya dan har ta manta abinda ya faru, sai da ya labarta mata abinda ya faru, nan taruka baki tana dariya sannan tace.
"Toh waye mijin da za'a daura miki aure dashi"

   Watsa hannun ta tayi sannan tace.
"Toh Ni koma waye ina ruwana ni dai aura  min kowa ma!"

   Dariya ta basu sannan Alhaji Muhmood yace.
"Shi kenan zan aurar dake haka yayi miki amma kuma zaki yi karatu yadda zaki ji dad'in auren."

     "Yoh wani karatu, ai kome ma Zanyi amma Baffana ince ka kai aure"

     "Har kin wucce ma"

Tsalle ta buga tace.
"Yawwa dole ma na nunawa Aaraih Ni ba sa'arta bace"

      _🙄😛😜Voter yayi kasa zan tafi hutu Alkur'an_

Oum-Muwaddah
  

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now