23

2.5K 544 45
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to my Aunty Nice😊

_Barka da Allah. Yan uwa musulmai! Ubangiji na kawo mana karshen annobar kobid19🤣😂 Mun dawo Akafta Allah ya maimaita mana🏃😎😘😍🤩_

23.
Ai kuwa na fecce a saba'in ko kyalina baka gani.
"Parih!!!"
     Buhayyah ta kwala min kira, kan Uba tuni na cikawa bujena iska.
    Mik'ewa yayi jikin shi na tsuma, dan yasan sarai zamu iya haɗuwa da Jalal.
              Ai da sauri ya fice Lamisah tana ce mishi.
"Honey! Ina zaka dan ance maka gantalalliyar can tafita..."

    Ai shima ko ta kanta bai bi ba, kallon Sabriyah tayi ƙamar zata fashe da kuka, tace.
"Kin gani ko! Kamar ba matar shi ba, haka yake muzanta min."

    "Hmm! Nayi mamakin da Mamie tace min zaku tafi da aljanar can! Amma ba damuwa kici Ubanta idan tayi miki Iskanci tunda fita zai nayi ya barku a gidan."

     ......  Haka suka yita zagina,

    Cikin ikon Allah na samu na shige gidan garin shiga muka yi karo da wani wanda ban san waye ba, kuma ba Jalal ba.

   Ware idanu nayi cikin jin haushi nace.
"Ji min mutum ka bangaje ni kuma baka bani hakuri ba."
Na tura mishi bakina.

      "Ai bangaje ki nayi ko?"
Ya tambaye ni,
Cikin gatsali nace.
"Hawa kaina kayi! Luk i No go fi tak nunsent, abeg give mi road meka fass!"

     Dafe goshi Buhayyah tayi, cikin jin ba dad'i tace.
"Kaicona! Ke kam! Da alamun ana asarar kudin tara ne! Wannan jakin turancin baki ya ishe mutum zuwa lahira da kafar shi ba sai an kai shi ba, ai ga Ya AMIDUD. Don Allah Ya Najmuddawlah kayi hakuri!"

Ware ido nayi cikin dariya na nuna shi nace.
"Kai Amma wannan sunar taka da tsayin jaraba! Kai harufa nawa kenan! Kuttt."

Juyawar da zanyi aikuwa sai A kan fuskar Ya AMIDUD.
Ban san lokacin da na bazama a guje ba nayi cikin gida, shima ya rufa min baya.
"Wayyo Allah na! Na shigangadina Wayyo Allah na! Mamie ki cece Ni wallahi zagina suke"

Jin irin ihun da nake, yasa Mamie tafito da sauri. Bayanta naje na buya ina haki.

        Leken shi nayi, shi ko halin bayayi amma dan niman magana nace mishi.
" Jimana dan kwallon! Shi kai baka hali ne? Yoh ina kaci ka koshi balle ka tara tsokokin Alqur'anin ko yar kumatai nan baka dasu! Wai tsaya kana nufin tun."
    "Keyi min shiru bani son shashanci, wuce kibi shi." Inji Mamie,
      Rau-rau nayi da idanuna, nace.
"Mamie nasa an kawo miki abinci ko iri. Afirishetin baki min ba na abincin yana dadi ko baya dad'i"

Kallon Buhayyah tayi sannan ta kalli Ya Amidud tace.
"Ban fahimci me take cewa ba! Kuna nufin abincin Parih ne bata Lamisah ba?"

      "Kutt! Inji wani munahikin ne yace bani ke girkawa ba, ita wancan tabaryan da zanin me ta sani banda Ni na girka kuma su hadu su cinye. Sannan su kirani da karuwa Alqur'an bani komawa gidan can"

      Shafa gashin kan shi yayi cikin damuwa, tare da narke fuskar shi wa Mamie yace.
"Kiyi hakuri! Mamie amma"

    "Wuce ka bar min gida ke kuma wuce daki."

            Zaro Ido yayi waje, kamar zasu fado kasa, girgiza kai yayi sannan yace.
"Amma Mamie baki tunanin cikin dare wancan Yaron zai kuma biyota, tunda haka ne shi kenan. Tayi zamanta sai da safe"

      Ya juya zai fita kallona yayi na murguda mishi baki, bai kula Ni ba yayi tafiyar shi, har ya kusan isa Palourn mamie tace.
"Zoka tafi da ita! Ku dai ji tsoron Allah a zaman da zaku yi karka manta amanarka ce ita."

     "Wayyo Allah na! Wallahi bani binshi kofa da takashi, Alqur'an wahala suke bani, Wayyo Allah Baffana." Na riketa gam.

   Zuwa yayi ya riko hannuna ya fitar dani daga gidan, aikuwa na fara mishi, bori ina botsarewa.

    Cikin rashin sani hannun shi ya kai kan kirjina, aikuwa ya tab'o biredi mai laushi.
"Wayyo Allah na! Ka tab'a min nan dina!"

Da sauri ya d'aga hannun shi yana me jin kunyar kallona, haka muka isa gidan. Tulatulan mata sun saka abinci a gaba, suna ci.

Wucewa yayi dani dakina, ya ture Ni. Sannan ya fita abinshi,
   Hannun da ya tab'a burodina yake ta kumshe shi, cike da jin wani irin abu a jikin shi. Kallon Lamisah yayi cikin nutsuwa. Sam bai tab'a lura da yanayinta ba sai da yau ya tab'o gidan laushi. Zama yayi yaki amfani da hannun wani irin kunya da yarrr yake ji.
    (Lolz! Ya Amidud an tab'o kayan laushi mana 🤣😎)

          Ban san ya suka kare ba, amma na daina jin motsin su a falon.
    Washi gari, kin fitowa nayi na gyara kwanciyata, dake banci komai ba jiya na kwanta, yunwa kuwa ta shiga cin ubana, dole na tashi na shiga wanka ina fitowa naga tara na safe, tsaki nayi sannan na fito kitchen daga Ni sai towel dan ban zata sun tashi ba, dake nayi wankar har na wanke kaina.

     Da sauri na shiga kitchen ɗin, naje na hada tea kenan, nafito aikuwa muka yi karo da mutum, tsoro ne yasa kofin hannuna faduwa.
  Naja da baya ina raba idanuna, kallona yayi daga sama har kasa, ga ruwa na diga akan shi, Yasaka towel a wuya. Nima kuma gashina a jiye, a dalilin karin da muka yi ya kai hannun shi k'ugu na, ya rike Ni. Nima tsoron kar na fadi na saka hannu na biyu na riko towel ɗin wuyar shi.

    Wannan tsayuwar da muka yi, ashe akan idanun ja'irar matar shi. Ai kuwa ta sake wata ƙatuwar salati.
    Wanda ya saka ya AMIDUD ya sake da ƙasa. Cike da jin haushi nace.
"Wayyo Allah na! Yu bireki mey k'ugus!  Yi wanto kili mi, ko? Bikos yu hiti min! Filis tak mi bak two Mamie, i kan't tak dis ani mo!"

      Kura min ido yayi cikin baƙin ciki, wato shekaru hudu bai sanya na nutsu nayi karatu ba, sai wani azzalumi turancin da nake zane shi da ita.

      Matar shi ta dawo dashi daga duniyar da ya tafi na takaicin da na kulla mishi. Yo ko a jikina an tsakuri kakkausa.

   "Honey! Meye zan gani? Ba dai wani abu bane Yarinyar nan ta maka ba?!"

     Kutt nice ma zanwa mijinta wani abu.

     Mik'ewa nayi ina rike k'ugu na, daukar kofina nayi naje na zaga bayanta, kasa kasa nace mata.

    "Wasan kwarzo muka gama dashi, kuma ya tab'a ni sosai kema kice yayi miki irin abinda yayi min in ba haka ba, wallahi yasha dake. Mijinki ya iya wasan kwarzo."

"Zanci Kutumar Ubanki!"
Ta ruga min Ashariya!.

Juyawa nayi naga ya dafe goshinsa, cikin kankanuwar murya nace.
"Ayya! Anti kyakyawa zagi bakyau! Idan ka zagi iyayen su naka ne ka zaga, kuma Ni bazan so na ganki a cikin jahannama kina miko min hannu ba, kin ga ki daina. Ba kyau Ya AMIDUD ma bai ji dadin ba  kin zagi kawun shi,"

    Nasan yaji mu, sake narke muryan nayi nace.
"Kuma iyayena ne fa, suna can a makwancinsu kika zage su. Ba damuwa! God dey se ebiritin."

  
"Ke!"
   Ya buga min tsawa, a firgice na juya. Sannan nace.
"Auuu! Wacce tayi zagi baka fasa mata janareton kunnenta ba sai Ni yar mareniyar Allah bani da Fada da modah shine kake son bireki mai kunne wai Ya Amidud woh yor on i kili, kayi hitin dina haka?!"

       🤣🤣🤣👌🏻 WHO your on i kill! Kunsan bamu da ilmin English! Ya Allah ka albarkaci Rayuwar mu da iliman nafi'a!

Karku manta kuyi min vote Bahaushiya! Free book ne! Ga Rayuwar Yan matan Arewa

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now