MRS AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
https://my.w.tt/XGvckkY6N6
Dedicated to my Aunty Nice😊
ʜᴀᴢᴀᴋᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏ.....
Los regalos🎁
48.Sam idanun shi ya rufe shi ya rufe kawai burin shi ya hukunta ni, abisa laifina.
Ga baki daya dauke wuta nayi ban san halin da ke ciki ba, sai da yayi juye bakin, sannan ya ga bana dogon motsi.Kamar mahaukaci haka ya koma yana kwalla min kira, tare da jijjigani..
Amma nayi nisan kiwo, d'ago ni yayi tare da rungume ni a kirjinshi yana sauke wani irin hawaye me zafi, d'ago ni yayi yaga kaina yayi baya
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Tashi ki rufa min asiri. Bani da wacce tafi ki. Don Allah tashi ina matuƙar sonki! Tashi Matata! Tashi Uwargidana! Tashi Mrs AMIDUDDAWLAH! Wayyo Allah na nayi abinda ya dame Ni" kayan shi ta kwasa ya saka, sannan ya koma ciki da sauri ya ciro min doguwar rigar na, yazo ya saka min, sannan ya dauke ni.Zuwa asibiti, ko kafin mu isa jini ya ɓalle min, hankalin shi yayi mugun tashi dan ji yaƙe kamar zai zauce.
Da sauri aka amshi ni, zuwa dakin ICU, cikin gaggawa aka shiga ƙoƙarin rike dan karamin cikin da bai wuce sati biyu zuwa uku ba.
Kamar zai yi hauka lokacin da aka ce mishi cikin ya zube, sabida wahalar da nasha da yake s**x dani.
Gaza hakuri yayi yaje inda wayar Asibitin yake, ya shigar da number Mamie! Ya kirata.
Tana d'auka ya sauke wata irin shasheka yace.
"Mamie! Na zubda cikin da ban san dashi ba! Mamie ya zanyi da Pharisa, idan ta san cikinta na zubda. Mamie ya zanyi da Pharisa."" Ka dawo min da ita?! Ko kuma ni nazo da kaina! Idan ta farka cikin kwana biyu kacal nake son ganinka Pharih."
Hawaye ne yake bin fuskar shi, cikin tashin hankali. Tabbas yayi kuskure. Tunda ai sai da tace mishi ya hakura ta gama makaranta amma yaki ji, sannan sai da ta gaya mishi Pharih bata gama hankali ba yabar ta, ta kara nutsuwa yace a'a toh gashi nan zai yi two ziro.
Dakyar ya lallaba kan shi zuwa dakin da aka fidda ni nayi fayau, sai uwar karan hanci.
Sai fadawar da nayi, zuwa yayi ya zauna a kusadani tare da rike hannuna, ya saka akan bakin shi.
Haka ya zauna a jikina lokacin sallah ne ke fidda shi. Bai kuma shiga tashin hankali ba, sai da yaga nafi awa biyar ban farka ba, nan ne yaje ya sami wannan likitan ya kira wannan nurse din, Suma ƙamar sun San da abinda yayi min suka ki tsayuwa mishi a kaina.
Sai da yayi wujiga wugija, sannan suka zo kaina aka saka min abin shaƙar numfashi.
Bani na farka ba sai karfe biyu na dare, da kuka na tashi. Ina bude ido na, nayi tozali da shi, da sauri na rufe idanuna.
Na birkice mishi sai da aka mi alluran barci.
---
Lamisah da Sabriyah babu wacce ta damu da ina nan bana nan hidimar gaban su suke kawai, gidan yayi kaca-kaca a kwana ɗaya, haka basu ganshi ba sai suka tattara mu xuka zuba mu a gefe, suka ta hidimar su. Duniya sabuwa......
Ni kam ban kuma farkawa ba sai da safe shima ciwon cikine ya taddani suka min allura, tare da babu wani magani. Suka ce mishi yayi ta lallabani, domin ina cikin tashin hankali.Duk zuwa lokacin ban san meke damuna ba, sai da yazo ya rike hannuna na juya mishi kai, ina share kwalla.
"Me ya faru dani?! Me ya kawo ni asibiti?!""Kiyi hakuri! Kinyi bari ne! Munyi rashin babyn mu!"
Ji nayi kamar ya soka min mashi a kirji na, ban san lokacin da na juya na kalle shi ba, nace.
"After you rape me! Now my lovely child! Cikin da ban san dashi ba ka kifar min da jinina! Ya AMIDUD wallahi na tsaneka fiye da kome a duniyar nan, kayi zina dani! Bai isheka ba. Now abortion, Ya AMIDUDDAWLAH! Idan rayuwa da kai guba ce! Toh nisantar ka itace, kaucewa ga fadawa guba, idan Sonka cuta ne! Ya AMIDUD gwara na mutu ka huta da son da kake ikirarin, Haba Ya Amidud meye nayi maka kake wulakantani son ranka ba, ita matar ka da baka son tasan halin da muke ciki."Zuwa yayi zai zauna kusadani nace.
"Wallahi zan bar asibitin idan ka zauna. Ni bazan maka Allah ya isa b'ata min rayuwa da kayi ba, amma Allah na ganin mu! Kuma shi yasan irin hukuncin da zai mana! Tunda munyi tarayya a sabon shi."Duk yadda yaso yayi min bayani yaki sauraron shi, karshe nace ta fitar min a daki, tunda haka ya zaba ya barni na huta ni.
Kamar zai yi hauka haka ya koma, dan ko da aka sallame ni, muna komawa gidan da ya ajiye Ni nace bana son ya Mai dani asalin inda ya dauko ni.
Haka ya dawo dani gidan shi wanda muka samu kamar babu halittun mata a gidan, d'akina na shige, yana rike da kayana, a hankali nake tafiya dan har yanzu. Jiri bai barni ba.
Ina shiga na kwanta, tare da lumshe idanuna, hawaye na zuba daga cikin su.
Ajiye kayan yayi. Bai saurari tambayar da suke mishi ba, ya haura sama, sai gashi ya shigo d'akina.
Rufe kofar yayi, haurawa gadon yayi.
"Love! Ke matata ce da!"Wani irin kallo na bishi da ita.
"Ai akuya bata da izzar da zata saka fatar kura ta razanani ba, Don Allah ka barni da jirgin da ya dame ni ko kuma na bar maka gidan ka! Ka gama yaudara na, yanzun kuma ka dawo da batun kana aurena, Dan wasa kenan! Ka buga kwallo a can a gidan ka, ma ka buga mana wani kwallon"Ka fita ko na fita.
Haka nace mishi.. cikin sanyin jiki ya fita, amma hankalin shi a tashe.
Yana fita Lamisah ta kawo mishi wani bill na zata kasuwa, da ya buga mata tsawa, sai da ta manne a garu.......Alqur'an ta kare maka Ya Amidud 🤔
🤣
Ashe haka kuke son MRS AMIDUDDAWLAH!?Ikon Allah! Koda yake akwai masoyan Bogi! Akwai masoyan da suka yi sadaukarwa sayan Mrs AMIDUDDAWLAH!
Kone kuka sani Typing yau🌺🤩😍....
Hmmm...... Allah domin ganin Wani post da wuri ku zuba Vote dan Alqur'an Vote dinku na rena shi yasa nayi Bahaushiyah abuna........
Domin samun shiga Bahaushiyah paid group..
08130269641....Wasu suna min magana akan na sanya su a group na Bahaushiyah!
Book din na kuɗi ne!😘😘