31

2.7K 571 60
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

https://my.w.tt/XGvckkY6N6

Dedicated to my Aunty Nice😊




     اللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ

  _Wannan na kune Masoyan Parih da Turancinta!🤭_

31
Murmushin mugunta Lamisah ta sake domin ta gama tsara yadda zata ci uba na saukake.

    Lokaci guda muka sauke murmushi, kallon juna muka yi da ita na kuwa mata gwalo, ana haka sai ga wata ƙatuwar mata tazo inda Lamisa take ta zauna, murmushi nayi na mike. Gurin matan naje ta baya na san yadda na ajiye mata kadangare a kafad'arta sannan na bar gurin ina da buri akan Lamisah so nake taji jiki kafin mu bar garin.

     Komawa nayi inda nake zaune. Na cigaba da zubawa matar ido, can na kalleta cikin tsoro na nuna mata kafad'arta.

       Girgiza min kai tayi, alamar meye.
Nuna mata kafad'arta nayi cikin tsoro, waigawa tayi  ta kalla. Wani uban tsalle ta buga tare da fadin.
       "Oh My God!"
Bata dire ko ina ba sai kan Lamisah tana birgima. Ganin mutane sun fara kokarin zuwa gurinsu nayi maza naje inda suke na dauke kadangare na, na saka a jaka.

Ina daga ido sai a na Ya AMIDUD yaga dai nasaka abu a jakar amma dake yana ta matar shi bai damu da sanin me na cusa a jakana ba.
  
Dakyar aka ciro Tuleliya akan yar miciciyar matar AMIDUD. Tayi laushi yar nima, na kuma koma na zauna ina dariya kasa kasa.
               Kuma aka nime kadangare ba a gani ba, kamar bani gurin. Kallon zargi ya AMIDUD yake min Ni dai ban ce mishi komai ba.

     Muna zaune har jirgin mu ya tashi, bai fasa bina da ido ba.
  Dan yana da yakinin nice na musu wannan abin.

         .......
Alhamdulillah! Mun isa garin Madrid lafiya, inda wasu daga cikin abokan shi suka zo daukar shi da motar club ɗin su.

     Tunda muka fito wani daga cikin abokan yake bina da ido. Kauda kai nayi dan ban son irin wannan kallon cire addini.

        "Dabji! Barka da zuwa ya hanya?" Inji wani dan afirka irinmu duk sauran masu jajjayen kunne ne.

        "Alhamdulillah! Abdudin mun same ku lafiya."

       "Masha Allah! Lafiya lau, sai godiya." Ya fada yana tsare ni da idanun.

          Har muka shiga motar bai fasa kallona ba, komawa kusada ya Amidud nayi na laffe a jikin shi, ina sauke numfashi.
  "Mtseew!" Lamisah tana tsaki,

   Kallonta Ya AMIDUD yayi dan ya tsani yadda yake nunawa bata yin abokan shi, dan basu taɓa zuwa gidan shi sun ci abinci ba, kuma shi mutum ne da yake son wannan al'adar.

     Katse mishi tunanin shi Abdudin yayi ta hanyar cewa.
"Dabji! Filin ƙwallo yayi kewar ka. Dan haka muna isa zamu fita da kai."

  Lumshe idanun shi yayi cikin gajiya da son hutawa kuma ba komai ya haifar mishi da gajiyar ba, sai saukar numfashina da yake ji a gefen hannun shi.

                  A hankali ya janye ni daga jikin shi, yace.
"Nifa bazan fita ba!"

   "Toh amma kasan dai!"
     "Wallahi ko kofar gidana bani fita. Insha Allah gobe zan yi sammakon."

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now