20

2.4K 343 26
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to my Aunty Nice

     *_🌹Shi  daukaka tamkar rigar aroce ta kan barka a lokacin da taso ko da kai baka shirya barinta ba.😊_*

Page_20

Kuka nake son nayi sabida tsananin tsoro yasani sake fitsari a jikina, ga uban rawan da nake Ni bana sanyi ba, A'a na bala'in tsoron Ya Amiduddawlah, wanda yake shake da bakina, yana kallon cikin idanuna. Yana ganin Jalal ya wuce.

"Lallai kin rika! Kice labarin da ake bani ba karya bane da gaske ne! Kin zama karamar karuwa! Shine bari ki lalata mana sunan gidan, wallahi kin cuci iyayena! Wallahi nayi da nasanin da Uncle Abtisham da Aunty Amatul Islam  suka haife ki,tir da halinki kazamar yar iska mara kunya."

      Shiru nayi sabida ban isa na mishi rashin kunya ba, haka Jalal ya gama sintirin shi bai ganni ba yaja motar shi ya koma,  ture Ni yayi sannan ya  tsinka min Mari har uku, kuma ya hanani kuka, cire rigar jikin shi yayi sannan ya wurga min yace.
"Wannan rigar ko da kudi aka hada Ni dashi bani kuma sakawa! Haka wacce babu komai akanta sai tsageranci."

    Kuka nake sosai saboda irin zagin da yake min bazan iya dauka ba, wucewa yayi na bi bayan shi.  Motar shi ya buɗe sabuwar dana gani yau, ya tab'a wani guri boot ya buɗe, sannan ya nuna min Boot din yace.
"Allah yayi min tsari na dauki karuwa a cikin motata, sai dai ki shiga bayan motar"

   Kallon shi nayi wasu kwalla masu zafi suka sauko min.
"Ya Amidud don Allah ka barni na shiga cikin motar sit mana."

       kiciniyar cire belt din shi yake nayi saurin shigewa cikin Boot din na kwanta tare da fashewa da kuka, yana zuwa dan mugunta ya buga motar da mugun karfi, sannan ya koma yaja motar da mugun gudu, dan rashin Imani haka yayi ta gudun ganganci, har ya isa gidan sannan yaje yayi parking.

     Yana fita ya nufi gurin Baba me gadi, ya mika mishi hannu sannan yace.
"Nagode 🤝 sosai, baba ka rike amanar da na baka sannan ka nuna kai dattijon Kwarai ne, Allah ya fadawa zuri'arka."

"Ba komai ai yiwa kaine! Gashi kuɗin da yake bani tsawon shekara guda ban tab'a ci ba, sabida mahaifinka bai rage Ni da komai ba"

    "A'ah kabar shi hakkinka ne Allah ya cire maka a jikin shi, kaci abinka nagode!"

  "Ba komai! Alhaji karami, ina mutuniyar take?!"

    Nuna mishi bayan mota yayi sannan suka iso, ya buɗe Ni.

       Tsili tsili nayi da idanuna, riko kunne na yayi sannan ya fidda Ni daga cikin boot d'in muka nufi, cikin gidan shi yana magana kasa kasa, muna shiga falon shi ya tunkude Ni, faduwa nayi na fashe da kuka, har ya juya zai nufi dakin shi. Sai yaji ina ai ina cikin jin dadi ne tunda ga fanka Nan na juyawa, dauka na yayi ya kaini kitchen ɗin su ya wullani sannan ya rufe da key yayi tafiyar shi.

          Washi gari da asuba ban san shigowar shi ba, sai da naji ya watsa min ruwan sanyi tare da cewa.
"Maza ki nufi cikin gida, ki duba store kizo kiyi mana abin karyawa ko na miki dukar tsiya wallahi babu wanda ya isa ya min magana! Karuwa kawai."

         Kamar maciji haka nazo na wuce shi, na nufi cikin gidan na kwaso duk abinda yace.
"Tsayawa nayi ina kuka! Dan ban san me zan dafa musu ba, kuma sun koma barci"

Tattara kayan nayi na zuba a tunkuyar nayi tafiyata, cikin gida dakin Mamie na wuce dan tana sama gurin daddy, sannan nayi kwanciyata bayan nacire kayan jikina, na daura towel nayi kwanciyata.

         Barcin da banyi jita cikin salama ba itace nake yinta yau, sosai na sake nake barci.

     ...... Ashe Jalal ya ganni, kawai ina ciki da Barci yazo ida nufin shi, lokacin kuma Ya AMIDUD yazo tafiya dani. A ka'idar gidan wacce take da miji ba ita ke girki ba sai abokiyar zamanta, dan haka ganin Mamie tana sama, kawai Jalal ya burma dakin Mamie sabida ya leka d'akina  bana ciki, shine bari yazo yayi watandar shi son ran shi.

              Sai gashi akan idanun Ya AMIDUD, shima leka d'akina yayi yaga bani ciki, a masifance ya nufi dakin Mamie, inda ya sami Jalal ɗin yana kokarin janye  towel daga jikina, rike hannunsa Ya AMIDUD yayi sai da yaji kashin hannun yayi kara, sannan ya kifa mishi mari wanda ya sashi sake ihun, da ya farka dani.

      A tsorace na tashi zan zauna yayi wani kwallo da Jalal, sai da ya isa bakin kofa, cikin hargagi yace.
"Wallahi kika sake na dawo kanki baki suturta kanki ba, sai na miki abinda bazaki manta dani ba"

      Da sauri na sauka a gadon na wucce ban daki na saka key jikina na rawa, sosai dambe ya kacame a tsakanin Jalal da Ya AMIDUD, na rasa me zanyi rigar Buhayyah da na gani a nan dakin Mamie na saka na fito, lokacin Aunty Amarya, tana ƙoƙarin rabasu, sai dukar Jalal yake, yana fad'in.
"Duk lalata mata rayuwa da kayi bai isheka ba! Amma kana gani akan idanun ka akayi komai dan bakin masifa kana cigaba da bibiyarta! Dan abu kazanka wawa jaki saba!"

         "Toh ka sake shi Indai akan Parih ce ba zai kuma tab'a ba, ka kyale shi Amiduddawlah nace."

Sake shi yayi lokacin na fito daga dakin. Cikin b'acin rai yace.
"Wuce muje, zaki gaya min me kike nima a jikin namiji, da kika lalata Kuruciyar ki, bazama guri daya yasa kika lalace ba muje, Next zamu koma London dake."

"Wayyo Allah na! Wallahi bani zuwa ko ina! Idan sai na bika ne gwara na mutu kowa ya huta"

   Murmushi Aunty Amarya tayi, sannan tace..
"Hmm! Yar so! Yar dangi tace bazata bika ba, ku nime mai nima taimako ki bashi ita ku bar zargin Jalal ne zai b'ata muku ita,  Yarinya ba, sau nawa tana fitar dare yawon banzata sai shine zai lalata muku ita."

   Zaro ido nayi ban san lokacin da kuka ya kwace min ba.

🙄😎 Vote 😎

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now