MRS AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
Dedicated to my Aunty Nice😊
_🌹itɑ kiɱɑ ɑɓɑcɛ ɗɑ ɓɑ kѳwɑ kɛ ɗɑ itɑ ɓɑ! ɗɑ zɑʀɑɳ kɑ รɑkɛ yɑ zuɓɛ ɑ iɗɑɳuɳ ɳɑgɑʀtɑttuɳ ɱutɑɳɛ ɓɑtɑ kuɱɑ kwɑรѳwɑ🌹_
Page_21
Ban tab'a ganin abinda ya girgiza Ni kamar abinda Aunty Amarya da Jalal suke fad'a, cikin d'aga murya, da kwakwazo wanda yaja hankalinsu Mamie, suka sauko daga sama.
Kuka ma ashe rahama ce, dan gani dai amma babu kukan ya dauke, saukowa Mamie tayi take tambaya abinda ke faruwa, Aunty Amarya ta nuna mata ni, sannan ta fara magana da cewa.
"Wai Amidud ne yake zargin Jalal! Wanda suke uba d'aya zai lalata wancan sakaryan wacce ta gama yawonta cikin dare!"Murmushi Mamie tayi sannan tace.
"Allah ya shirya mana su, wuce d'aki"
"A'a! Mamie ta wuce muje kawai,"
Haka na koma bayan ta ina kuka nace.
"Mamie!"
Matsawa tayi cikin nuna bata damu ba tace.
"Ka dauketa!"Barin falon tayi, na juya zan Kamota ya, sai gani na nayi ina yawo, a sama kafin na fahimci meke faruwa ya ficce dani daga gidan, kuka nake da ihu nake da iya karfina, amma babu wanda ya kawo min agaji haka ya kai Ni har dakin shi, ya dangwala ni a kasa. Sannan ya shure ni tare da tsirta min yawun shi, gogewa nayi ina kuka.
"Wallahi na kuma ganin kin fita a gidan nan sai na karyaki, kowa yayi miki mugun shaida, shi ya koya miki amma gashi Mahaifiyarshi ta nuna bata san da haka ba, na kara ganinki a inda yake, makarantar tunda can ma kina da kananun karuwan da suke bud'a miki ido"
Yana gama gaya min me zafi yayi ficewar shi,
Kuka nayi shi har na godewa Allah. Ina zaune sai gashi yazo.
"Tashi ki wucce ki dafa mana abinda zamu karya dan matana tasa ba cin abinci karfe biyu."Jikina na rawa haka na mik'e na rab'a gefenshi na fita, ina shiga kitchen ɗin, dakyar na gama abin karyawan, ina gamawa ya shigo kitchen ɗin ya duba abincin, d'aga hannun shi kamar zai mare Ni, yace.
"Lusara kawai! Dubi jagwalgwalon da kika mana ko waye zai ci kayan amai idan mata ta tace bazata ci, Ni dake ne a gidan nan."Komawa gefe nayi, kamar zan shige cikin bangon tsabar tsoron shi, ba karya ina jin tsoron Ya Amidud saboda fuskarshi babu alamar wasa, kullum a take yake.
Kwashe abincin nayi naje na jera musu, ina gamawa yana shigo min da Kayana, watsa min yayi a tsakar dakin. Sannan yaje ina jin shi cikin wata nauyayyen turanci me mugun shakuwa, wanka nayi na saka wata karamar gown ta ankara, iyakarta gwiwata, sai wando slim jeans, baki nasaka yar karamar gyale na, na fito zuwa falon. Kitchen na nuna na dauko abincina, nazo na wuce abuna.
"Honey! Meye ya kawo aljanar yarinyar nan cikin gidan nan!""Hmm! Gwarama Kiyi hakuri domin kuwa tare zamu koma London Arsenal!"
Wani irin kallon tayi mishi shima kuma ya tsuke fuska, irin babu wasa a Maganar shi.
Ture abincin tayi sannan ta mike zata bar falon, kallonta yayi sannan ya kauda kai yace.
"Ki zauna ko kuma na sab'a miki"Kuka tasaka mishi, tare da cewa.
"Wallahi bazan zauna da karuwa ba, dub'eta fa. Yarinyar karama sai karuwanci har tasan tayi wanka ta dauki kwalliya har haka.""Ke wani shegen ne ya hanaki tashi kiyi?!"
"Kana nufin har wannan jagwalgwalon itace tai?!"
"Da kika gama cinye dadin zaki yi tunanin itace tayi ko ba ita bace!"
Sannan ya kaiwa bakin shi luma, tare da lumshe idanun shi yana cinye dad'i, na rigasu gama cin abincin na fito. Ina ganin yadda suke diban Gara, dariya nayi nace.
"Ashe dai karuwa ta iya haɗa Gara"
D'ago kai yayi, tare da watsa min wani irin kallon, tare da nuna min kitchen.
Wucewa nayi bakina kanin kafana, naje na fara wanke filet dina, shigowa tayi tare da fisgo ni cikin masifa tace.
"Wallahi zaki bar gidan nan!"Cikin iskancin da na koya a makaranta nace.
"Kika ce!"
"Ubanki nace"
Zaro ido nayi nace.
"Yanzun dubeki kamar tabarya da zani shine zaki zagar min iyaye, abu ko fasali wata salaf salaf dake""Kan kutumar bala'i! Ni kika zaga?" Ta nuna kanta.
Dariya na saka sannan na juya mata baya ina tafiyar agwagwa, nace.
"Can da yawarki"
Sannan na wuce dakina, ina dariya, ihu ta shiga kurmawa. Tana zagina dake yana ban daki, kafin ya fito yazo kofar d'akina tayita dukar kofar tana zagina da karuwa. Har da ce min.
"Mijina yafi karfin yar kauye haka karuwa!"Ta window na leko tare da cewa.
"Idan mijinki ya same Ni mata! Haba ai Kawayena since sai yafi kowa sa'a dan ina da kayan aiki, dan haka mijinki ko a tire ake kasa shi bani daukar shi Ni Parih sai Mr Handsome!"Dukar kofar tayi, nace.
"Oho dai bulogari kawai.""Sai naci kaniyarki idan kika fito."
"Oho dai idan baku nime Ni dan komai ba kodan kwasar Gara wa tumbinayenku, mijin ki ma zai nime abinda zai tada komaɗar da yayi"
"Wallahi zai na miki duka"
" Hhhhh! Matar Ya Amidud wallahi ko mafarki kika yi kin dake Ni, da safe kina tana tashi kiyi sadaka, maganin masifa"Haka ta biye min nayita manna mata hauka har ya fito.
"Meye haka! Lamisah kin biyewa Parih kunata hauka a cikin gida kaman wasu yara""Karuwar ce nake biyewa Wllhy sai ta bar min gida, dan ban fahimci zamanta a gidan nan ba, yarinya baliga kuma wacce akwai aure a tsakanin ku! Wallahi bazan yarda ba sai ta bar gidan nan"
"Aiko sai da ki mutu! Amma gidan Ya AMIDUD, kamar gidana ne, kuma na zo kenan bani fita"
"Ina wasa dake? Ko dake muke magana?! Akwai sa'anki a cikin mu ne?! Wallahi kika Kure Ni sai na karya miki mukamiki"
Kamar ruwa ya cinye Ni haka nayi shiru, ina zan iya hayagagar, shi yasa naja makatar bakina nayi shiru, tunda bani da hujjar magana kuma tsoron shi nake ji kar ya shigo ya min bid'ibid'i,."Honey! Kace tafi min daga gida"
"Babu inda zata fa!" Ya bata amsa......
Daga gobe ne?!🤣😂😎🙄