*MRS AMIDUD....?!*
_KURUCIYAR JAN PARIH_
Dedicated to my Aunty Nice😊
_Kafin kiran kan wane ka fara waiwayawa suwaye aka kirasu wane? Kafin kambama kanka a me kuɗi! Me ilimi! Me kyau! Sai ka duba Alumomi nawa aka hallaka sabida izza da d'agawa, karka yi tunanin tab'a kumar wani zaisa naka kumar ya karu sai ma ya zube wanwars karshe akere ana b'oye fuska, idan ka yarda kanka jan komarka kake gefe, domin da zaran duniya ta fara soki burutsi za a yi manta amonka da sautinka_ mutunci madara ce......
Wannan book ɗin baki d'aya shi kyauta ne ga Mutanen da suka sayi MJ2/3😍😘
Page_4"Baffa! Wannan kuma menene? A nan" ta nuna round about,
Murmushi yayi sannan yace.
"Wannan shine round about."
D'aga kai sama cikin tunani, ta kuma leka Baffa sannan tace mishi.
"Kace me sunan hi?"
"Round about!"
"Aihoo na gane sunan hi, randabat toh kenan randa ake ajiyetawa toh kenan idan Yar a kurkura tana jin ƙishirwa ba sai dai su zo su gyata su hai ruwa kenan"
"Bala'iiiiiii!" Inji Nura, me ba
Dariya ce ta kwacewa Baffanta yanayi ya kumawa, suna cikin tafiya dake sun biyo ta baya wato Maiduguri bypss, sai ya zagayo dasu Army barrack, dai dai, suka bullo tabaya kenan toh nan ma akwai wani round about, ɗin, wanda kana shigowa Bauchi zaka ga angina Giwa da.
Karewa gurin kallo tayi sannan tace.
"Baffa wannan kuma randabat din da wancan abun na meye"Juyawa yayi dan iya gajiya ya gaji da shegen tambayarta.
"Ai yana cinye duk me ganin abu ya tambaya ne."
Shiru tayi bata kuma magana ba, har suka wucce jifatu.A can g.r.a ko nace sir kashim, unguwar suka nufa. Cikin sir Kashim din wani had'ed'en gida suka danna.
A hankali motar ta shiga gidan, me mugun kyau da ɗaukar hankali, tun a mota Parih take kallon gidan, har motar ta tsaya sannan Alhaji Muhmood ya fito daga motar, ya buɗe mata sauka tayi tana kallon gidan, tunowa da Labarin da Iya Kaka ta bata yasata ja baya, sakamakon hango gidan karshe, wato dakin generator abinda Iya take gaya mata ba komai bane.
_Wato kinga mutanen da kayukan mutane suke kuɗi suna da dakin da yake firinji kudi, dan haka ki raba kanki da binnin nan_Dafa kafad'arta Baffa yayi ta fasa mishi ihu tare da k'amk'ame shi, tace.
"Wallahi Ni ku mai dani gida na fasa zuwa binnin"Mamaki ne ya rufe Nura yace..
"Toh meye kuma?!"
"Wallahi Iya kaka tace masu kudin binni da kayukar mutane suke yi."Cikin tsananin takaici Nura yace..
"Aikuwa can dakin gurin Franka zamu wulla ki a wancan daki."Aikuwa ta ware murya ta zuduma musu ihu, bana wasa ba,
"Haba Nura!"
"Kayi hakuri Alhaji yarinyar ce da ban haushi."Riƙe hannunta yayi har cikin gidan, tana tirjewa yana janta har zuwa cikin gidan.
Suna shiga yaran shi suka tawo da gudu suna mishi oyoyo aikuwa Parih ta juya da gudu,, sai da yabi bayanta, ta kasa bud'e kofar, abinda ya koreta kuwa, teddy da taga a hannun Aarib, shine ya sanyata wasan tsare. Komawa bayan Baffa tayi ta boya tana leka teddy."A'ah Alhaji Barka da hanya, Jal Parih, fito mana."
Inji wata babbar mace. Kyakyawa me kyan diri, kana ganinta ka ga bafulatana, a kala shekaru hansin da biyu, ka tasowa tayi tace.
"Alhaji lafiya? Ku ke tsaye.""Ki bari kawai Adawiyah, Parih ce ta hanani motsi daga shigowar mu shine ta juya a guje dama kuma kafin mu iso sai da muka Ji jiki da ita."
Riko hannunta Hajiya Adawiyah tayi.
"Ayya ka tuna lokacin da Amatul Islam tazo kafin aurenta da Absham, ai haka muka yi fama da ita har bayan auren su kafin su tafi Pakistan, haka yayi ta Fama da ita."Cikin jimami yace.
"Allah ya jikansu da Rahama Amin, gashi yarinya zata tashi bata sansu ba.""Alhaji Barka da zuwa! A'a Parih ce amma Alhaji kunsha artabu da Iyar Parih "
"Ke dai bari,"
"Daddy me ka kawo mana."
Yaran suka tambaya, biyu mata sai na miji a tsakiyarsu,
Nuna musu Parih yayi, ita kuma hankalinta na kan tv falon inda yake aiki ya fitota da hannu mutumin cikin tv yayi ta girgiza kai, ya kuma kiranta ta girgiza mishi kai bazata zo ba, aikuwa ya taso da sauri.
"Wayyo Allah na na higa uku Alkur'an bazan zo ba"
Kafin su an kara Parih tayi wani uban tsalle ta koma bayan kujeran falon ta b'oya jikinta na rawa,(🤣😂)Me zasu yi ban da dariya, tsabar kauyanci zalla.
Alhaji Muhmood yake basu labarin yadda sukayi da ita kafin ta shiga motar shi, da irin tambayar da suka sha."Fito abinki kinji Parihna"
Zaro ido tayi waje sannan tace.
"Kwarankwatsa idan na hito kama Ni zai yi kinga ji ce min yayi nazo"
Had'iye dariyar ta tayi, sannan tace.
"Babu abinda zai miki, miki kinji fito."
"Hikenan zan hito! Don Allah kice mihi kar ya kuma yahito ni."More comments nd Voter
More Page😎