30

2.8K 666 48
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

https://my.w.tt/XGvckkY6N6

Dedicated to my Aunty Nice😊

    

   

30.
A razane ta mike zaune tana raba idanun.
Share ta yayi dan ya cusa mata haushi ya dauki rigar shi ya fito zuwa dakina.

    Ina kwance dan bayan da na idar da sallah na kwanta kayan jikina da na kwanta dashi 3qrts ne, dan haka yana shigowa.

         Ya duba yadda nake barci, daukar pillow yayi ya wurga a kasa.

      Sannan ya kwanta rub da ciki, baya jin barci amma dan rama abinda lamisah.

        ......
Kululu! Cikinta ya bata sauti.
"A ina yasan wannan lamari! Ba sai Likita bane ya gaya mishi ba."

     A rud'e ta fito daga dakin ta. Kallon kofar d'akina tayi taga a rufe.

        Haka tayi ta sintiri a kofar d'akin, har kusan sha daya ya farka.
             Har zai fita sai ya shiga ban daki yayi wanka da alola, sannan ya tashe ni. Tura mishi baki nayi cikin shagwaɓa nace.
"Wai meye yasa kai ka cika damun rayuwata! Duba barci nake amma ka...."

    Zare ido nayi dan ganin Ya AMIDUD ya dauke ni zuwa ban daki.
   "Wai meye haka?!"
    "Ban sani ba! Amma nasan matuƙar zaki min rashin kunya toh noma zan baki kunya."

Ture shi nayi ina b'ata rai, cikin raina ina cewa.
*Mutum sai kace wani d'an iska! Ya wani dauke Ni kamar wata Yar tsanar yara.*

          "Waye dan iska?!"
   A firgice na kalle shi, tsabar waita nace.
"Da gaske kaji abinda na fada ne?!"

           Juyawa yayi ya fita bai kuma bin takaina ba.
*_Irin abinda nake gudu kenan! Yarinyar da zaka iya Haihuwar ta! Itace take zaginka! Alhamdulillah da bani da wani feelings akanta da ban san inda zan cusa kaina ba_*

Wannan itace abinda yake fada yayinda yake barin dakin.

Turus ya tsaya nad'e hannun shi yayi a kirjinshi, yana kallon yadda ta zuba mishi ido, cike da mamaki tare da farga.
"Amidud! Ba dai."

"Koda wasa! Karki fara zargina idan zaki yi ma kiwa akanki. Ce miki nayi zan biya bukata dake. Niman yadda zan sami nutsuwa a gare ki kika ki. Toh sai me dan na fita na samu a wajen da nake da ikon samu, na miki alqawarin bazan tab'a sauraren wata mace ba amma kinki fahimtar haka."

   Riko hannun shi tayi suka shige dakin su.
        "Don Allah! Karka min haka. Wallahi zan iya maka yadda zaka ji ma nafi ko wacce mace kulawa da kai, don Allah ka rufe min asiri."

           Ta faɗa tare da zubda kwalla, kokuwar raba shi da rigar jikin shi take, har ta samu nasarar toh(Hazikai sun hanani filla filla 😂🤣🤸 Da anga tijara)

  Wato abinda ya f'ahimta ta iya komai na jan hankalin d'a namiji.

Matsalar ta tana da matuƙar kiwuya da don jikinta. Shi yasa matukar zasu jega rayuwar aure toh takan nuna kasawarta.

          Baka jin komai a dakin sai bada wata irin sauti.
Haka suka gama abinsu. Dukda bai samu yadda yake so ba, amma ya rage  zafi inji shi.
"Me yasa baki ganewa?! Me yasa ba zaki fahimci yadda nake gudun b'acin ranki ba?! Wallahi tallahi yarinyar can bani sonta!

Ko sha'awar karama irinta ba nayi, amma sai kiyita gaya min magana son ranki, Why Lamisah?"

       D'ago kai tayi cikin damuwa tace.
"Hmm! Kayi hakuri don Allah! Amma don Allah ka gaya mata a gabanta baka sonta, idan ba haka kayi mata ba. Zata iya tunanin wata rana zaka iya."

Rike hannunta yayi sosai, yana kallon cikin idanunta.
"Idan da zan sota da nayi tun kafin na aureki! Idan da sha'awarta nake ji, da bazan jima ba na aurota! Ki yarda da Ni Allah babu dalilin da zai sani auro wancan pagal din. Amma Insha Allah zan miki abinda zai saki farin ciki."

         Mikar da ita yayi suka shiga ban daki, a tare suka yi wanka. Suna fitowa kayan su. Suka saka sannan suka fito d'akina suka shigo. Nima nagama banzar shigar da na saba! Karamin gajeren wando. Da riga me dogon hannun.

                "Amma wannan shigar bai dace ba gaskiya. Kuma kina jin zafin haka, kace ta cire."

   Kura min ido yayi. Yaga shi nake kallo,
     "Kin ganta nan! Matata ce! Kuma ina matuƙar sonta! Dan haka idan kina tunanin wani abu a ranki ki daina dan Ni bana sonki."

             "Auuuwu! Toh ni ina ruwana. Matar kace mi kuma na yor seeseta. Nut wori mi ef yu lek mi sidoun witi mi ef yu nu lek mi tak mi home!"

       Ina gaya mishi haka na juya mishi baya nayi kwanciyata.
Fita suka yi . Matar shi tace.
" Yarinyar nan ta rena ka. Gaskiya bazan kayi mata jan ido in ba haka ba zata kunyata a gaban mutane."

   Haka tayi ta ziga shi har ya kunnu sosai, dan haka koda suka kawo min abinci naki tashi.

        "Zaki tashi ko sai na zane ki!"
   Ya daka min tsawa, tashi nayi na zauna ina kwalla.

      Daukar abincin nayi na fara ci, ina kuka sosai.

         Zaro belt din jikin yayi yana nadewa zai zane Ni.
"Kukan Uban me kike min? Wallahi idan baki min shiru ba, sai na fasa jikinki, wawuya kawai.
 
     Kuma wallahi wannan ya zama maganar mu dake na karshe akan shigar jikinki idan kuma na kuma ganinki da shigar banza sai na zane ki yadda gobe ba zaki kuma ba.

  Idan an kiraki da jahila ki kamawa mutane rashin kunya, Allah ko mata na kika mata rashin kunya. Sai na miki mugun duka."

    Haka ya gama razana ni, tare da Alkawarin sai ya farfasa min jiki.

    Lokac guda tsoron shi ya kamani, dan haka ina gama cin abinci na sauya kayan jikina, shi kuma ya da matar shi suka tafi yi mana sabon booking.

          Ni ɗaya tal a masaukin, haka suka gama abinda zasu yi sannan suka dawo bayan sun sha yawon su, ina kan abin sallah ya shigo ya ajiye min abinci.
"Minti goma suka rage miki, dan haka kiyi maza kici zamu tafi."

       Gyad'a kai nayi, a raina nace.
"Wallahi sai na haukata matar ka, tunda tasa kayi min fada itama sai tayi kuka kamar yadda nayi."

     Haka naci abincin a gurguje, ina ci ina kwarewa.

     Ina gama cin abincin sai gasu shida matar shi. Mik'ewa nayi na wanke hannuna tare da ɗaukar kayana. Sannan muka fita,

             Hmm naga salo sosai. Murmushi nayi tare da tuna abinda zai faru zuwa anjima kadan.

        Domin ina son idan muka shiga airport din kafin tashin jirgin mu. Na shiga Mall din cikin na sayo kadangaren roba ko macijin roba.

      Tsayawa nayi naki tafiya, kallona ya juya yayi yana kallona.
"What??!"
        "Kayi hakuri! Ka bani kuɗi zan sayi wata Teddy ne a cikin mall din airport din"

 

         "Hmm!" Ciro kudin yayi tare da mika min, na amsa da sauri.

      "Honey! Me zata yi da kudi?!"
"Ita ta sani?!"
       Kallonta nayi na zabga mata harara, na nuna mata karamin yatsana. Alamun sai kinyi fitsari a wandon ki.

     Tare da murguda mata bakina nayi.
       Ganin yadda nake kifkifta mata idanu, haka muka isa daga shiga. Naje na sayo kadangaren da macijin, a raina nace.
"Sillar rama ta kare miki! Ba dai mijinki baya zaman gida ba, hhhh  Alqur'an sai kinyi karamin kirezy Ni dake ne, dama na barki ne muje zaki ga yadda ake wasan sai kin rasa yadda zaki cusa kanki"

     Itama Lamisah shirya nata plan din take, yadda muna shiga Spain. Sai ta sani barin garin ba tare da kowa ya fahimci itace.

Thanks
   🤭😞Mun kai Pagen 30 har yanzun Vote Bai kai 4k ba Kamar baku yin labarin.

    Please ku tayani forward 👌🏻
Oum Muwaddah 🤫

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now