Page_6

2.8K 474 43
                                    

*MRS AMIDUD....?!*

_KURUCIYAR JAN PARIH_

Dedicated to my Aunty Nice😊

Page_6
     Juyawa tayi abinta Jalal na hangota, daga window dakin shi har ta wucce cikin gida, lokacin har su Hajiya Adawiyah sun fito daga cikin gidan suna nimanta, a kofar falo suka gamu, sai wiki-wiki take da idanunta.
"Parih! Ina kika je ko kaya baki saka ba."

"Mamie waje take gurin Malam Almu! Ban san me ya faru ba sai tashin Babbar rigarshi kawai nake gani"

      Kallon ta Hajiya Adawiyah tayi domin jiran karin bayani daga bakin Parih.
  Tura nan ƙaramin bakinta tayi sannan tace.
"Yoh naga kuna mitar ya dame ku hine na kore hi"

     Zaro ido suka yi gabaki d'aya su suka ce.
"Meye!!!?"
     Wucce su tayi tare da watsar da hannun ta a iska, tace.
"Eh koran hi nayi bayi kuma zuwa muku sai dai ku ji labarin ya hige gidan nan."

      Bin ta suka yi da ido, musamman Jalal da yake binta da wani irin kallo.

       Fita yayi daga cikin gidan ya nufi, inda d'akin shi yake ya faɗa gadon shi yana rintsa idanunshi, tuno yanayin tariyar yayi.

       .....
"Parih karki kuma fita babu kaya a jikinki! Kinji dan akwai masu yanka mutane a unguwar nan kina jina,"
  Gyada kai tayi idanunta a waje, can ta d'ago kai tace mata.
"Hajiya! Idan an yanke kan mutum cinyewa ake?"

        "Eh toh musamman idan mutumin ya kasance magananne! Kuma me fita ba kaya"
   Ta karshe maganar ta hanyar haka.
           Shafa mata Jet Hajiya Adawiyah tayi zata taje mata uban gashin kan ta, ta riko hannun ta cikin ihu tace.
"Alkur'an! Baki taje min gahina haka! Kutt kin manta inda ruwan tsige mutum da rashin ya zuba min ne, da zaki taje min Alkur'an kina tajewa hita gahin zai yi kamar yadda ake sale gahin kaza!"
   
    Mamaki ne ya rufe Hajiya Adawiyah tace.
"Toh shi kenan! Bari na miki a hankali yadda bazai miki zafi ba tunda zan tsige miki gashi me"

   Shigowar Buhayyah da Amrozia yasata kwace kanta tace.
"Don Allah! Zo ki duba min tsakar kayina ko an tsige min gahina"

     Zuwa Buhayyah tayi ta leka kanta! Da gaske yayi ja amma ba wani na tashin hankali ba.
"Sannu! Amma ba wani ciwo bane da kawai ja gurin yayi sabida kalar skin dinki'

  Kallon Buhayyah tayi sannan ta yatsina fuska tace.
"Me kika ce?"
       "Kinga zo ki saka kayan Buhayyah kafin mu shiga kasuwa."
          Juyawa tayi gashin kanta yayi tsage tsage, taki kuma a gyara mata.
   Cikin shagwaɓa Buhayyah tace.
"Mamie yaushe zamu tafi Gida dubu?"
          Kallon ta Hajiya Adawiyah tayi sannan ta cigaba da abinda take yi, dan tasan dalilinta na son guduwa daga gidan, sabida dodon su da zai dawo gidan wato Babban Yayansu.

    Narka fuska tayi sosai kamar zata fasa ihu, ita ko PARIH tana gaban madubi tana aiki. Wato zama tayi ta bud'e kwalbar maganin mura ta juye a cikin roban man shafawa.

   
    "Please Mamie!"
Juyawa Parih tayi a fusace, kamar wacce aka yi da ita.
"Ke dilla can! Kin dame mu da wani abu wai fidda"

    Rike baki suka yi sakamakon  b'ata fuskar ta da tayi wai nan ta kure a daka, idan kaga fuskar tankar an shafa bakin paint. Dariya Buhayyah ta saka tare da rike cikin tace.
"Wallahi kin koma kamar Yar auta!"

        "Zo na goge miki! Amma fuskar ki tab'aci!"
      
"Alkur'an baki goge min kwalliyata!"
         Duk yadda suka so goge mata kwalliyar taki,  karshe haka suka kyaleta, ta suka fito kowa sai dariya suke mata, abincin ta Amrozia tayi ta ajiye mata a gabanta. Kallon abincin tayi sannan ta d'ago kanta kamar zata fasa kuka tace.
"Meye sunan wannan abincin me kama da gwazarma?"
  Wato makaroni! Take tambaya,
    Leka kwanon tayi sannan ta d'ago kanta da sauri kamar wacce taga dodo tace.
"Alkur'an bani cin abincin nan!"
 
       "Kici macaroni ce!"
    "Markarome! Jifa sunan abu sai kace markaɗe! Wallahi bani cin sa"
  
  Kuka tasaka tare da kwanciya tayi a kasa, tare da birgima tana ihu.
"Wayyo Allah na! Wallahi bani cin wannan gwazarman nan, Alkur'an ku mai dani gurin Kaka Iya, ta bani gaya naci."
Sai da Alhaji Muhmood ya sauko daga sama, ya zauna kusada ita yace.
"Ku kawo min tuwon da aka min!"
           Aunty Amarya ce ta kawo mishi tuwon akayi ya dauka ya zuba mata, a cikin filet kallon tuwon tayi ta ganshi ruwan kasa wato semo miyar egusi, d'ago kai tayi sannan tace.
"Wannan abu me kama da bayan garin nan kuma nufin Ni ce zan ci! Wallahi bani cin shi"

         Dafe goshin sa tsabar tashin hankali,
          
         Rigimar da tasaka musu, kad'ai ya isa.

          Asalin Alhaji Muhmood dan misau ne daga kauyen Dabji, su uku iyayensu suka haifa, Alhaji Muhmood sai Hajiya Fatimah tana aure a Gamawa, sai  Abtisham Mahaifin Hal Parih.

       Alhaji Muhmood yana da mata biyu, Hajiya Adawiyah sai Amaryanta Aunty Mariyah. Sannan yana da yara goma, Hajiya Adawiyah tana da Yara shida,  Amiduddawlah shine babba sai Sabriyah tana aure A gida dubu itace Buhayyah take cewa zata gurinta.
    Sai Ahmad wanda yake binta Sabriyah, sai  Fahmeedah da Fahhamah yan biyu ne, autarsu ce Buhayyah.

       Aunty Mariyah tana da yara Hudu, Jalal shine Babban sa'an Ahmad, sai Hashmat take binshi ita kuma sa'ar su Fahmeedah da Fahhamah, sai Amrozia wacce suke sa'anin da Buhayyah, tsakanin su da Aarib shekara d'aya suka bashi
    Gidan ana zaman lafiya sosai dan Hajiya Adawiyah ta kame girmanta, ita kuma Aunty Amarya ta rike kankantar ta, sannan taja Amiduddawlah a jiki sosai wanda ya zama ɗan d'akin ta ne.

    Sai Hajiya Fatimah tana da yara uku,  Najmuddawlah shine babbar, Huwaydah sannan karamar su Jadwah.

          Sai Mahaifin Jal Parih, Abtisham, Parih kadai suka haifa.
          Asalin sunanta Jal Parih ce, bayan Rasuwar Iyayenta da aka bawa Kaka Iya tace ita bazata iya kiranta da Jal PARIH ba, sabida bata iya kiran sunan ba, da farko ma Jar Fara take kiranta dashi, sai daga baya Kawun Parih yake ce mata bafa haka sunan yake ba, Sunan Jal PARIH ce, tace ita bazata iya ba sai da abinda yazo bakin ta takirata da Jan Parih.....

     🙄🙄🙄🙄
_Kun dame Ni da Update sannan babu comments ɗin arziki balle Vote idan naga Voter da comments maybe na baku 7 gobe da safe_

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now