22

3.4K 372 33
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to my Aunty Nice😊

pɑgɛ_22
  Yana gaya mata haka ya tawo bakin kofa na ya buga, buɗewa nayi sannan na sunkuyar da kaina kamar mutuniyar arziki.

"Wallahi na dawo naji labarin kin mata rashin kunya sai na zaneki! Kuma karfe uku ki shiga ki mana abincin rana"

  Tura baki nayi gaba, cikin kunkuni nace.
"Ita matar gidan zaman me take da bazata girka maku abinci ba sai!"

     "Keee! Zagina kike?!"
  Zaro ido nayi tare da yin rau-rau da idanuna nace.
"Ni ban zageka ba"
Tsaki yayi tare da barin kofar dakin nace.
"Allah zai yaga min baƙi ne a hana Ni magana"

           Cak ya tsaya Alqur'an garke kofar nayi tare, da sauke ajiyar zuciya. Ina cewa,
" Mutum sai kyan tsiya! Mtseew ko burge Ni bayi ba, kawai kayan shi ne yayi min kyau"

     Dafe kirjina nayi lokacin da matar shi ta shiga buga min kofar cikin tsokana nace.
"Doguwa da hankali dace ne!  Me zan miki"

      "Ubanki kika zaga!"
   Sai dai window naje sannan nace.
"Eh naji Ubana ya gode! A wuce a yi girki idan arusa ya dawo ya loda a tumbiyeyen shi dan yau boyiboyinku bazata dafa ba!"

         "Kan Uba!"

      "Coman Gara way! Yau sai dai yunwa ta karku dan bazan girka muku ba, ai Mijinki ne ki shiga ki  zuba mishi esfirianki ki!"

         Dukar kofar tayi cikin wani irin zagi.
Nace "oho"

   Gyara kwanciyata nayi na fara barci, cikin jin dadin sam na manta zan shiga na mishi girki.
Sai can da naji ana kiran sallah na tashi, sannan na wucce nayi wanka saboda bani da tsarki, ina fitowa naji yana cewa.
" Zaki buɗe ko sai na karyaki idan na bude."
    Tura baki nayi naje na bude, shaf na manta towel ne a jikina, zaro ido matar sa tayi, to Ni ina ruwana, rankwshi kaina yayi na fasa kuka tare da rike towel ɗin da yake shirin faduwa a jikina, turani dakin yayi sannan ya shigo, tare da banke kofar.
    Tsaro yasani shigewa ban daki da gudu, ina shiga na rufe gam ina kuka.

        "Wato ban isa ince kiyi abu ba shine kika kwanta, wallahi na kirga goma baki fito ba, sai na biyo ki har ban dakin."

  "Toh naji kayi hakuri ka daina dukana, idan kana min haƙa zan dinga jin haushinka"
   Tsaki yayi ya ficce tare da buga kofar fitowa nayi na dauki riga da skirt na saka na lace na fito ko dan kwali ban daura ba,  na sake gashin a bayana na wuce kitchen ashe kayan abinci ya sayo wanda zasu yi amfani dashi na kwanaki kafin su koma, cus-cus na. Dauka   dauki kayan lambu na wanke, dukda bani da kintsi (🤣😎 idan kaci ka mugu ko mara kirki dole sai ka zambaci kanka) Mamie bata barmu haka ba,  sai da ta koya mana sarafa  abinci na gargajiya da na zamani, jollop ɗin cus-cus din nayi da kayan lambu, sannan na duba naga d'anye kifi na ice zama nayi na wanke dan naji Mamie tana cewa shi mutum ne me son kifi musamman na ice.

       Wanke kifin nayi da lemon tsami, na cire mishi karnin sannan na markad'a kayan miya kamar jajjage, na zuba akan kifin zuba mai a tunkuya na yanyanka albasa suka shiga soyuwa, rage wutar gas din nayi. Na fito duba kayana nayi babu wayata, tsaki nayi sannan na koma ciki kitchen na zuba kayan miyar na ci-gaba da soyawa har yayi min sannan na tsayar da ruwan miyar sannan na zuba kifin na fasa mishi maggi da gishiri, sannan na fito, ganin shi nayi yana zaune, kauda kai nayi dan gidan ya kaure da kamshin girkin. Ganin na nufi kofar fita, yace min.
"Ke!"
Juyawa nayi ina raba idanu.
"Uwar me zaki fita yi"
Tab'e baki nayi sannan nace.
"Zanje amso zobo ne da kayan kamshi"
      "Dame dame?!"
Tura baki nayi sannan nace.
"Ni nasan abinda nake bukata!"
   "Toh koma ba zaki fita ba!"
    "Toh! Da zobo da tiara sai sigar!"
" Na sayo sugar yana cikin kwali"
         "Toh sai citta da kanunfari!"
      "Hmm! Suke nan"
  "Wayata!"
          Sannan na juya zuwa kitchen ɗin, bayan kaman minti goma sai ga Buhayyah, rungume juna muka yi sannan na matsa mata ta shiga daga zobon, Ni kuma ina kwashe abincin! Na zuba a warme biyu, sai miyar kifin. Sannan na koma yanka ganye salat, na hada na zuba a wani ƙaramin bowl.

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now