27

2.7K 403 72
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

https://my.w.tt/XGvckkY6N6

Dedicated to my Aunty Nice😊

      *Wiriri 🤸🤸🤸 Ba fada damu ba kwana mita! Loma d'aya gaggari kato! Wannan shine kirarin Pharih🤫🤣😜*

 

27.
    Zaro idanu nayi waje tare da kallon gefe da gefe, kafin na ce.
"Wacece katuwar banza! Ai singalali god'iya! Kinji mijinki wai kece katuwar banza"

    Na kuma rufe bakina da hannu ina dariya, Halwani sai dariya yake. Tsabar yaji dad'in yadda nake shirmen.

     "Don Allah! Bar dariya" ya fadawa Halwani, Ni kuma ya juyo ya kafe Ni da ido, ganin yadda nake dariya, na yi baya da kaina. Dake ban saka hijab ba, karamin gyale na yane kaina dashi, toh idan ina dariya jikina ke rawa hatta kirjina. Abinda ya shagaltar dashi kenan. Ya kuma kafe Ni da ido,

    "Honey! Wannan irin kallon da?!"
     Diriricewa yayi sabida Kunyar da ya kama shi, sai a lokacin na lura da ashe kallona.

             Juyawa yayi ya koma inda yake, yana me b'ata rai kamar wanda yake da gaskiya.

    *Amidud! Meke damunka? Meye yake adabbar ruhin ka? Meye matar ka bata dashi? Itama tana da abinda yarinyar take dashi karka bari ka jawa kanka reni*

Da wannan hudubar zuciyarshi ta karfafa mishi abinda yake hasashe!
        Har suka isa filin tashi da sauka na jirage, dan daga nan Lagos zasu wuce daga can kuma zasu wuce Abu Dhabi! Na kasar Dubai.

         Sun dan jima bayan zuwan shi, Lamisah sai narkewa take a jikin shi.

              Tunda na zauna nake kallon yadda jirgi yake, ina mamakin Yadda zan kasance a cikin jirgin.

          Dole na nutsu bawai dan ina Tsoron kowa ba, sai dan tsoron yadda zan kasance a cikin jirgi. Take ciki na ya cire gefe guda.

         Lokacin da jirgin mu zai tashi ne na rud'e. Zuwa yayi ya janyo ni jikin shi, yace.
"Rufe idanunki?"
  Ya manta da matar shi fa, a hankali muke tafiya hakuri nayi na bud'e idanuna! Na kalli muna tunkarar jirgin.

     D'ago kai nayi ina kallon shi, bai kulani ba, yace.
" Kalli gabanki mata na taka kallon ki"

       Ban san lokacin da na daura kaina a gefen kirjin shi ba, ina tura bakina nace.
"Ina ruwana da ita! Matar kace. Ni kuma Kanwar kace"
Na fada ina tura mishi bakina.

Mintsinina yayi sai da na saka mishi kuka. Aikuwa Lamisah tace.
"Honey! Meye haka?"

      "A'a moni ne ba honi ba, ni wallahi na ma fasa zuwa!"
         Matse ni yayi na kuma saka mishi kuka, ina fadin.
"Sai na gayawa Mamie!"
    Danbarwa muka yi sosai kafin jirgin mu ya tashi.

  Hmmm Allah ya kiyaye shemu aikin kauyanci! Domin jirgin na tashi. Na tsala musu ihu, sai da kowa ya zuba min ido.

   Kunya ya kama shi, matar shi sai tura baki take, yo ko a jikin na.
      Can da tashin mu aka kawo mana abinci, kallon wata farar namar kaza nayi, na juya musu kai nace.
"Alqur'an bani cin abincin da aka dafashi da namar jaki!"

   Zaro idanu yayi cikin damuwa yace.
" Maza dauka kici! Babu namar jaki."
    "Yasin bani cin abincin da!"
     Na gaya mishi a hasale.

           Kawo min cake aka yi da wani lemon gora..

         Mun isa Lagos lafiya sai zare idanu nake, muna isa masaukin mu kafin jirgin mu ya tashi sai da muka raba hali da Lamisah, amma wannan karon nice da laifi.
         Abinda ya faru kuwa🙈🙊🙉 bayan saukar mu, ya nuna min dakin da zan zauna  kafin lokacin tashin mu yayi. Toh muna shiga na kwanta, su kuma suka wuce nasu.

        Toh da na shiga ban daki, sai naga komai na ban dakin ba irin na gida bane, gurin kar nayi musu b'arna. Shine naje na kirata na nuna min.
    
            Kuma daddin dad'awa ina jin fitsari, kawai ina shiga dakin su na bankad'e su, Alqur'an suna tsaka da......🙊🙉
    "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Yau naga boni! Wayyo Allah na kuyi hakuri"

          Ture shi tayi Ni kuwa na fice da gudu. Jikina na kerma, nufa duk Iskanci na ban tab'a ganin irin wannan Rayuwar ba.

      Zuwa nayi Tsakiyar gadona na takura kaina, tare da boye fuskana, a tsakanin cinyata.

          Shigowa yayi da niyyar yayi min fada, dan koda ya fincikoni, fitsari na sake a jikina tare da saka mishi kuka.
"Don Allah kayi hakuri! Wallahi bazan kuma ba"

              Ture Ni yayi, daga dakin yayi ficewar shi.

                Itama ta shigo, cikin masifa ta gama zagina har da ce min.
"Iskancin ya motsa shine aka zo ganin me nake da mijina! Karuwa kawai!"

     Tab'e baki nayi sannan nace.
" A dauri kashi ko a b'ata igiya uwar me zan gani, da wani kayan hana arzikin ku nan tirrrr da kazamai kawai, ai idan naga kayan takaicin ku na kwala asara duniyati da lahirati"

      "Ke ban son rashin kunya ina gaya miki mijina yafi karfin ki"
  Ta gaya min.
   "Eh nasan yafi karfina! Nima Y'a ce! Kuma ko da miliyan aka hadani da mijinki gwara na auri
          Me kwasan kashi da mijinki, Allah yayi min tsari da zama inuwar shi, kuma ki saka a ranki nafi karfin shi."

           D'aga hannu tayi zata mare ni. Na fashe da dariya sannan nace.
"Tochi mi! Tochi danja, i siwe a go fi sikata yo hedi"

            " Wallahi sai na hada ki dashi tunda ya hanaki haukar turancin nan"
   
"Idan yazo kice ya dauki Ni ya wurgani cikin teku kifi ya cinye Ni shine ƙarshen k'iyayyar da kike min!"

     "Kee fara kike ko Parih sai na miki illa"
     
"Nima nayi miki alqawarin sai na hanaki sukuni!"

    "Wannan rashin hankalin fa? Kin zo kin sami yarinya kunata shirme! Wuce ki bani guri ko na sab'a miki"

     Fita tayi, Ni kuma yayo kaina ya tsinka min mari, sai da naji kamar an make ni da karfe, d'ago kai nayi ina Kallon shi.

         Ban san lokacin da naja kwatina na fara kiciniyar fita a dakin ba, na kasa kuka.

       Sai hadiyar zuciya nake, kwace jakar yayi. Ya tura Ni ban daki sannan ya bude min famfo akaina, yana fadin.
"Ban tab'a dukar mace ba, sai ke ko Lamisah ban tab'a Zungure ta ba, amma ke kin sani na mare ki. Bawai dan kin zageta ba! Har Ni zaki ce da ki aure Ni gwara ki auri me kwasan kashi! Kinsan yadda maganar ta dake ni, kiyi wanka ki fito idan na kuma jin haka sai na miki dukar tsiya"

       🙊🤭☹️.....

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now