ℛℴ𝓂𝒶𝓃𝒸𝒾𝓃ℊ 𝒫𝒶ℊℯ💋

4K 495 80
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

https://my.w.tt/XGvckkY6N6

Dedicated to my Aunty Nice😊

𝓜𝓪𝓲_𝓓𝓪𝓶𝓫𝓾❦︎

 

40.𝓻𝓸𝓶𝓪𝓷𝓬𝓲𝓷𝓰 𝓹𝓪𝓰𝓮

      Ihu yaron yayi tare da zuɓewa kasa rike da sandar girman shi, naja Hannun Mayah muka bar gurin, kallona Mayah tayi cikin tashin hankali tace.
"Kinsan halin Baban Yaron kuwa?! Toh kashe mutum a gurin shi, sauki yake dashi akan kashe sauro "

   "Hukumar FIFA! Tasan girman darajar Yayana bazata bari wani ya cutar dashi, ke jinki me yasa Club din Madrid suka ki rabuwa da Yayana ai dan suna moruwa dashi ne! Kawai koyi kwatar kanki, kafin wani ya ci miki mutuncinki "

      Muna komawa Class sai ga Uban yaron tare da wasu yan koran shi.
   Da wasu kananun idanun shi kamar matsatsaku, yazo ya tsaya a gaba na.

      Tsabar bala'in tsoron shi dake ko magana yake, tsoron daga kai ake, Ni kuwa kallon juna muka yi cikin rashin tsoro nace.
"Kana da bukatar wani abu ne?!"
  
Murmushi yayi sannan yace.
"Meye Rio yayi miki?!"
      
  "Ubangijin mu ya hanamu aikata Alfasha, kuma ya gargad'e mu da muke kanmu! Ban yi mishi haka dan tozarci ba sai dan ya gane Ni bana cikin mutane banza, amma idan haka ya dame shi yayi hakuri. Ni musulma ce! Kuma ya san da haka.

        Kuma ko kai ne aka zo aka yiwa abinda yayi min nasan sai inda karfin ka ya kare. Ko ba haka ba"

     Gyad'a min kai yayi sannan nace.
"Kazo rama mishi ko? Bayan nice yayiwa laifi."

   "Kiyi hakuri! Ba zai kuma tab'a ki ba, wani ma idan ya tab'a ki, ki gaya mishi sai na sa yan mishi barin wuta, akan shi"

    Gyad'a mishi kai nayi, dan haka cikin ruwan sanyi na warware wannan rikicin, kuma ya tafi yana me jin dadin bayanin da nayi Mishi.

         Naga mamakin mutane akan abinda ya faru, wasu har suna cewa ko zasu min tsiya amma ba yanzun ba.

          ......
A gajiye na koma gida, dan yau Ya Amidud zai dawo daga, Arsenal sunje wasan Championshi.

        Sallah nayi tare da fitowa da sauri na fara abincin dake yana son tuwo, na jima sosai a kitchen ina aiki. Ina gamawa na tattara abincin na wuce dashi d'akina dan wannan mahaukaciyar cinye min zata yi.

         Wanka nayi tare da yin sallar la'asar, ina cikin saka kayana ya shigo, juyawa nayi ina kallon shi.

   Share shi nayi cikin jin haushi, wanda ban san dalilin haka ba.
    Takowa yayi har bayana, ya sanya hannun shi ya juyo ni,

    " Amor mio,amo pos de
Cien razones"
        (My Love, i love You more than a hundred reasons)

       Tab'e baki nayi sannan nace mishi,
    
"That is great, so tell me five reasons" dan ina iya jin wasu kalmomin amma bazan iya fadar su ba.
       D'ago kai na yayi ina kallon cikin idanun shi yace.
"Numeros uno, por tu bella  sonrisa"
(First because  of your beautiful smile)

          "Hmmm thanks you mijin Lamisah, what is  the second reasons" nace mishi ina tsare shi da ido.
          Girgiza kai yake, cikin damuwa. Riko hannuna yayi muka zauna, sannan yace.

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now