*MRS AMIDUD....?!*
_KURUCIYAR JAN PARIH_
Dedicated to my Aunty Nice😊
🤣😂 Angry bird😎
Page_5
"Fito kinji babu abinda zai miki."
"Humm kawai ki kore hi zan fito."Dafe goshinta Hajiya Adawiyah tayi sannan tace.
"Yi hakuri fito,na Kore shi."
Dakyar tafito daga bayan kujera, tana zare idanunta.Zauna da ita tayi akan kujera, aikuwa ta buga tsalle sai da Yaran gidan suka fashe da dariya.
"Buhayyah kalli abin dariya."
Wacce aka kira da buhayyah, murmushi tayi sannan ta mika mata hannu, tace.
"Parih! Har kin manta damu ne! Aarib! Wannan arusa kin tunashi kika ce haka kuke kiran katu a Dabji, sai Ni kika ce idan da a Dabji nake me kyau za a kirani, sai Amrozia. Kin tunamu"Rau-rau tayi da idanu sannan cikin kankanuwar Murya tace.
"Zaki mai dani gurin Kakata wallahi daga zuwana naga Bala'in da suka fi karfina,"Dariya suka yi sannan ce.
"Toh ai kin dawo kenan bazaki kuma zuwa dabji ba."Kura musu ido tayi kafin tayi wani irin yatsuna fuska, sannan ta ware murya ta fasa musu kuka, tanayi tana bubuga kafa a kasa, duk suka rud'e aka rasa wanda zai iya dakatar da ita, ihu take tare da buge buge, tana ture komai na gurin.
"Wayyo Allah! Da nasan haka zaki koma da banyi kasassabar dauko ki ba, kiyi shiru"
Dakyar suka rarrasheta Hajiya Adawiyah ta shiga da ita ciki.
Suna shiga daki ta bud'e baki tana kallon duniyar dake cikin d'akin, kallon katon madubin jikin wardrob tayi, tare da yiwa kanta gwalo, sannan ta fashe da dariya, tace.
"Wallahi naganni babban a wannan madubin, wannan ba Irin na Iyah bane nata iya fuska kake gani, wayyo dube Ni, na zama katuwa""Jan muje kiyi wanka."
Nuna mata ban daki tayi, sim-sim ta wucce, har cikin ban dakin. Tana taka dan capter din da ake sakawa a bakin kofa ta fasa ihu, ta juya da mugun gudu ta koma bayan Hajiya Adawiyah, jikinta na rawa, sai da ta rike ta har cikin ban dakin, taga ruwa a cikin abin wanka, ga karafunan panpo. Shiga suka yi Hajiya Adawiyah ta nuna mata ruwan wanka, da yadda zata yi tace mata.
" Bari na kawo miki brush da closeup"
Shiru tayi sannan tace.
"To kuma meye borus da kilozef,"Juyawa tayi ta kalli yadda karafunan suke, kai hannunta tayi ta dabo wani panpo wanda aka saka alamar jan paint, na ruwan zafi, aikuwa tana tsaye a kasar panpon ruwan me zafi ya shiga saukowa akanta, da ta buga waya suwa ta fita da mugun gudu tana wancakalar da hijabin ɗinta da dan kwalinta.
Tana ihu tare da birgima, Ga baki dsya mutanen gidan suka taru akanta sai cewa take.
"Wayyo Allah na, yau naga buni. Wato tsige Ni za ayi ta tsakar ka. Alkur'ani bani kuma shigewa wancan dakin."
Tsaki wani matashin Saurayi yayi sannan yace.
"Dad! Yaushe ka dauko wannan bararojin, dub'eta fa, tazo tana ihu kamar wacce aka tsige namar jikinta.""Jalal! Ina wasa da kai ne, ina ruwanka da ita, fita ka bamu guri."
Kukan da take yi ne ya kare tabi Jalal ɗin da ido, ta kalli irin gashin da ya bari, irin azonto din nan.
"Wannan gahin sa, kamar hikar angulu"
D'agowa duk suka yi tare da kallon gashin aikuwa suka kwashe da mugun dariya, har Dad din su, sai dariya suke mishi, kamar zai saka kuka ya juya tare da zabga mata harara.Sannan yasa kai yafita yana fadin idiot, kallon su tayi sannan tace.
"Toh kuma meye uduwat"
Fita Dad yayi daga dakin yana darawa.Riko hannunta Hajiya Adawiyah tayi suka shiga ban daki, da kanta tacire mata kaya, tana kallon halittar da Allah yayi, ga kyau ga diri, dan ba karya Fulanin Dabji kyakyawa ne, bafa muna kyawawan ba, idan kaga baki a cikin dabji bakone, Jan Parih ba fara ce kuma ba za a kirata baka ba, dan zamu iya kiranta da kalar fatar Mawakiyar nan ta U.s rihanna sannan Allah yayi mata baiwar gashi, Kuma baki sid'iki,
Daga yanayinta kawai zaka tabbatar da zatayi tsayi, sannan bata da yawan jiki sirirya ce, fuskar ta shima dan Karami me zagaye da siririn hancin da karamin bakinta, kawai ka nazarci yadda pari take.Kin cire rigar tayi, Hajiya Adawiyah tayi dariya sannan tace..
"Wanke miki kai zanyi na kuma miki wanka."
Kamar zata yi kuka tace.
"Ai Iyah ta dade da daina min wanka."Zaro ido Hajiya Adawiyah tayi cikin mamaki tace.
"Sabida me?!"
Tura baki tayi can cikin bakinta tace.
"Sabida na balaga mana"
Zaro idanu ta kuma a karo na biyu tace..
"Kin balaga?! A ina kenan?!"
Watsar da hannu tayi sannan tace.
"To ai nima yanzun yan mata ce kinga an daina min wanka."Da Hajiya ta gaji da surutu kamata tayi ta cire mata kaya har da kwalin kanta, ta zauna ta wanke kanta fess anayi tana jifar Hajiya Adawiyah da tambaya.
"Hajiya kince ban balaga ba, meye ya rage? Kuma idan na balaga ya zan zama babba kenan? Gaskiya gwara na balaga dan bana son ana min wankan,"Kallon Bakin Parih tayi kamar ta buge, amma sai tana ganin Absham da Amatul Islam.
Tana mika mata towel ta jefo mata tambaya.
"Hajiya! Ni kam wannan karfen me kunshe da ruwan tsigeka da ranka ne?!"Ba bita kanta ba tafita tabarta a ban dakin, abokiyar zamanta tasamu tace.
"Auntynsu lafiya?!"Tsaki tayi sannan tace.
"Malam almu yazo yana jiran Daddy, kuma wancan satin fa ya bashi kudi wannan satin ma yazo."Shiru tayi sannan ta dauko mai zata bawa Parih amma babu ita babu dalilinta,
Ita kuwa Parih daga jin maganar sune tayi waje da towel a daure, tana zuwa taga tsohon a zaune, kusada shi taje, ta fara tona rami, tsohon yace.
"Jikata me kike haka babu kaya."
Sunkuyawa tayi tana kallon ramin, sannan tace.
"Ayya baba tsoho ina hango kabarinka ne, domin duk wanda yazo nan gidan yanzun da nazo sai na leko karbarin shi.""Ke ja'iran ina ne, dan gidanku a ina kika tab'a jin an hango kabarin mutum."
"Laaa! Kaji min bana tsoho wai da gundira mishi karya, don Allah zo na nuna maka Alkur'ani ga kabarinka nan."
Jikin tsohon ne ya shiga kerrma, da cira kafin ta bud'e baki tuni ya arta a guje sai tashin Babbar rigarshi a iska kake gani (🤣😂)
Parih.......