18

2.2K 320 22
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

Dedicated to my Aunty Nice.

   😂🤣 Kaiii Jama'a meye laifin Abdul da kuka washe shine!

   Gaisuwa gare ku Masoyan Parih 💁🏻‍♂️

Page_18

Muna shiga gidan Aunty Amarya tace min.
"Kaza kanki da motsi kin dawo!"
Juyawa nayi na kalli Jalal ashe ya fita, tura baki nayi nace.
"Babu abinda ya dame ki dani! Tunda ba gurinki nake ba"

  Make min baƙi tayi na rike gurin, tare da fashewa da kuka, na bar falon na nufi d'akin Mamie!

       Kallona tayi dan na bar su Buhayyah suna kwaso min kayana.
"A ina kuka tsaya?!"
     Niman kukan nayi na rasa, domin kuwa ban yi tsammanin tambaya daga gareta ba sai da ta kuma buga min tsawa, wanda ya sani fashe mata da kuka nace.
"Ai shine ya kaini yawo muka ci kayan dad'i"

  Ban tab'a ganin b'acin ranta ba sai yau fad'a take kamar zata doke ni, sai da ta min tass sannan ta tura aka kira shi tayi mishi fad'a sosai.

        Tsabar kuka shiga d'aki nayi na kwanta, ban tashi ba sai kiran sallah, na tuna tun a wunti yayi Sallah sannan yace.
"Idan muka koma sai Kiyi a gida"
Shine na tadda faɗar Mamie, har abinci rana fushi nayi baki ci, da dare ma kin fita nayi, ina kwance har Mamie ta gaji ta kawo min abinci nace na koshi. Kallon Aarib tayi sannan tace.
"Kai dauko min wayar charge nan naji da wannan me kunnen kashin."

              Da sauri na tashi ina tura baki nace..
"Wannan tulelen mugu ne! Toh na tashi!"
   Haka ta sani cin abinci har sai da na fara yunkurin amai, sannan ta hakura, ta kuma kara da min nasiha sosai sannan ta shafa kaina. Kafin ta futa a dakin.

          +++
Bayan dawowata da kwana uku muka koma makaranta, duk yadda Jalal yaso mu shirya naki domin a cikin nasihan da Mamie tace min.
"Idan kika bari maza suna rike ki, mutuwa zaki yi kuma, Ni da baffanki babu ruwan mu dake, dan haka babu ruwan ki da Jalal."

  Tun ta tsorata Ni kuma, gani da shegen tsoron mutuwa, ya sani gudun shi, da ya dame Ni kuwa na sanya mishi kuka, dan dole ya kyaleni.

               +++
   Bayan shekara uku

   Lokacin mu yana tafiya, fiye da tafiyar hawainiya. Rayuwar mu karewa take kamar yadda ake karar da ruwan a cikin mazubi, kwanci tashi asarar me rai, dan har na shiga aji d'ayan Secondry,  abubuwan sai a hankali domin bawani canji sai na alamun girman da nayi dan yanzun na cika shekaru sha biyar, kuma amadadin nutsuwa sai na kuma haɗuwa da shaidanun kawaye, masu masifar rashin ji, da wasan banza.

            

                  Wani abinda yake d'aga hankalin Mamie yadda muke wasan banzan da muke da Jalal, wanda tayi fad'a har ta gaji. Ban san yadda zan fada muku irin girman da nayi ba, dake ina samun kulawa da cima me kyau, nayi wani irin cika ne daga sama har kasa zuwa sama,  wani lokacin kuma ina makaranta zai je lokacin break, idan na shiga motar, wasan banza zai ta min har sai na gaji nace mishi wallahi sai na gayawa Mamie.

             Yau na dawo a gajiye, ina taku kamar  bazan yi tafiya ba, ina shiga motar nan.
"Malam Nura! Ya aiki"

"Lafiya! Parih ya karatu"
     Kwanciyata nayi dan cikina na ciwo, kallon fuskana nayi na sake murmushi, na janyo jakata na ciro karfen hujin hancin da Sa'imah Garu ta saya min na sakala, sai wani button da ake sakawa a kasar baki ko saman baki, mannewa nayi sannan na saka na hancin na, sai wani wanda Faseelah tace min. A jikin cibiya ake sakawa.(🙄 Anya Parih kawayenki nan yan arziki ne! Wannan ai duk yan iska ne)

            Murmushin jin dadi nake sakewa har muka isa gida, muna shiga naga wata dalleliyar mota, Ni kaina motar ta hauka Ni, sauka nayi ina kallon motar har na shiga cikin gidan, dake yau kafin na tafi makarantar sai da Mamie ta rankwshi ni, na fita da kuka. Akan wani sakon da ta gani a jakar makarantar ta samu sakon Faseelah, ban san me sakon yake kunshe ba ta mare Ni har da rankwshi. Tana min fatan shirya.

         Koda na shiga falon kauda kaina nayi ban kalli kowa ba, ina jin muryan mutane a falon amma naki ce musu komai.

"Kee zo nan!"
   Gabana ne ya fadi nace..
"Wayyo Allah na! Yaushe wannan mutumin ya dawo."
  Juyawa nayi cikin jin haushi nace.
"Xkuzimi!
   Sannan nayi wuccewa ta, ina jin muryan Aunty Amarya tana cewa.
"Wallahi Yarinyar nan ta lalace! Dubi Hancinta fa! Sai kace yar iska duk idanunta ya buɗe bata tsoron kowa sai Mamienku"

         Shiru tayi yana girmama girman da nayi, sai kace wacce ake bata abincin kaji yarinya ta haɓɓaka haka.

             "Durling tunanin! Tunanin me kake yi" murmushi yayi yace.
"Honey! Babu komai ina mamakin yadda yarinyar ta girma ne"

           "Hmm! Baka jin abinda Aunty take fada ne maybe akwai me matseta ne, dan naga tafi su Buhayyah girma! Gaskiya Daddy ya aurar da ita, ko kuma taja muku abin kunya dan idanunta ya rigada ya buɗe."

     Nan ita da Aunty Amarya suka yita zuga shi. Ni kuwa ina gama cire kayana, na saka wani boom short na jeans sai yar shirt me hannun vest na fito abuna, dan kayan da Jalal yake sayi min Ni da matar shi, na wuce su nake kitchen na zubo dan wake, da manja sai gurji da tumatur na zuba yaji, nazo  gaban su na zauna na fara ci a hankali.

           ....... Tafiya ya fara miƙewa ina ganin na kusan dakatarwa sabida Azumin da ya tunkaro mu

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now